Hankalin Trump Ya Tashi, Kungiyar ISIS Ta Kashe Sojojin Amurka a Tsakiyar Syria

Hankalin Trump Ya Tashi, Kungiyar ISIS Ta Kashe Sojojin Amurka a Tsakiyar Syria

  • Sojojin Amurka biyu da wani mai fassara farar hula sun mutu bayan wani dan ISIS ya kai hari kan dakarun hadin gwiwar Amurka da Syria
  • Ma'aikatar tsaron Amurka ta ce harin kwanton bauna a Palmyra ya jikkata wasu sojoji uku, inda jami’an tsaro suka hallaka wanda ya kai harin
  • Harin shi ne na farko tun bayan kifar da Bashar al-Assad, yayin da hukumomin Syria ke gargadin yiwuwar kutsen mayakan ISIS a hamada

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Damascus – Sojojin Amurka biyu tare da wani mai fassara farar hula sun mutu a tsakiyar Syria a ranar Asabar bayan wani da ake zargin dan kungiyar ISIS ne ya bude musu wuta.

Kafafen yada labaran gwamnatin Syria sun ruwaito cewa an kai harin ne a birnin Palmyra, wanda ya jikkata sojojin Amurka da na Syria.

Kara karanta wannan

'Yana kan daidai': Gumi ya goyi bayan Matawalle, ya fadi tasirinsa a Zamfara

Wani dan kungiyar ISIS ya kashe sojojin Amurka a cikin tsakiyar Syria.
Sojojin Amurka a makabartar Arlington da ke Virginia. Hoto: BRENDAN SMIALOWSKI/AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Dan kungiyar ISIS ya kashe sojojin Amurka

Hedikwatar rundunar sojin Amurka ta yankin Gabas ta Tsakiya, wato US Central Command (CENTCOM), ta tabbatar da wannan harin a sakon da ta wallafa a shafinta na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

CENTCOM ta ce:

"A ranar 13 ga Disamba, 2025, wani dan kungiyar ISIS ya hallaka sojojin Amurka biyu da wani farar hula tare da jikkata wasu uku, a harin kwanton bauna da ya kai masu a Syria.
"Sojoji sun yi musayar wuta da dan bindigar kuma an kashe shi. Saboda girmamawa, za a boye sunan sojojin da aka kashe na tsawon awanni 24 har sai an sanar da iyalansu."

Martanin hukumomin tsarom Amurka

Mai magana da yawun Ma’aikatar Tsaron Amurka, Sean Parnell, ya ce harin ya faru ne yayin da sojojin ke “ganawa da manyan shugabanni” domin tallafa wa ayyukan yaki da ta’addanci.

Jakadan Amurka a Syria, Tom Barrack, ya ce harin ya shafi “dakarun hadin gwiwar gwamnatin Amurka da Syria.”

Kara karanta wannan

Babbar magana: Wani bam da aka dasa a kan titi ya tashi da mutane a Zamfara

Shi ma Sakataren Tsaron Amurka, Pete Hegseth, ya rubuta a shafinsa na X cewa:

“Mugun mutumin da ya aikata wannan hari an kashe shi ta hannun dakarun kawance.
"Muna so ku sani da babbar murya cewa, duk wanda ya farmaki 'yan Amurka, ko a ina suke, zai kare 'yar rayuwarsa da sanin cewa Amurka za ta farauce shi har sai ta kashe shi."

Gargadin kutsen mayakan ISIS

Wani jami’in sojan Syria da ya nemi a sakaya sunansa ya ce an kashe sojojin ne “a lokacin wani taro tsakanin jami’an sojin Syria da Amurka” a wani sansanin soji a Palmyra.

Dan ISIS din ya harbe sojojin Amurka ne a taron dakarun hadin gwiwar Amurka da Syria.
Sojojin Amurka a bakin aiki. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Wani shaida ya ce ya ji karar harbe-harbe daga cikin sansanin. Sai dai wani jami’in Pentagon da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa AFP cewa harin “ya faru ne a yankin da shugaban Syria ba ya da cikakken iko a kai.”

Mai magana da yawun Ma’aikatar Cikin Gida ta Syria, Anwar al-Baba, ya ce an riga an yi gargadi ga dakarun kawance game da yiwuwar “kutsen ISIS” a yankin hamada.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tarwatsa Fulani makiyaya da harbi, an sace shanu 168 a Filato

Kungiyar sa ido don kare 'yan cin dan Adam a Syria ta ce taron ya zo ne a matsayin wani bangare na dabarar Amurka na karfafa tasirinta a hamadar Syria.

SANA ta kara da cewa jiragen sama masu saukar ungulu sun kwashe wadanda suka jikkata zuwa sansanin Al-Tanf a kudancin Syria, inda sojojin Amurka ke zama a karkashin kawancen duniya na yaki da ISIS.

Amurka ta tare jirgin China a hanyar Iran

A wani labari, mun ruwaito cewa, sojojin Amurka sun kai samame kan wani jirgin kaya da ke kan hanyarsa daga China zuwa Iran.

An ce hakan wani mataki ne da ake ganin yana kara tsaurara matsin lambar da gwamnatin shugaba Donald Trump ke yi a teku.

Bayan kwace kayayyakin, an bar jirgin ya ci gaba da tafiyarsa, abin da ya nuna cewa ba a tsare jirgin gaba daya ba a lokacin.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com