Ramadan 2026: Tsofaffi da Wasu Mutane 7 da Shari'a Ta ba Su Damar Shan Azumi
Azumi a watan Ramadan yana ɗaya daga cikin wajibai a Musulunci, kuma yana ɗaya daga cikin shika-shikan Musulunci guda biyar. Sai dai, ba kowa ne ke da ikon yin azumi ba saboda wasu dalilai na musamman.
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Dr. Mujazin, Shugaban Cibiyar Da'awa da Ilimi a Jami'ar Muhammadiyah Surakarta (UMS), ya bayyana cewa Allah SWT ya yi sassauci ga Musulmin da ba za su iya yin azumi ba.

Source: Getty Images
Mutane 8 da za su iya shan azumi
Jami'ar UMS ta rahoto a shafinta na intanet cewa, Dr. Mujazin ya ce:
"Allah SWT ya ba da umarnin yin azumi, tare da samar da madadin hakan ga waɗanda ba su da ikon sauke wannan nauyin."
Ga rukunin mutane takwas waɗanda shari'a ta ba su damar ajiye azumi:
1. Masu ciwo mai tsanani
Musulmin da ke fama da matsananciyar rashin lafiya wadda ba a sa ran samun waraka, kamar shanyewar ɓangaren jiki ko masu wankin koda ko jini, an ba su damar shan azumi.
Idan mutum ya warke daga baya, zai biya azumin, amma idan ciwon na dindindin ne, zai bayar da fidyah ne kawai kamar yadda Allah ya bayyana a cikin Suratul Baqarah, aya ta 184.
2. Masu aiki mai matuƙar wahala
Ma'aikatan da ke yin ayyuka masu wahalar gaske waɗanda azumi zai iya jefa rayuwarsu cikin haɗari na rashin lafiya an ba su damar ajiye azumi, amma dole ne su rama daga baya.
Sheikh Wahbah al-Zuhaili, a cikin wani littafinsa mai suna: Al-Fiqh al-Islami wa Adillatuhu, wanda Research Gate ta wallafa a shafinta, ya rahoto ra'ayin Abu Bakar al-Ajiri kan azumi ga leburori masu aikin wahala, inda ya ce:
"Ma'aikacin da ke tsoron mutuwa ko lahani ga jikinsa saboda tsananin wahalar aiki na iya shan azumi, muddin aikin ya zama dole gare shi."
3. Matafiyi

Source: Getty Images
Allah ya ba matafiyi sassauci na ajiye azumi. Matafiyi zai rama azumi na kwanakin da ya sha bayan watan Ramadan ya ƙare.
A cikin littafin Fikih Muyassar, an ce daga cikin sharudan da matafiyi zai sha azumi, akwai maganar yin tafiyar da ta kai nisan kusan kilomita 80 (mil 48).
4. Tsofaffi masu rauni
Tsofaffi waɗanda ba su da ƙarfin jure yunwa da ƙishirwa saboda tsufa an yafe musu azumi, sai dai za su biya fidyah ta hanyar ciyar da mabukaci a kowace rana.
Wannan na kunshe ne a cikin hukuncin da Allah ya yanke a Kur'ani mai tsarkiSuratul Al-Baqarah, aya ta 184.
5. Mata masu haila da jinin biki
Mata masu jinin al'ada ko na haihuwa ba za su yi azumi ba har sai jinin ya ɗauke. Annabi (SAW) ya umarci mata da su rama azumin da ya wuce su, amma ba za su rama sallah ba.
Dr Zakir Naik, a jawabin da ya yi a wani taro, wanda ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya kafa hujja kan hakan da wani Hadisi na Muslim, mai lamba 335.
6. Mutane masu matsalar kwakwalwa
Azumi baya wajaba akan wanda ba shi da hankali, domin samun cikakken hankali yana ɗaya daga cikin sharuɗɗan ingancin azumi.
Annabi (SAW) a cikin wani Hadisi da Abu Dawud da Ahmad suka ruwaito, ya ce:
"An ɗauke alƙalami akan mutum uku: Mai barci har sai ya tashi, mahaukaci har sai ya warke, da yaro har sai ya balaga."

Source: Getty Images
7. Mata masu juna 2 da masu shayarwa
Idan azumi zai jefa lafiyar uwa ko ta jariri cikin haɗari, Musulunci ya ba su damar ajiye azumi domin kiyaye rayuka.
Malaman Musulunci su na cewa fatawa mafi inganci ita ce matan za su rama azumin da suka sha bayan sun samu sauki.
8. Ƙananan yara
Yara ƙanana ba su da wajibcin yin azumi har sai sun kai munzalin balaga. Sai dai ana iya koya musu tun suna ƙanana idan suna da ƙarfin hakan.
Dr. Mujazin ya jaddada cewa ko da yake akwai waɗannan sassaucin, kada Musulmi ya ɗauki maganar azumi da wasa. Idan akwai ikon biya, to dole ne a biya bashi domin nauyin baya gushewa haka kawai.
Abubuwan sani game da azumin Ramadan
A wani labari, mun ruwaito cewa, mafi yawan Musulmai a fadin duniya sun tashi da azumin Ramadan a ranar Laraba, 18 ga Fabrairu, 2027 bayan ganin wata.
Sarkin Musulmi Muhammadu Sa’ad Abubakar II ta bakin Shehun Borno ne ya sanar da ranar fara azumi a Najeriya, a sanarwar da ya fitar daren ranar Talata.
A cikin watannan rahoto, Legit Hausa ta jero abubuwa 10 da ya kamata Musulmi ya sani kafin fara azumi, ciki har da muhimmancin tsarkake niyya da daidaita abinci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng



