An Yi Babban Rashi: Wata Fitacciyar Jarumar Fim Ta Rasu Ta na da Shekaru 91 a Faransa

An Yi Babban Rashi: Wata Fitacciyar Jarumar Fim Ta Rasu Ta na da Shekaru 91 a Faransa

  • Brigitte Bardot, fitacciyar jarumar fina finan Faransa da ta zama zakara wajen kare hakkin dabbobi, ta rasu tana da shekaru 91
  • Bayan barin harkar fim a 1973, ta sadaukar da rayuwarta wajen fafutukar ceto dabbobi ta hanyar kafa babbar gidauniyar taimako
  • Shugaba Emmanuel Macron ya jinjina wa jarumar a matsayin wata alamar yanci da fasaha wadda ta bar tarihi mai dorewa a Faransa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Faransa - Fitacciyar jarumar fina-finan Faransa, Brigitte Bardot, wadda ta kasance tamkar silar sauya tunani kan yanci a shekarun 1950 da 1960, ta riga mu gidan gaskiya tana da shekaru 91.

Gidauniyar da ta kafa ta sanar da rasuwarta a ranar Lahadi, inda ta bayyana cewa jarumar ta rasu ne bayan ta sadaukar da babban sashen rayuwarta wajen kare haƙƙin dabbobi maimakon ci gaba da shaharar da ta samu a fagen fina-finai.

Kara karanta wannan

'Sai naga karshen shekarar 2025': Jarumar fim ta mutu awa 24 da yin bidiyo

Fitacciyar jarumar fina finan Faransa, Brigitte Bardot ta mutu.
Jaruma Brigitte Bardot ta na wasa da kare a wajen daukar fim din The Midday Ghost, a kusa da Rome. Hoto: Bettmann / Contributor
Source: Getty Images

Bardot: Fitacciyar jarumar fim ta rasu

Ko da yake an kwantar da ita a asibiti a watan Oktoba, gidauniyar ba ta bayyana takamaiman lokaci ko wurin da jaruma Brigitte Bardot ta yi numfashinta na ƙarshe ba, in ji rahoton BBC.

Bardot, wadda aka haifa a ranar 28 ga Satumba, 1934 a birnin Paris, ta zama tauraruwa a duniya bayan fitowarta a fim ɗin "And God Created Woman" a shekarar 1956.

Ta fito a fina-finai kusan 50 kafin ta yanke shawarar hannu matsugunni.

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya bayyana ta a matsayin "gagarumar jaruma" ta ƙarni na 20, wadda ta wakilci rayuwar yanci da kishin ƙasa.

Sadaukar da rayuwa wajen kare haƙƙin dabbobi

Babban sauyi a rayuwar Bardot ya faru ne lokacin da ta haɗu da wata akuya a wurin ɗaukar fim ɗinta na ƙarshe. Domin ceton akuyar daga kisa, ta saye ta har ma ta ajiye ta a ɗakin otal ɗinta.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta fadi ainihin dajin da bama baman Amurka suka sauka a Najeriya

Wannan ya sa ta kafa gidauniyar "Brigitte Bardot Foundation" a shekarar 1986, wadda a yanzu take da masu ba da gudummawa kusan 70,000 da ma'aikata 300.

Ta bayyana cewa shaharar da ta samu a matsayinta na jaruma ita ce ta ba ta damar yin fafutukar kare dabbobi, a cewar rahoton The Guardian.

Brigitte Bardot, jarumar fina finan Faransa ta rasu tana da shekaru fiye da 90
Jaruma Brigitte Bardot ta ziyarci sansanin karnukanta a ranar 7 ga Oktoba, 2001, a Faransa. Hoto: Charly Hel/Prestige / Contributor
Source: Getty Images

Jarumar ta bar fim, ta koma kula da dabbobi

A shekarun baya, jarumar fim Bardot ta yi rayuwar kaɗaici a gidanta da ke Saint-Tropez, inda take kewaye da tsirrai da dabbobi maimakon mu'amala da mutane.

A wata tattaunawa da ta yi a shekarar 2024, ta bayyana cewa tana alfahari da matakin da ta ɗauka na barin harkar fim domin fuskantar abin da take ƙauna.

Rasuwarta ta bar babban gibi ga masana'antar nishaɗi ta duniya da kuma ƙungiyoyin kare haƙƙin dabbobi waɗanda ta jagoranta na tsawon shekaru da dama.

Jaruman Kannywood da suka rasu a 2025

A wani labari, mun ruwaito cewa, yayin da Kannywood ke fitar da ƙayatattun fina-finai masu inganci, a ɗaya ɓangaren kuma, masana'antar ta yi rashin wasu manyan jarumai biyar.

Kara karanta wannan

Halin da mazauna kauyen Sokoto ke ciki a yanzu bayan harin Amurka

Masana'antar shirya fina finan Hausa ta shiga alhinin mutuwar jaruman yayin da wasunsu suke tsaka da taka rawa a wasu ayyuka, lamarin da ya sa aka maye gurbinsu da wasu.

Daga cikin jarumai biyar da suka yi bankwana da duniya a 2025, akwai Maijidda Muhammad, wadda aka fi sani da Fulani a shirin fim mai dogon zango na Labarina, da Malam Nata'ala.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com