An Gano Mai Bara da Ya Mallaki Manyan Gidaje, Mota da Tarin Dukiya
- Hukumomi a birnin Indore sun gano wani kuturu mai bara da ke da dukiya mai yawa da suka hada da gidaje, motoci da wasu harkokin kasuwanci
- Bincike ya gano kuturun mai baran a Indiya da ke samun dubban kudi a kullum daga yin maula tare da bai wa ‘yan kasuwa bashi da ke da kudin ruwa
- Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya bayyana ne yayin samame a kokarin gwamnati na kawar da roko a titunan Indore na jihar Madhya Pradesh
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
India – Wani kuturu mai bara da aka dade ana gani a titunan birnin Indore a jihar Madhya Pradesh ta Indiya ya janyo hankalin jama’a bayan da hukumomi suka gano cewa yana da tarin dukiya da ta hada da gidaje uku, mota da sauransu.
Rahotanni sun ce an gano lamarin ne a yayin da hukumomin birnin ke aiwatar da shiri na musamman domin kawar da masu bara daga tituna.

Source: Twitter
Rahoton Times of India ya nuna cewa an samu kuturu mai suna Mangilal a kasuwar Sarafa Bazaar, daya daga cikin wuraren kasuwanci mafi cunkoso a Indore.
Yadda mai baran yake rayuwa
Shekaru da dama, Mangilal ya kasance sananne a Sarafa Bazaar, inda yake zaune yana sunkuyar da kai kasa ba tare da ya kalli jama’a ba, abin da ke kara jawo tausayi daga masu wucewa.
Yanayin da yake ciki da yadda nakasarsa ke bayyana a fili ya sa mutane da dama ke daukarsa a matsayin mai tsananin bukata, suna zuba masa kudi a hannu ko a kan katakon da yake zaune a kai domin taimaka masa.
Sai dai bayan da hukumomi suka dauke shi daga titi, suka kai shi wurin da aka tanada, suka yi masa wanka tare da ba shi tufafi masu tsafta, sai aka fara yi masa tambayoyi domin fahimtar ainihin halin da yake ciki.
An gano mai baran yana da dukiya
A yayin tambayoyin, jami’an gwamnati sun gano cewa Mangilal ba ya fama da talauci kamar yadda mutane da dama a yankin ke zato.
Rahotanni sun nuna cewa yana samun makudan kudi a kullum daga bara, kudin da yake amfani da su wajen zuba jari da kuma ba wa ‘yan kasuwa rance mai kudin ruwa a Sarafa Bazaar.
Bincike ya kara nuna cewa yana da gidaje uku da suka hada da wani gini mai hawa uku, wani gida na daban, da kuma wani falo da aka ba shi ta wani shirin tallafin jin kai na gwamnati.
Haka kuma, an gano cewa yana da babura masu kafa uku guda biyu da yake bayarwa haya ga wasu mutane, sannan yana da mota guda daya.
Furucinsa da matakan da aka dauka
Mangilal ya amince cewa kudin da yake samu daga bara ba wai don ciyar da kansa kadai yake amfani da su ba, yana daukarsu a matsayin hanyar samun jari domin harkokin kasuwanci.
Rahoton Economics Times ya bayyana cewa ya ce shi kansa ba ya rokon mutane, sai dai su zuba masa kudi a kan katakon da yake zaune a kai.

Source: Twitter
Hukumomi sun ce suna ci gaba da bincike domin gano ko yana da asusun banki, tare da duba rawar da wasu daga cikin ‘yan uwansa ke takawa, ganin yadda aka gano cewa wasu daga cikinsu ma suna harkar bara.
Donald Trump zai koro 'yan Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin shugaban Amurka, Donald Trump ta fitar da sunayen 'yan Najeriya da za ta maido gida da zama.
Amurka ta wallafa sunayen mutum 79 da ta ce sun aikata manyan laifuffuka da ba za a barsu su cigaba da zama a kasar ba a halin yanzu.
Hakan na zuwa ne karkashi shiri na musamman da Trump ya kawo domin fatattakar bakin haure daga Amurka zuwa kasashensu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


