'Yan Bindiga Sun Kashe Dalibai a Jami'ar Amurka, Trump Ya Magantu a Fusace

'Yan Bindiga Sun Kashe Dalibai a Jami'ar Amurka, Trump Ya Magantu a Fusace

  • Shugaba Donald Trump ya nuna alhini kan kisan dalibai biyu da raunata wasu a jami’ar Brown, yana mai cewa abin ya girgiza kasar
  • Lamarin ya sake tayar da muhawara a Amurka kan tsaurara dokokin bindiga, yayin da ‘yan siyasa ke kira da a dauki matakan gaggawa
  • Jami’an tsaro sun saki mutumin da aka tsare a karon farko, bayan bincike ya karkata zuwa wata hanya ta dabam game da harin

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America – Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi jimamin mutuwar mutane biyu tare da jikkata wasu tara a wani harbin bindiga da ya faru a jami’ar Brown.

Trump ya bayyana hakan ne yayin liyafa a Fadar White House, inda ya ce ya wajaba a fara taron da addu’a da girmamawa ga wadanda suka rasa rayukansu.

Kara karanta wannan

Ministan sadarwa ya fadi me ya sa ba a kama 'yan bindiga masu kira da waya

Trump da wajen jami'ar Brown
Donald Trump da jami'ar Brown da aka kai wa hari a Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

CNN ta rahoto cewa ya bayyana jami’ar Brown a matsayin wata babbar makaranta mai matukar daraja, yana mai cewa irin wadannan abubuwa masu tayar da hankali na iya faruwa a ko’ina.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Martanin Trump bayan harin 'yan bindiga

A jawabin da ya yi, Trump ya ce wadanda suka mutu yanzu suna “kallonmu daga Aljanna,” yana mai nuna alhini da ta’aziyya ga iyalansu da al’ummar jami’ar.

Ya ce abin da ya faru a Brown jami’a ce mai tarihi da suna a duniya, kuma lamarin ya nuna irin kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta.

Jami'ar da aka kai hari Amurka
Jami'ar Brown da aka kai hari a Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Jawabin nasa ya zo ne a daidai lokacin da ake kara samun rahotannin harbe-harbe masu yawa a sassan Amurka a wannan shekara.

Karuwar hare-hare a kasar Amurka

Rahotanni sun nuna cewa harbin da ya faru a jami'ar Brown ya kara adadin manyan harbe-harbe a Amurka zuwa daruruwa a cikin shekarar 2025 kadai.

The Guardian ta rahoto cewa lamarin ya sake tayar da muhawara mai zafi kan ko ya kamata gwamnatin kasar ta dauki tsauraran matakai game da dokar mallakar bindiga.

Kara karanta wannan

An tsorata Bello Turji ya mika wuya bayan sojoji sun kashe mataimakinsa

Sanata Chris Murphy, dan jam’iyyar Democrat daga jihar Connecticut, ya kwatanta abin da ya faru da harbin Sandy Hook na shekarar 2012, yana mai cewa irin wadannan hare-hare na da muni.

An saki wanda aka kama a Amurka

A wani bangare na ci gaban bincike, magajin garin Providence, Brett Smiley, ya bayyana cewa an saki mutumin da aka tsare tun farko dangane da harin.

Babban lauyan jihar Rhode Island, Peter Neronha, ya ce shaidu sun nuna cewa bincike ya karkata zuwa wata hanya dabam, don haka babu dalilin ci gaba da tsare mutumin.

Shugaban ‘yan sanda, Oscar L. Perez, Jr., ya ce an samu bayanai daga jama’a, kuma hukumar FBI ta bi sahun bayanan kafin a gano mutumin da aka tsare.

A halin da ake ciki, jami’ar Brown ta dakatar da karatu da jarabawa, yayin da dalibai da mazauna birnin Providence suka gudanar da taron tunawa domin nuna hadin kai da juna.

An kashe sojojin Amurka a Syria

A wani labarin, mun kawo muku cewa wasu da ake zargi 'yan kungiyar ISIS ne sun kashe sojojin Amurka biyu da wani jami'i.

Kara karanta wannan

Sababbin jakadu: Mutane 5 da Tinubu ya nada da suka fuskanci manyan zarge zarge

Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi Allah wadai da kashe sojojin kasar da aka yi a wani sako da ya nuna cewa ya fusata.

Trump ya kara da cewa Amurka za ta dauki fansa game da harin da aka kai kan jami'anta, yana mai cewa 'yan ISIS za su dandana kudarsu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng