Gasar Olympics: Koriya ta kudu kamar dai bata gayyatar musulmi

Gasar Olympics: Koriya ta kudu kamar dai bata gayyatar musulmi

- An saba gina masallatai a wuraren wasanni somin baki musulmi

- Wannan karon Koriya ta ki amincewa da tsarin a filayen wasannin Olimpis

- Kasar Koriya dai ita ce zata karbi bakuncin kasashen duniya domin wasannin

Gasar Olympics: Koriya ta kudu kamar dai bata gayyatar musulmi
Gasar Olympics: Koriya ta kudu kamar dai bata gayyatar musulmi

A gasar Olimpics da za'a fafata a kasar Koriya ta kudu a bana, 2018, kasar ta Koriya ta cije ta qi amincewa a gina masallatai na wucin gadi domin samawa musulmi masu neman sauke faralli wuraren ibadunsu na yau da kullum.

A tsari dai, ko a ina ne a duniya, akan samar da irin wadannan wurare, na alwala da sallah da ma na sauran bukatu ga kowanne addini idan da bukatar hakan, sai dai, wannan karon alamar abun ba zai yiwu ba.

DUBA WANNAN: Kudaden da Najeriya ta samu a bara: Adadinsu

Kasar dai ta Koriya, ta kafu ne karkashin gurguzu na zamanin da ake yayin hakan a yankin, sai dai, tuni ta balle ta koma tsarin jari hujja, wanda ba kamar na gurguzu ba, ya yarda akwai ababen bauta na addinai.

Hukumar kula da harkokin yawon bude ido ta Koriya Ta Kudu KTO, ta soke wani shirin samar da masallacin tafi-da-gidanka da aka yi niyyar samarwa a Gangneung saboda gasar Olymoics ta hunturu, sakamakon kin hakan da masu fafutuka da ke adawa da musulunci suka nuna.

Duk da cewa yawan musulman Koriya Ta kudu kashi 0.2 cikin mutum miliyan 51 na kasar ne, hukumar KTO ta yi niyyar gina wajen sallah ga musulmai a lokacin gasar Olympics ta hunturu, saboda ta samar da yanayin da musulmai za su ji dadin zama a kasar, da kuma kara yawan baki musulmai 'yan yawon bude ido.

Sai dai babban jami'in hukumar Kang Suk-ho, ya shaida wa Al Jazeera cewa sun soke shirin ne bayan kungiyoyi da dama sun soke shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng