Bayan kai Hare Hare, Donald Trump Ya Fara Hararo Barazanar Tsige Shi a Amurka
- Shugaba Donald Trump ya gargadi ‘yan jam’iyyarsa cewa faduwa a zaben da ke tafe na iya jawo sake tsige shi daga mulkin kasar Amurka
- Donald Trump ya danganta yiwuwar tsige shi da idan ‘yan jam'iyyar Democrat su karbi ikon Majalisa, inda ya ce za su aikata hakan
- Hakan na zuwa ne yayin da ra’ayoyin jama’a ke nuna damuwa kan tattalin arziki da alkiblar kasar Amurka a lokacin da Trump ke kai hare-hare
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Amurka – Shugaba Donald Trump ya yi gargadi ga ‘yan jam’iyyar Republican cewa idan suka rasa ikon Majalisa a zaben da za a yi, ‘yan Democrat za su iya tsige shi.
Trump ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya gabatar a wani taron manufofin ‘yan Republican na Majalisar Wakilai, inda ya ce nasara a zaben na da matukar muhimmanci ga makomar gwamnatinsa.

Source: Facebook
Rahoton NBC ya nuna cewa Trump ya ce idan jam’iyyarsa ba ta samu rinjaye ba, to ‘yan adawa za su nemo dalilin tsige shi, ko da kuwa dalilin ba shi da tushe.
Gargadin Trump kan batun tsige shi
A cikin jawabin nasa, Trump ya ce dole ne ‘yan Republican su yi nasara a zaben da za a yi domin kare manufar gwamnati a shekaru biyu na karshen wa’adinsa na biyu.
Ya bayyana cewa idan ba a samu nasara ba, ‘yan Democrat za su dauki mataki cikin gaggawa domin tsige shi, yana mai cewa hakan zai kasance tamkar siyasar ramuwar gayya.
Trump ya jaddada cewa tsige shi zai zama abin da zai hana gwamnatin sa aiwatar da manufofinta yadda ya kamata, musamman a bangaren tattalin arziki da tsaro.
Yanayin zaben da za a yi a Amurka
Rahotannin jin ra’ayin jama’a sun nuna cewa yawancin masu kada kuri’a na ganin kasar Amurka ba ta tafiya a kan hanya da ta dace da muradinsu.
Rahoton Reuters ya nuna cewa tattalin arziki na daga cikin manyan damuwar jama’a, lamarin da ka iya shafar yadda za su kada kuri’a a zaben da ke tafe.

Source: Twitter
A zaben da za a yi Nuwamban 2026, dukkan ‘yan Majalisar Wakilai da kuma kusan kashi 1 cikin 3 na ‘yan Majalisar Dattawa za su fafata a zabe, abin da zai tantance ko ‘yan Republican za su ci gaba da rike Majalisa.
Martanin Trump da ‘yan Democrat
Shugaba Trump ya ci gaba da jaddada cewa ba shi da laifi, yana mai cewa dukkan matakan tsige shi na siyasa ne ba wani abu ba.
Bayan wani farmaki da Amurka ta kai a Venezuela da kama shugabanta, Nicolás Maduro, wata ‘yar Majalisar Wakilai daga California, Maxine Waters, ta nuna cewa matakan Trump na iya sake janyo batun tsige shi.
Ta ce ‘yan Democrat ba za su iya yin shiru ba idan aka fuskanci matakai masu tsanani daga gwamnatin Trump, lamarin da ke kara zafafa rade-radin siyasa a Amurka.
Jirgin Amurka ya sauka a Abuja
A wani labarin, mun kawo muku cewa wasu bayanai sun nuna cewa jirgin sojan Amurka ya sauka a birnin tarayya Abuja a Najeriya.
Rahotanni da Legit Hausa ta samu ya nuna cewa jirgin ya sauka ne cikin dare da misalin karfe 11:00 amma ya tashi ba da dadewa ba.
Wani mai sharhi kan lamuran tsaro a yankunan Afrika ya bayyana cewa jirgin ya taso ne daga kasar Senegal, inda ya dan ya da zango a Abuja.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


