Ta Faru Ta Ƙare, Donald Trump Ya Hana Ƴan Ƙasashe 19 Shiga Amurka, An Saki Sunaye
- Gwamnatin Donald Trump ta dakatar da karɓar dukkan 'yan hijira daga ‘yan ƙasashe 19, tana mai cewa tsaron Amurka ya fi komai muhimmanci
- Sabon takunkumin ya shafi masu neman Green Card da shaida zama 'yan Amurka, musamman daga ƙasashen da aka sanya wa takunkumi
- Matakin ya biyo bayan harin da wani ɗan Afghanistan ya kai wa sojojin Amurka a Washington, abin da ya harzuka Trump kan bakin kasar
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Amurka - Gwamnatin Donald Trump, ta ba da umarnin gaggawa na dakatar da karbar dukkanin sababbin takardun neman izinin shiga Amurka daga ƙasashe 19.
Wannan matakin ya fito ne daga wata takarda mai shafuka huɗu da hukumar shige da fice da ba da izinin zama a Amurka USCIS ta fitar a ranar Talata.

Source: Twitter
An hana 'yan kasashe 19 shiga Amurka
A cewar USCIS, dakatarwar ta shafi masu neman katin kasar, da masu neman izinin zama 'yan Amurka, tare da jaddada cewa an ɗauki wannan mataki ne don ƙara tsaurara binciken tsaro, in ji rahoton Reuters.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Takardar ta ce:
“Mun fahimci cewa wannan mataki zai iya janyo tsaiko ga wasu aikace-aikace na masu son shiga Amurka. Amma wannan jinkiri ya dace idan aka kwatanta da wajibcin kare tsaron ƙasa.”
Matakin ya shafi ‘yan ƙasashe 19 da Trump ya saka wa takunkumin shiga Amurka tun watan Yuni, ciki har da:
- Afghanistan
- Iran
- Libya
- Somalia
- Sudan
- Yemen
Sai kuma wasu ƙarin ƙasashe bakwai da ke ƙarƙashin takumkumi na musamman, ciki har da:
- Cuba
- Laos
- Sierra Leone
- Venezuela
Matakin Trump bayan harin Washington DC
Trump ya dauki wannan mataki ne kwanaki kaɗan bayan da wani mutumi ya bude wa sojojin kasar biyu wuta, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar ɗaya, ɗaya kuma ya jikkata sosai.
An gurfanar da wanda ake zargi — dan asalin Afghanistan wanda ya shiga Amurka a zamanin gwamnatin Biden — a kotu ranar Talata, inda ya ce bai aikata laifin komai ba.
Rahotannin NBC sun nuna cewa hukumar ta yi gargadin cewa tun da akwai shari’o’in neman mafaka sama da miliyan 1.4, akwai yiwuwar wannan dakatarwa ta janyo dogon tsaiko ga dubban mutane.
Kakakin USCIS ba ta mayar da martani kan tambayoyin manema labarai ba zuwa daren Talata, 2 ga watan Disamba, 2025.

Source: Facebook
Hukumomi sun goyi bayan karin takunkumi
Daraktan USCIS, Joseph Edlow, ya soki tsarin tantance ‘yan Afghanistan da suka shigo bayan janyewar Amurka daga ƙasar a 2021, yana mai cewa:
“Ba a tantance su yadda ya kamata ba.”
Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida (DHS), ƙarƙashin Kristi Noem, ta yi kira da a ƙara tsaurara matakan shigar bakin haure kasar.
A wani sako da ta wallafa a shafinta na X, Kristi Noem ta ce:
“Na gana da shugaban kasa.
"Na ba da shawarar a dauki cikakken takunkumi ga duk wata ƙasa da ke turo mana da masu aikata laifi, masu dogaro da taimakonmu, da masu zamar mana kaska a kasa.”
Trump zai dauki mataki kan 'Third World'
A wani labari, mun ruwaito cewa, Donald Trump ya ce tsarin hijira zuwa Amurka ya haddasa matsaloli ga tsaro, da cunkuso a makarantu, asibitoci da gidaje.
Trump ya yi misali da jihar Minnesota, inda ya ce ce ’yan hijira daga Somalia sun canja tsarin rayuwar jihar ta hanyar abin da ya kira “tasiri marar kyau”.
Shugaban kasa Trump ya ce zai dakatar da shigowar masu neman zama a Amurka daga ƙasashe masu tasowa, da suka shafi Afrika, Asia da Latin Amurka.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


