Jirgin Sama Ya Yi Hatsari, Wani Babban Jami'in Gwamnati da Mutane 4 Sun Mutu a India

Jirgin Sama Ya Yi Hatsari, Wani Babban Jami'in Gwamnati da Mutane 4 Sun Mutu a India

  • Mataimakin babban minista, Ajit Pawar ya rasu tare da mutane hudu a wani mummunan hadarin jirgin sama da ya auku a yammacin Indiya
  • Ana zargin rashin kyawun gani da kuma rashin hasumiyar kula da jirage a filin jirgin Baramati ne suka janyo jirgin Pawar ya sullubo kasa
  • Firamistan India, Narendra Modi ya aika sakon gaggawa bayan mutuwar Pawar, sannan an zakulo wasu bayanai game da mataimakin ministan

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

India - Wani jirgin sama dauke da babban jami’in gwamnati ya yi hatsari a yammacin kasar India ranar Laraba, inda hakan ya yi silar mutuwar daukacin mutane biyar dake ciki.

Jirgin samfurin Learjet 45 yana kan hanyarsa ne daga babban birnin kasuwanci na Mumbai zuwa garin Baramati, inda nan ne mahaifar babban jami'in.

Kara karanta wannan

'Dan bindiga da ya hana Turji, yaransa sakewa ya mutu, an kashe shi wurin sulhu

Hatsarin jirgin sama ya yi silar mutuwar mataimakin babban ministan Indiya.
Masoyan Ajit Pawar, babban mataimakin minista a Indiya da ya mutu a hatsarin jirgin sama. Hoto: AFP
Source: AFP

Mataimakin minista ya mutu a hatsarin jirgi

Rahoton kafar watsa labaran AP ya nuna cewa jirgin saman ya yi katantanwa a gajimare, kafin ya fado ya kama da wuta a wani fili kusa da hanyar saukar jirage.

Hotunan talabijin sun nuna hayaki yana tashi daga baraguzan jirgin da ya kone kurmus, kimanin kilomita 254 daga birnin Mumbai.

Hukumar kula da sufurin jiragen sama ta tabbatar da rasuwar Ajit Pawar, mai shekaru 66, wanda shi ne mataimakin babban ministan jihar Maharashtra dake yammacin India.

Kafafen yada labarai na kasar sun nuna cewa rashin kyawun gani ne ya janyo hadarin, inda tuni hukumar binciken hadurran jiragen sama ta fara bincike mai zurfi.

Filin jirgin sama na Baramati ba shi da hasumiya ta musamman (ATC) mai kula da zirga-zirgar jirage, inda ta sanya ma'aikatan jirgin suke tambayar malaman dake makarantun koyon tuki kusa da wurin game da yanayin iska.

Kara karanta wannan

Juyin mulki: Yadda Kanal na soja ya tsara kifar da Gwamnatin Bola Tinubu

Tasirin mataimakin ministan Indiya da ya rasu

Pawar ya kasance babban jigo a siyasance kuma daya daga cikin mambobin gwamnatin hadaka ta Firaministan India, Narendra Modi, in ji rahoton Yahoo News.

Mataimakin ministan ya shahara kwarai wajen jan ra'ayin masu jefa kuri'a a karkara, musamman a yankunan da ake noman sukari a jihar Maharashtra inda yake da gagarumin tasiri.

A lokacin da hadarin ya hadu, Pawar yana kan hanyarsa ne ta zuwa Baramati domin kaddamar da yakin neman zaben kananan hukumomi.

Firaminista Narendra Modi ya yi ta'aziyyar mataimakin ministan Indiya da ya rasu a hatsarin jirgi.
Firaministan India Narendra Modi tare da mataimakin minista, Pawar a wani taro. Hoto: @narendramodi
Source: Twitter

Sakon ta'aziyya daga Firamistan India

Firamistan India, Narendra Modi ya bayyana Pawar a matsayin bawan Allah wanda ya sadaukar da rayuwarsa domin yi wa al'umma hidima, musamman talakawa.

Modi ya wallafa a shafinsa na X cewa:

"Rasuwar sa haka kwatsam ta firgita ni kuma ta jefa ni a tsakanin bakin ciki. Ina mika ta'aziyya ga iyalansa da masoyansa marasa adadi."

Baya ga Pawar, ma'aikatansa guda biyu da kuma matukan jirgin biyu duka sun riga mu gidan gaskiya a wannan mummunan hadari da ya faru a ranar 28 ga Janairu, 2026.

Kara karanta wannan

Sojoji sun bankado masana'antar kera bindigogi, an cafke makeri

Jirgi dauke da fasinjoji 200 ya yi hatsari

A wani labarin, mun ruwaito cewa, jirgin sama na kamfanin Air India ya gamu da hatsari jim kaɗan bayan tashinsa daga birnin Ahmedabad da nufin zuwa Landan.

Jirgin, mai lamba AI171, nau’in Boeing 787-8 Dreamliner, ya rikito ƙasa ne jim kaɗan bayan tashinsa daga filin jirgin sama na birnin Ahmedabad dauke da fasinjoji 200.

Ministan harkokin sufurin jiragen sama na Indiya, Ram Mohan Naidu Kinjarapu, ya ce yana cikin “zullumi da ɓacin rai” bisa wannan hatsari da ya yi ajalin dukkan fasinjoji.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com