Manyan mabarata 10 na duniya da arzikinsu yafi na wasu manyan masu kudin Najeriya

Manyan mabarata 10 na duniya da arzikinsu yafi na wasu manyan masu kudin Najeriya

- Bara dai wata irin dabi’ace ta tsayawa roko daga jama’a ba tare da an tashi an nemi na kai ba

- Wasu dai sun mayar da bara hanyar ci, sha da kuma saka sutura tare da tara dukiya

- Sai dai ana ganin Mumbai bara na da matukar ci don har kamar ta fi aikin gwamnati kawo kudi

Bara dai wata irin dabi’ace ta tsayawa roko daga jama’a ba tare da an tashi an nemi na kai ba. Mutane da yawa sun mayar da bara sana’a kuma a ita suke samun na ci, sha da sutura.

Akwai mabaratan da suka fi wasu masu kudin tarin dukiya. Hakan kuwa bai sa sun hakura da wannan mummunar dabi’ar ba.. Ga wasu manyan masu kudi daga cikin mabaratan duniya.

Manyan mabarata 10 na duniya da arzikinsu yafi na wasu manyan masu kudin Najeriya
Manyan mabarata 10 na duniya da arzikinsu yafi na wasu manyan masu kudin Najeriya
Asali: Facebook

1. Bharat Jain:

An gano cewa shi ne mabaraci wanda yafi kowa arziki a duniya. Bharat jain dan asalin Mumbai ne kuma yana kasance babban mai arziki. Bharat na da shekaru 52 a duniya kuma yana bara ne a yankin Parel da ke birnin Mumbai. Yana barar ne a Azad maidan ko kuma Chhatrapati Shivaji Terminus. Yana samun INR 2,000 zuwa 2,500 a rana kuma ya mallaki gidaje biyu masu darajar Lakh 80. Yana da shagon kanshi wanda yake samun 10,000 a kowanne wata.

2. Eisha:

Elisha mace ce ‘yar kasar Saudi Arabia wacce ta rasu tana da shekaru 101. Bayan mutuwarta ne aka gano yawan dukiyarta. Miliyoyin gareta a yayin da ta mallaki manyan gine-gine hudu, kayan karau da kuma sisin gwal. Da aka hada jimilar dukiyarta, ta mallaki $miliyan daya.

3. Simon Wright:

An hana Simon Wright bara amma a hakan yana samun pam 50,000 daga wajen masu mishi kyauta a duk wata. Simon na rayuwa a wani katafaren gida mai darajar pam 300,000.

5. Ted Williams:

Dan asalin Ohio ne Ted Williams kuma yana samun kudin barar shi ne daga waka. Yana bara ne a kan titin Ohia kuma a lokacin yana da tsananin talauci. Wani dan jarida ne ya ji yadda yake rera waka sannan yayi mishi bidiyo tare da wallafa shi a Youtube. Bidiyon ya bazu kuma daga nan Williams ya dinga samun kudi.

KU KARANTA: Labarin Ramatu matar da take samun ribar miliyan daya da rabi a kowanne mako da sana'ar sayar da carbin malam

6. Krishna Kumar Gite:

Wannan mabaracin daga Mumbai yake. Krishna Kumar Gite na samun tsakanin Rs 1,500 zuwa Rs 2,000. Yana da gidan kan shi a Nallasopara.

7. Sambhaji Kale:

Kamar fa bara ta fi aikin gwamnati ci a Mumbai. Sambhaji Kale da duk iyalan shi duk bara suke yi. Sambhaji Kale yana samun a kalla Rs 1,000 a rana. Yana da asusun banki kuma yana saka hannayen jari a kamfanoni. Yana da gida a Virar, gidaje biyu da kuma fili a Solapur.

8. Sarvatia Devi:

Sarvatia Devi mabaraciya ce daga Patna kuma tana zama a gidan shi da ke kusa da Sinima din Ashok. Tana biyan kudin inshora 36,000. Tana yawo a duniya don ta ziyarci manyan wuraren bauta a ciki da wajen India.

9. Corey & Rongfeng:

Corey da Rongfeng na da labari mai cike da mamaki. Corey ya fara aiki ne bayan da ya tara kudi daga bara. Yana kai mujallu a kowacce rana kuma yasa samun $100. Hakazalika Rongfeng na kwana ne a tituna. Wata budurwa ce ta taimake shi da kudi har ya fara kasuwanci kuma yayi arziki mai tarin yawa. Ya ba budurwar $163,000 don nuna godiyar shi.

10. Massu/ Malana:

Massu ko kuma Malana wani mabaraci ne daga Mumbai wanda yake daga cikin mabarata masu kudi a duniya. Da mota yake zuwa wajen barar kuma da ita yake komawa gida. Bayan sauya kayan barar shi, yana daukar sa’o’I 8 zuwa 10 yana bara. Yana samun Rs 30,000 zuwa 40,000 a kowanne wata kuma yana da kadara mai darajar lakh 30.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel