Dogon Dare: Wani Birni a Amurka ba Zai Sake Ganin Hasken Rana ba har Sai a 2026

Dogon Dare: Wani Birni a Amurka ba Zai Sake Ganin Hasken Rana ba har Sai a 2026

  • Utqiagvik, wani gari da ke a Arewacin Amurka ya shiga dogon dare inda rana ba za ta sake fitowa ba na tsawon kwanaki 64
  • Masana sun ce duk da cewa rana ba za ta fito ba, amma gajimare na ba da wani haske da ke kama da hasken alfijir a garin
  • Masana kiwon lafiya sun bayyana cewa dogon dare na iya shafar bacci, kuzari da sauyin yanayi ga mazauna garin Utqiagvik

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Amurka - Garin Utqiagvik da ke Arewacin Alaska ya shiga wani yanayi na musamman da ake kira Polar Night (dogon dare) inda rana za ta daina fitowa gaba daya na tsawon kwanaki fiye da 60

A ranar 18 ga watan Nuwamba, 2025 ne rana ta fadi a Utqiagvik, karo na karshe a 2025, inda ake sa ran za ta sake fitowa a ranar 22 ga Janairu, 2026.

Kara karanta wannan

Sojar Amurka ta rasu bayan harin da dan bindiga ya kai musu, Trump ya fusata

An shiga dogon dare a garin Utqiagvik da ke birnin Alaska, inda rana ba za ta sake fitowa ba sai 2026.
Yayin garin Storsteinen, Tromsdalen a Norway, lokacin da dogon dare ya fara a ranar 14 ga Janairun 2025. Hoto: NurPhoto via Getty Images
Source: Getty Images

Wannan al’amari ya faru ne saboda tsarin juyawar duniya, wanda ke sa yankunan da ke cikin Arctic Circle su fada cikin duhu na dogon lokaci, in ji rahoton Fox Weather.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Utqiagvik: An shiga duhu a birnin Alaska

Duk da haka, masana sun ce ba lallai garin ya kasance cikin tsananin duhu ba, domin za a iya samun dan haske daga sararin samaniya, amma ba na rana ba.

Masana sun bayyana cewa koda ace rana ba za ta fito kai tsaye ba, hasken da ke kusa da sararin samaniya kan bada dan haske mai kama da na alfijir.

Dusar ƙanƙara, giza-gizai da bakan gizo na yankin kan kara taimakawa wajen ba wannan gari haske, yayin da ya ke cikin daren Polar.

Garin Utqiagvik ya yi suna wajen samun wannan yanayi saboda yana Arewacin Alaska, kusan mil 500 daga Fairbanks, inda sauyin juyarwar duniya ya fi shafa.

Kara karanta wannan

Ana jimamin sace dalibai, 'yan bindiga sun sake yin awon gaba da mutane a Neja

Yadda Polar Night ke tasiri ga yanayi a Utqiagvik

Rashin hasken rana yana sa yanayi ya sauya zuwa matukar sanyi a Arewacin duniya, kamar yadda rahoton The Telegraph ya nuna.

Masana sun ce wannan duhu ne ke taimakawa wajen gina polar vortex, watau wani curin hadari na sanyi da ke taruwa a saman sararin samaniya.

A wasu lokuta, wannan hadari na sanyi kan zubo da dusar kankara zuwa kudancin duniya, kuma ya janyo matsanancin sanyi a wasu jihohi na Amurka.

A lokacin rani kuwa, yankin yana samun kusan watanni uku na hasken rana ba tare da dare ya shiga ba.

Mazauna garuruwan da ake dogon dare sun ce suna jin dadin yanayin, don suna samu wadataccen bacci.
Masu yawan bude ido na daukar hotunan garin Storsteinen da ke Norway, lokacin da aka shiga dogon dare. Hoto: NurPhoto via Getty Images
Source: Getty Images

Yadda mutane ke rayuwa cikin dogon duhu

Rayuwa cikin kusan kwanaki 64 na duhu na bukatar daukar matakai daga mazauna irin wannan yanki, kamar dai garin Utqiagvik.

Rahotannin kiwon lafiya sun nuna cewa rashin fitowar rana kan rikita tsarin bacci da dankon jiki, yana rage kuzari da karfin aiki.

Kara karanta wannan

"Mun san su": Sanata Maidoki ya ba gwamnati zabi 2 kan kawo karshen 'yan bindiga

Mutane kan dogara da 'fitilun bature' wajen samar da haske, motsa jiki da shan Vitamin D don rage tasirin duhun ga lafiyarsu.

Wata mazaunin garin Inari da ke Finland, Esther Berelowitsch, ta taba shaidawa jaridar BBC cewa:

"Ni zan so a ce wannan daren ya wuce na watanni biyu. A nan na ke kake ganin tsantsar ikon ubangiji, yadda abubuwa ke gudana duk da babu hasken rana.
"Ina kwanciya barci da wuri, sannan ina samun wadataccen bacci, sam ba na so a ce lokacin nan ya wuce."

Sai dai wasu mazauna Arctic suna ganin wannan lokaci lokaci ne na nishaɗi, jin sanyi, haduwar iyali da kuma kallon hasken da ake kira Northern Lights a samaniya.

Kasashen duniya 6 da rana ba ta faduwa

A wani labari, mun ruwaito cewa, a wasu sassa na duniya kamar Norway, Kanada, Iceland, da Finland, rana ba ta faduwa na fiye da kwanaki 70.

Wannan abin da ke faruwa 'na musamman' yana haifar da nau'ikan hasken rana da duhu, yana daidaita salon rayuwa da ayyukan mazauna garuruwan.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamnan da ake zargi da yunkurin kifar da gwamnatin Tinubu zai kai kansa EFCC

A Svalbard da ke cikin Norway, rana tana haskakawa ba tare da fadi ba daga 10 ga Afrilu zuwa 23 ga Agusta, wanda ya maida ita yankin Arewacin Turai da mutane suka fi zama.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com