UAE: Daular Larabawa Ta Gamu da Mummunan Iftila'i, Al'amura Sun Tsaya Cak a Birane
- Mamakon ruwan sama da ya sauka ya jawo ambaliya a Dubai da Sharjah, lamarin da ya haddasa sokewa da jinkirta tashin jiragen sama
- Kamfanoni da filayen jiragen sama sun fuskanci matsala yayin da hanyoyi suka cika da ruwa, wanda ya tilasta hakura da zirga zirga
- Wannan lamari ya tuno da mummunar ambaliyar da ta afku a Daular Larabawa a 2024 bayan saukar ruwa mafi yawa a tarihin kasar
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Dubai - Hukumomin filayen jiragen sama a Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) sun soke ko jinkirta tashin jirage da dama bayan afkuwar mummunar ambaliyar ruwa.
An ce wani mamakon ruwan sama mafi karfi da ya sauka a kasar a ranar Juma’a ne ya hadda ambaliyar da ta nutsar da hanyoyi a manyan birane.

Source: Getty Images
An samu ambaliyar ruwa a Daular Larabawa
Kamfanin jiragen sama na Emirates da ke Dubai ya soke tashin jiragensa 13 a ranar Juma’a, 19 ga Disamba, 2025, in ji rahoton Channels TV.
An kuma samu jinkiri da karin soke tashin jirage a filin jirgin saman Sharjah sakamakon ruwan sama da aka yi tun da daddare, wanda ya zo hade da walƙiya da tsawa mai karfi.
A Sharjah, babbar hanya ta birnin ta cika da ruwa da sassafe, inda aka ga mutane sun cire takalmansu, suna tafiya cikin ruwan a hankali.
An kuma hango wani mutum a saman kekensa yana kokarin tsallaka titi, wanda ruwan ya shanye tayoyin kekensa, alamar da ke nuna zurfin ruwan.
Ambaliya ta tilasta mutane zaman gida
Abubuwan da suka faru sun tuna wa mutane irin ambaliyar da ta afku a daular a watan Afrilun 2024, lokacin da ruwan sama mafi yawa a tarihi ya haddasa cunkoso da soke fiye da jirage 2,000 a babban filin jirgin saman Dubai.
Tun a ranar Alhamis, ‘yan sandan Dubai suka gargadi mazauna biranen daular da su zauna a gida sai idan akwai bukatar fita ta gaggawa, yayin da ake sa ran zuwan mamakon ruwan sama.
Da Asubar ranar Juma’a, an ga motocin tsaftace muhalli suna aiki a sassan Dubai domin share hanyoyin da suka toshe manyan magudanun ruwa, in ji rahoton Punch.

Source: Getty Images
An hango mamakon ruwa a kasar UAE
Shafin yanar gizon Filayen Jiragen Sama na Dubai ya nuna cewa an samu jinkirin tashin jirage da dama, yayin da aka soke tashin wasu.
Ofishin mai magana da yawun filayen jiragen saman Dubai ya ce an soke ko kuma an jinkirta tashin wasu jirage ne sakamakon yanayi mara kyau.
Cibiyar kula da yanayi ta UAE ta riga ta yi gargadin cewa za a samu ruwan sama daga Alhamis zuwa Juma’a a sassan kasar, ciki har da Dubai da babban birnin kasar, Abu Dhabi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

