Hotuna: Yadda sojojin saman Najeriya suka kera sabon jirgin sama mai saukar Ungulu

Hotuna: Yadda sojojin saman Najeriya suka kera sabon jirgin sama mai saukar Ungulu

- Sojojin saman Najeriya sun kera wani sabon jirgi mai saukar ungulu

- Sojojin sun kera jirgin ne a garin Fatakwal, inda shugaban hukumar sojin kasar ya halarci wajen domin gabatar da jirgin

- Shugaban ya bayyana cewa wannan cigaba da aka samu ba karamin tasiri zai yi ba wajen yaki da masu tada zaune tsaye

Sojojin saman Najeriya sun sake kera wani sabon jirgin sama mai saukar Ungulu, wanda suka samu nasarar hada tare da wasu injiniyoyi na gida Najeriya da kuwa wasu daga kasashen ketare.

An gabatar da sabon jirgin ne yau Asabar 24 ga watan Agusta a garin Fatakwal, inda aka bayyana irin cigaban da ake samu daga wajen sojojin Najeriya wajen kere-kere na fasaha.

Hotuna: Yadda sojojin saman Najeriya suka kera sabon jirgin sama mai saukar Ungulu
Hotuna: Yadda sojojin saman Najeriya suka kera sabon jirgin sama mai saukar Ungulu
Asali: Facebook

Idan ba a manta ba a shekarar 2018 shugaban rundunar sojin saman na Najeriya, Air Marshal Abubakar Sadique, yaje garin Fatakwal domin halartar gabatar da jirgi irin wannan, wanda shine karo na biyu da aka taba yin irin wannan a kasar tun lokacin da tsofaffin sojojin saman da suka kera wani jirgi a shekarar 2000.

Hotuna: Yadda sojojin saman Najeriya suka kera sabon jirgin sama mai saukar Ungulu
Hotuna: Yadda sojojin saman Najeriya suka kera sabon jirgin sama mai saukar Ungulu
Asali: Facebook

KU KARANTA: To fah: An kama wani Malamin sakandare da yake takura daliban shi su tura masa hotunansu tsirara haihuwar uwarsu

A bayanin da yayi a wajen wannan taro, shugaban sojojin saman ya bayyana cewa wannan cigaba da ake samu a fannin kere-keren jirgi ba karamin tasiri zai yi ba wajen kawo karshen 'yan ta'adda da kuma dawwamar da zaman lafiya a Najeriya.

Hotuna: Yadda sojojin saman Najeriya suka kera sabon jirgin sama mai saukar Ungulu
Hotuna: Yadda sojojin saman Najeriya suka kera sabon jirgin sama mai saukar Ungulu
Asali: Facebook

Sannan shugaban sojojin yayi alkawarin inganta rayuwar jami'an sojin sama na kasar nan baki daya, inda a karshe yayi musu fatan alkhairi.

Hotuna: Yadda sojojin saman Najeriya suka kera sabon jirgin sama mai saukar Ungulu
Hotuna: Yadda sojojin saman Najeriya suka kera sabon jirgin sama mai saukar Ungulu
Asali: Facebook

Kafin ya bar garin Fatakwal din shugaban ya tsaya ya gana da manyan jami'an sojojin sama na kasar nan, inda suka yi magana dangane da yadda za a kawo cigaba a wannan hukuma.

Hotuna: Yadda sojojin saman Najeriya suka kera sabon jirgin sama mai saukar Ungulu
Hotuna: Yadda sojojin saman Najeriya suka kera sabon jirgin sama mai saukar Ungulu
Asali: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel