Ana neman ‘Dan Marigayi Shugaba Gaddafi na Kasar Libiya ruwa a jallo
– Babban Kotun Duniya na ICC na neman iyalin Shugaba Gaddafi
– Ana zargin shi Saif-al-Islam din da wasu laifuffuka
– Shekaru kusan 6 kenan da aka kashe Shugaba Muammar Gaddafi
Kotun Duniya na neman wani ‘Dan Marigayi Muammar Gaddafi. Kama shi dai zai iya kara kawo rikici a Yankin na Libiya. Kuma dai har yanzu ba a san inda ‘Dan tsohon shugaban yake ba.
Cikin ‘yan kwanakin nan ne aka saki ‘Dan Marigayi Shugaba Muammar Gaddafi na kasar Libiya a karkashin wani lamuni. Sai dai babban Kotun Duniya ICC na neman sa kuma ruwa a jallo cewa ya aikata wasu laifuffuka lokacin Mahaifin sa na mulki.
KU KARANTA: Abin tausayi: Karanta labarin wani Dan Kano da ke Legas
Wasu dai sun soki sakin na shi da aka yi wanda har yanzu ba a san ma inda ya shige ba. ICC ke cewa dole Gwamnatin kasar ta kama shi domin a hukunta sa amma dai wasu na ganin sake sa ne zai kawo zaman lafiya a Yankin musamman yadda ya ke da magoya.
Kun ji cewa Dan Attajirar na Misis Alakija watau Folarin Alakija ya kashe kusan Biliyan 2 wajen bikin aure. Folarin ya auro wata ‘Yar kasar Iran ce da ke zaune a Ingila mai suna Nazanin Jafarian Ghaissarifar.
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
An yaye wasu Sojojin saman Najeriya
Asali: Legit.ng