Babbar Magana: Rasha Ta Ce a Shirye Ta ke Ta Gwabza Yaki da Kasashen Turai
- Bayan ganawar sa’o’i biyar da wakilan Donald Trump, ba a samu gagarumin ci gaba ba a tattaunawar zaman lafiya tsakanin Rasha da Amurka ba
- Vladimir Putin ya zargi kasashen Turai da hana samun zaman lafiya tare da cewa Rasha “shirye ta ke ko yau ko gobe” idan aka far mata da yaki
- Ministan harkokin wajen Amurka, Marco Rubio, ya ce an samu ɗan cigaba kan batun tsaron Ukraine, amma har yanzu ana fuskantar kalubale
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Moscow, Rasha – Tattaunawar sasanci tsakanin Rasha da Amurka kan rikicin Ukraine ta ƙare ba tare da wani gagarumin ci gaba ba, kamar yadda hadidimn Vladimir Putin, Yuri Ushakov, ya bayyana.
Ganawar, wadda ta ɗauki kusan sa’o’i biyar da wakilan gwamnatin Trump – Steve Witkoff da Jared Kushner – ta zo ne a lokacin da shugaban Rasha, Vladimir Putin, ya ce ƙasarsa “shirye take ta fuskanci Turai” idan har rikici ya tashi.

Source: Getty Images
The Guardian ta ce Putin ya bayyana cewa kasashen Turai ne ke hana Amurka cimma yarjejeniyar zaman lafiya, yana mai cewa ba za su karbi sharudansu wajen tsayar da yakin ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayanan Rasha bayan zama da Amurka
Duk da cewa Amurka ta ce an samu ɗan cigaba kan batun tsaron Ukraine, rahotanni sun nuna cewa bangarorin biyu sun kasa cimma matsaya kan muhimman batutuwa.
Yuri Ushakov da ya yi magana da kafafen yada labaran Rasha bayan ganawar, ya ce:
“Ba a gano bakin zaren warware rikicin Ukraine ba… har yanzu akwai aikin mai yawa.”
Ya ce tattaunawar ta kasance mai amfani sosai, amma hakan bai kai ga samun matsaya game da muhimman batutuwa ba.
A cewar sa:
“Ba mu tattauna takamammen tayin Amurka ba… amma mun tattauna abin da ke kunshe a cikin takardun.”
Ushakov ya kuma bayyana cewa wasu sashe na tattaunawar ba za a bayyana su ga jama’a ba, sannan ba a hango wani gagarumin taro tsakanin Putin da Trump nan kusa ba.

Source: Getty Images
A wani bangaren, ministan harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya ce an samu ɗan ci gaba, musamman kan samun tabbacin tsaro ga Ukraine.
Rasha ta ce ta shirya yaki da Turai
Rahoton Reuters ya nuna cewa kafin fara tattaunawa da Amurka, Putin ya yi kakkausar suka ga kasashen Turai, yana cewa:
“Turai ne ke hana Amurka shawo kan rikicin Ukraine… Rasha ba ta son yaki da Turai, amma idan suka fara, to muna shirye."
A gefe guda, Putin ya yi ikirarin cewa sojojin Rasha sun kwace birnin Pokrovsk, wani muhimmin sansanin dabarun tsaro na Ukraine.
Rasha ta yi magana game da Najeriya
A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin kasar Rasha ta yi magana kan barazanar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi wa Najeriya.
Rahotanni sun nuna cewa Rasha ta ce tana saka ido tare da bibiyar duk abubuwan da suke faruwa a Najeriya game da tsaro da zargin da Trump ya yi.
Shugaba Donald Trump ya yi zargin cewa ana yi wa Kiristoci kisan kare dangi a Najeriya, wanda a kan haka ya yi barazanar daukar matakin soji.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


