Saudiyya Ta Sanar da Ranar Fara Azumi bayan Ganin Watan Ramadan
- Gwamnatin kasar Saudiyya ta sanar da cewa an ga watan Ramadan a yammacin yau Talata, 17 ga watan Fabrairun shekarar 2026
- Hakan na zuwa ne bayan fara duba jinjirin wata da hukumomin kasar suka yi bisa umarnin da gwamnati ta bayar ga 'yan kasar baki daya
- An samu rahotanni game da sakamakon duba watan Ramadan a wasu kasashen Musulmi da sauransu da ke fadin duniya a yau Talata
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Saudi Arabia - Kasar Saudiyya da Oman sun sanar da ganin wata; yawancin ƙasashen Asiya za su fara azumi 19 ga Fabrairu kamar yadda rahotanni suka nuna.
Hakan na zuwa ne yayin da watan Sha'aban ya cika kwana 29 kuma al'ummar Musulmi a fadin duniya suka fita duba wata da yammacin yau.

Source: Facebook
An ga watan Ramadan a Saudiyya
Legit Hausa ta tattaro bayanai da hukumomin Saudiyya suka yi game da ganin wata ne a shafin kasar na Haramain ya wallafa a Facebook.
Sanarwar da Saudiyya ta fitar ta nuna cewa:
"An ga wata a Saudiyya, Ramadan 1447 zai fara daga daren yau.
"Allah Maɗaukakin Sarki Ya karɓi azuminmu, tsayuwar dare da sauran ayyukan ibadarmu, Ya kuma ba mu ikon amfani da lokutan wannan wata mai albarka wajen aikata abin da zai faranta Masa rai. Ameen.".

Source: Facebook
Labarin ganin wata a kasar Indonesia
Ƙasar Indonesia ta sanar a hukumance cewa watan Ramadan zai fara ranar Alhamis, 19 ga Fabrairu, 2026, bayan da ba a ga jinjirin watan ba.
An yanke hukuncin ne bayan kammala tsarin ganin wata na gargajiya da Ma’aikatar Harkokin Addini ke jagoranta, wanda ke tantance ranar fara Ramadan a kowace shekara.
Labarin ganin wata a Malaysia
Rahoton Hisdustan Tmes ya nuna cewa hukumomi a Malaysia sun bayyana cewa ba a ga jinjirin watan Ramadan ba a ranar Talata ba.
Sakamakon haka, Laraba 18 ga Fabrairun 2026 za ta kasance ranar ƙarshe ta watan Sha’aban, yayin da za a fara azumi ranar Alhamis, 19 ga Fabrairu.
Sanarwar ta fito ne daga shugaban majalisar sarakuna na Malaysia, Tan Sri Syed Danial Syed Ahmad, bayan an duba wata a wurare 29 a faɗin ƙasar.
Batun ganin wata Japan da Philippines
Kwamitin duba wata na Japan da kuma Babban Muftin Philippines, Sheikh Abdulrauf Guialani, duk sun sanar cewa ranar farko ta Ramadan za ta kasance 19 ga Fabrairu, 2026 ganin ba a samu ganin jinjirin wata ba.
Da yammacin yau ne 'yan Najeriya za su fita duba wata a jihohi 36 na kasar da Abuja, inda za a jira sakamako daga fadar mai alfarma Sarkin Musulmi.
Shirin shiga watan Ramadan
A wani rahoton, kun ji cewa an bukaci al'ummar Musulmi su yi shiri na musamman domin shiga watan Ramadan na shekarar 2026.
Legit Hausa ta hada rahoto na musamman game da tanadin da ya kamata kowane Musulmi ya yi domin shiga watan Ramadan a kimtse.
Daga cikin abubuwan da ake bukata Musulmi ya yi akwai tsara lokutansa ta yadda zai samu damar yin ibada a kan lokaci yadda ya kamata.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


