Yadda Kashe Musulmai a Gaza ke Saka Turawa Shiga Musulunci
- Sabon binciken IIFL ya gano cewa rikice-rikicen duniya, musamman na Isra’ila da Gaza, na daga cikin manyan dalilan da ke sa 'yan Britaniya shiga cikin Musulunci
- Masu binciken sun ce matasa da dama suna ganin duniya “ta zama ba dai-dai ba kan zuba ido ana kashe mutane”, lamarin da ke ƙara musu sha’awar Musulunci
- Bayanan kididdigar sun nuna cewa Kiristanci ne addinin da mutane suka fi karancin shiga a Birtaniya tare da kawo wasu dalilai da suka ce su suka haifar da hakan
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Britain - Sabon rahoto ya gano cewa rikice-rikicen duniya suna taka muhimmiyar rawa wajen janyo hankalin mutane zuwa Musulunci.
Wannan rahoto, wanda cibiyar IIFL ta wallafa, ya yi nazari kan mutane sama da 2,000 waɗanda suka canja addininsu zuwa wani daban.

Source: Getty Images
Rahoton The Telegraph ya ce binciken ya ce akwai yiwuwar alaƙa tsakanin karuwar sha’awar Musulunci da tashin hankali da ya shafi al’ummomin Musulmi a kasashen duniya, musamman rikicin Isra’ila da Gaza.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Masu binciken sun ce maganganun da ake yawan ji a kafofin watsa labarai na cewa mutane suna komawa Musulunci saboda adalci da damuwa kan zalunci “na iya zama gaskiya”.
Abin da ke saka Turawa shiga Musulunci
Masu binciken IIFL sun gano cewa kaso 20 na waɗanda suka koma Musulunci sun ce rikice-rikicen duniya ne suka fi tasiri wajen yanke shawarar su.
Rahoton Yahoo News ya ce sau da yawa suna ganin abubuwan da ke faruwa a duniya na nuna “rashin adalci” da kuma yadda Musulmi ke fuskantar zalunci.
A cewar rahoton:
“Masu canza addini zuwa Musulunci sun bayyana cewa rikice-rikicen duniya da kuma fahimtar rashin adalci sun taka rawa ga imaninsu.”
Hakan, a cewar masu binciken, ya nuna suna goyon bayan bayanan da aka rika gani a 2023 da 2024 na karuwar mutane da ke komawa Musulunci musamman bayan tashin tashinar rikicin Isra’ila da Gaza.

Source: Getty Images
Wasu abubuwan da ke jawo canza addini
Ga Kiristoci, rahoton ya nuna cewa mutuwar 'yan uwa ko aboki da kuma matsalolin lafiyar kwakwalwa ne manyan dalilan da ke sanya mutane sauya addini.
A wasu addinai kamar Hindu, Buddha ko Sikh, dalilan sun fi karkata zuwa matsalolin tunani da rikicin rayuwar duniya.
Rahoton ya kuma ce akwai yuwuwar batun rasa masoya a lokacin annobar COVID-19 ya sa wasu suka koma Kiristanci.
IIFL ta gano cewa kaso mafi yawa na masu sauya addini sun bar Kiristanci gaba ɗaya. Kashi 39 sun rabu da addini kwata-kwata.
“Babban sauyin da ake samu shi ne barin addini gaba ɗaya, fiye da komawa wani sabon addini.”
Falasdinawa 54 sun angwance a Gaza
A wani rahoton, kun ji cewa an yi wani gagarumin biki a Gaza, inda aka daurawa Falasdinawa sama da 50 aure a makon da ya wuce.
Hakan na zuwa ne bayan tsagaita wuta da aka yi a Gaza duk da ana zargin Isra'ila da cigaba da kai hare hare wasu yankunan Falasdinawa.
Wata gidauniya ta tallafawa da yawa daga cikin Falasdinawa da kudi da wasu kayayyaki kuma sun bayyana farin cikinsu ga abin da aka musu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


