Tirkashi: Kotu Ta Tura Tsohon Shugaban Kasa Gidan Yari, Zai Yi Zaman Shekaru 5 a Korea
- Wata kotu a Koriya ta Kudu ta yanke wa tsohon shugaban kasar, Yoon Suk Yeol hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru biyar
- Bayan wannan hukunci, masu gabatar da kara suna neman a yanke wa tsohon shugaban kasar hukuncin kisa a wata shari'ar daban
- Yoon shi ne shugaba na farko da aka taɓa kamawa yana kan mulki a tarihin Koriya ta Kudu, biyo bayan soke dokar ta-bacin da ya sanya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Korea ta Kudu - A ranar Juma'a, 16 ga Janairu, 2025, wata kotu a ƙasar Koriya ta Kudu ta yanke wa tsohon shugaban ƙasar, Yoon Suk Yeol, hukuncin ɗaurin shekaru biyar a gidan yari.
Wannan hukunci ya biyo bayan samunsa da laifuffuka da suka haɗa da yin amfani da jami'an tsaro wajen dakile ƙoƙarin kama shi bayan gazawar da ya yi na sanya dokar ta-ɓaci a watan Disamba, 2024.

Source: Getty Images
Kotun Seoul ta samu Yoon da laifin tura jami'an tsaron fadar shugaban ƙasa domin su tare jami'an bincike daga aiwatar da takardar sammacin kama shi, in ji rahoton Reuters.
Alƙalin kotun ya bayyana cewa tsohon shugaban ya yi amfani da tasirinsa wajen mayar da jami'an tsaron ƙasar tamkar jami'an kashin kansa domin biyan buƙatun kansa da tsira daga shari'a.
Laifuffukan da aka same shi da su a kotu
Baya ga zargin hana kama shi, tsohon mai gabatar da ƙara na ƙasar mai shekaru 65 ya fuskanci wasu laifuffukan da suka haɗa da ƙirƙirar takardun bogi na gwamnati.
Haka kuma, kotun ta tabbatar da cewa ya saɓa wa matakan shari'a na sanya dokar ta-ɓaci, waɗanda ya kamata a ce an tattauna su a taron majalisar zartarwa kafin aiwatarwa.
Wannan shi ne hukunci na farko da aka yanke wa Yoon game da tuhume-tuhumen manyan laifuffukan da yake fuskanta tun bayan rugujewar dokar ta-ɓacin da ya sanya.
Ko da yake ya saurari hukuncin cikin nutsuwa ba tare da nuna wata damuwa a fili ba, lauyoyinsa sun bayyana cewa za su ɗaukaka ƙara domin suna ganin hukuncin ya biyo bayan matsin lambar siyasa ne.
Takun-saƙa tsakanin masoya da 'yan adawa
A wajen harabar kotun, an samu tsauraran matakan tsaro yayin da masu goyon bayan Yoon suka taru suna ɗauke da kwalaye masu rubutun cewa tsohon shugaban ya zama abin farautar siyasa.
Masu zanga-zangar sun nace cewa tarihi ne zai yi wa Yoon shari'a, yayin da ƴan sanda suka zagaye ginin kotun domin gudun barkewar hargitsi.
Idan ba a manta ba, majalisar dokokin ƙasar tare da goyon bayan wasu mambobin jam'iyyar Yoon ne suka kaɗa ƙuri'ar soke dokar ta-ɓacin sa'o'i kaɗan bayan sanar da ita, sannan daga baya aka tsige shi daga mulki a watan Afrilun bara.
Yoon shi ne shugaba na farko da aka taɓa kamawa yana kan mulki a tarihin Koriya ta Kudu, bayan da aka tura jami'an ƴan sanda sama da 3,000 domin dauko shi, in ji rahoton CBC.

Source: Getty Images
Ana so a yanke wa tsohon shugaba hukuncin kisa
Wannan hukunci na shekaru biyar ya shafi ɓangaren dakile bincike ne kawai, amma akwai wata shari'ar daban inda masu gabatar da ƙara ke neman a yanke masa hukuncin kisa.
Suna tuhumarsa da laifin kulla maƙarƙashiya ga Korea ta Kudu ta hanyar ƙoƙarin sanya mulkin soja ba tare da ƙwaƙƙwaran dalili ba gami da ƙoƙarin dakatar da ayyukan majalisar dokoki.
Yanzu haka dai Yoon yana tsare a gidan yarin Seoul, inda yake ci gaba da kare kansa da cewa yana da ikon sanya dokar ta-ɓaci a matsayinsa na shugaban ƙasa.
Ya ce matakin nasa ya biyo bayan ƙoƙarin da jam'iyyun adawa ke yi ne na hana gwamnati gudanar da ayyukanta, lamarin da ya jefa ɗaya daga cikin manyan ƙasashen tattalin arziki a Asiya cikin rudani.
'Dan Kano ya yi bajinta a kasar Korea
A wani labari, mun ruwaito cewa, wani 'dan Najeriya da ke aikin bincike a Korea ta Kudu ya kirkiri na'urar da za ta iya kamawa tare da kashe sauro daga nisan kilomita daya.
An rahoto cewa na'urar da Dakta AbdulQaadir Maigoro ya kirkira za ta iya gane nau'in sauro cikin dakiku da cutar da ya ke dauke da ita da kuma kashe shi.
Da wannan fasahar, ana sa ran Dakta AbdulQaadir Maigoro zai taimaka wajen yaki da cutar zazzabin sauro ta 'asymptomatic' da ke lalata kwakwalwar dan Adam.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


