2026: Cikakken Jerin Kasashe 45 da Ƴan Najeriya Za Su Iya Zuwa ba Tare da Biza ba

2026: Cikakken Jerin Kasashe 45 da Ƴan Najeriya Za Su Iya Zuwa ba Tare da Biza ba

  • Fasfo din Najeriya ya samu karbuwa a kasashe 45 na duniya inda matafiya zasu iya shiga ba tare da shan wahalar neman biza ba
  • Kasashen Afirka kamar Ghana, Kenya, da Rwanda sun soke takunkumin biza ga 'yan Najeriya domin bunkasa harkokin kasuwanci da bude ido
  • Wannan rahoto ya jero kasashe 45 na duniya da ke ba 'yan Najeriya damar shiga cikinsu, walau kafin tafiya ko kuma a filin jirgi idan an isa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Masu riƙe da fasfo ɗin Najeriya yanzu suna da damar ziyartar ƙasashe 45 a faɗin duniya ba tare da buƙatar neman biza tun kafin lokacin tafiya ba.

Wannan ci gaba babban albishir ne ga matafiya, ’yan kasuwa, da masu yawon buɗe ido, domin zai rage wahalhalun gudanar da takardu da tsadar kuɗaɗen biza.

Kara karanta wannan

AFCON2025: Najeriya ta gamu da babban cikas yayin da take shirin haduwa da Moroko

'Yan Najeriya na iya zuwa kasashe 45 ba tare da biza ba
Matafiya a filin jirgin sama da fasfon Najeriya. Hoto: Osarieme Eweka, Jacoblund
Source: Getty Images

A cikin waɗannan ƙasashe 45, guda 27 ne ke ba da cikakkiyar damar shiga kyauta, yayin da sauran suke ba da biza a lokacin da mutum ya sauka a filin jirgi ko kuma neman izinin tafiya ta yanar gizo, in ji rahoton The Nation.

Kasashe da za a iya zuwa babu biza

Kasashen Afirka da dama sun ɗauki wannan matakin domin ƙarfafa kasuwanci da yawon buɗe ido a tsakanin ’yan uwa mazauna nahiyar:

  • Gambia: Tun a shekarar 2019, ƙasar Gambiya ta buɗe iyakokinta ga dukkan matafiya ’yan Afirka ba tare da bukatar biza ba.
  • Benin: Maƙwabciyar Najeriya, watau Benin, ita ma ta soke biza ga dukkan ’yan Afirka tun shekarar 2019.
  • Kenya: A watan Oktoba, 2023, Shugaba William Ruto ya sanar da soke biza ga dukkan matafiya ’yan Afirka domin haɓaka kasuwanci.
  • Rwanda: Tun a Nuwamba, 2023, Rwanda ta ba da damar shiga ƙasarta kyauta ga dukkan ’yan Afirka.
  • Ghana: Sabon shiga cikin jerin ƙasashen, Ghana yanzu tana ba da damar shiga ba tare da biza ba ga ’yan Afirka don zama cibiyar kasuwanci a Afirka ta Yamma.

Kara karanta wannan

Farashin abinci: Manoma sun soki gwamnati da rashin adalci, sun shiga ɗimuwa

Sauran kasashen da za iya shiga cikin sauƙi

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa baya ga waɗanda aka lissafa a sama, fasfo ɗin Najeriya na ba da damar shiga waɗannan ƙasashe masu zuwa cikin sauƙi:

Ƙasashen Afirka

Ƙasashen Caribbean da sauransu

Burkina Faso, Cameroon, Cape Verde, Chad, Côte d’Ivoire, Guinea, Guinea-Bissau, Liberia, Mali, Niger, Senegal, Sierra Leone, Togo.

Barbados, Dominica, Haiti, Montserrat, Saint Kitts and Nevis, Fiji, Cook Islands, Kiribati, Micronesia, Vanuatu.

Fasfon Najeriya ya na da darajar da za a iya shiga kasashe 45 da shi ba tare da biza ba.
Fasfon Najeriya da Ministan harkokin cikin gida, Tunji Alausa. Hoto: Osarieme Eweka
Source: Getty Images

Girman matsayin fasfon Najeriya

Wannan mataki yana nuna irin girman darajar fasfo ɗin Najeriya da kuma yadda ƙasashen duniya ke ƙoƙarin sauƙaƙa zirga-zirga tsakanin al'ummu.

Ko da yake yanayin shiga ya bambanta daga ƙasa zuwa ƙasa, babban manufar ita ce samar da damar gudanar da harkokin kasuwanci da ziyarar dangi cikin sauri kuma cikin sauki.

Kasashe 7 sun sassauta matakan biza

A wani labari, mun ruwaito cewa, an samu wasu ƙasashe na duniya da suka fara sauƙaƙa musu samun biza da shiga ƙasashensu cikin sauƙi.

Kara karanta wannan

2027: Tinubu ya ware sama da Naira tiriliyan 1 a domin harkokin zabe

Daga Afirka zuwa Gabas ta Tsakiya, gwamnatocin ƙasashe da dama sun fara sassauta dokokin shige da fice, suna ƙara buɗe ƙofofin haɗin gwiwa da Najeriya.

Sassaucin da aka samu a Afrika ta Kudu, Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) da sauransu, zai taimakawa dalibai, 'yan kasuwa da masu yawon bude ido.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com