Libya: An Bindige Dan Marigayi Shugaban Kasa, Muammar Gaddafi har Lahira
- An ruwaito cewa an harbe Saif al-Islam Gaddafi, ɗan tsohon shugaban Libya Muammar Gaddafi, har lahira a birnin Zintan
- Lauyansa ya ce wasu mutane huɗu dauke da makamai sun kai masa hari a gidansa, yayin da ’yar uwarsa ke cewa ya mutu kusa da iyakar kasar
- Saif al-Islam, wanda aka taba yankewa hukuncin kisa, ya kasance fitaccen mutum a siyasar Libya bayan rasuwar mahaifinsa a 2011
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tripoli, Libya - Rahotannin da muke samu sun tabbatar da cewa an kashe Saif al-Islam Gaddafi, ɗan marigayi shugaban Libya, Muammar Gaddafi.
Majiyoyi a ranar Talata 3 ga watan Faburairun 2026 sun ce ana zargin an harbe Saif al-Islam har lahira a birnin Zintan da ke yammacin Libya.

Source: Getty Images
An bindige dan Gaddafi a Libya
Rahoton BBC News shi ya tabbatar da wannan labarin a yau Talata 3 ga watan Faburairun 2026 da muke ciki.
Kafin rasuwar mahaifinsa a 2011, ana kallon Saif al-Islam Gaddafi a matsayin na biyu mafi girman jagora a Libya.
Rahotanni sun nuna cewa mutuwar Saif al-Islam, mai shekaru 53, wadda aka dade ana kallonsa a matsayin magajin mahaifinsa, ta samu tabbaci daga shugaban tawagarsa ta siyasa.
Lauyansa ya shaida wa manema labarai cewa wasu mutane huɗu dauke da makamai sun kai masa hari a gidansa da ke birnin Zintan, amma har yanzu ba a san wadanda ke da alhakin kai harin ba.
Sai dai a wani labari dabam, ’yar uwarsa ta bayyana a gidan talabijin na Libya cewa Saif al-Islam ya rasu ne kusa da iyakar Libya da Aljeriya.
Tun bayan kifar da mulkin mahaifinsa a 2011, ana kallon Saif al-Islam a matsayin mutum mafi tasiri a Libya, bayan Muammar Gaddafi wanda ya yi mulki daga 1969 har zuwa lokacin da aka kashe shi a juyin juya hali.

Source: Getty Images
Takaitaccen tarihin marigayi Saif al-Islam
An haife shi a 1972, kuma ya taka muhimmiyar rawa wajen kyautata dangantakar Libya da kasashen Yamma daga shekarar 2000 zuwa rushewar gwamnatin Gaddafi.

Kara karanta wannan
Mutane sun bada mamaki a jana'izar Sheikh Rigi Rigi, an ji sunaye 3 da ake kiransa da su
Bayan cire mahaifinsa daga mulki, an tsare Saif al-Islam a gidan yari na tsawon kusan shekaru shida a Zintan, bayan zarginsa da taka rawa wajen murkushe zanga-zangar adawa da gwamnati.
Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya (ICC) ta nemi gurfanar da shi bisa laifukan cin zarafin bil’adama, sakamakon rawar da ake zarginsa da ake yi.
A shekarar 2015, wata kotun Libya ta yanke masa hukuncin kisa ba tare da kasancewarsa a gaban kotu ba, bisa rawar da ya taka a gallazawa masu adawa da gwamnati.
Ko da yake ba shi da mukami a gwamnati, Saif al-Islam ya kasance yana tsara manufofi tare da jagorantar manyan tattaunawa, ciki har da yarjejeniyar da ta sa mahaifinsa ya yi watsi da shirin makaman nukiliya.
Wadannan yarjejeniyoyi sun taimaka wajen dagawa Libya takunkumin kasa da kasa, lamarin da ya sa wasu ke kallonsa a matsayin mai kawo sauyi a kasar.
Duk da haka, Saif al-Islam ya sha musanta cewa yana son gadon mulki daga mahaifinsa, inda ya ce 'iko ba gona ba ce da ake gada', cewar Al Jazeera.
Dan marigayi Gaddafi zai yi takara a Libya
A baya, an ji cewa Saif al-Islam Gaddafi ya yi rajista a matsayin ‘dan takara a zaben shugaban kasa da za aka shirya a wancan lokaci a Libya.
Hukumar zaben kasar Libya ta tabbatar da cewa Saif al-Islam ya shiga takarar 2021 domin gadon kujerar mahafinsa.
Sai dai daga bisani an dakatar da zaben har na wani lokaci da ba a kayyade ba wanda ya jawo tasgro a siyasar kasar.
Asali: Legit.ng

