TIRKASHI: Azumi a inda rana ba ta faduwa

TIRKASHI: Azumi a inda rana ba ta faduwa

Watan Ramadana wata ne da musulmai ke kauracewa ci da sha tun daga fitowar  alfijir zuwa faduwar rana . A kasashe kamar Najeriya sa’oi kimanin 14 ne kawai ake yi na azumi

TIRKASHI: Azumi a inda rana ba ta faduwa
Faduwar Rana

Amma a wasu kasashen turai su kan kai kimanin sa’oi 20 zuwa 23 a kullum a kafin su sha ruwa. A irin wadannan kasashe rana kwana da yini ta ke yi a sama. An soma watan azumi na wannan shekara a Najeriya a ranar Litinin 6 ga watan Yuni bayan da sarkin Muslmi ya Muhammad Sa’ad Abubakar na III ya sanar da ganin wata, a inda bisa ka’ida, musulmin kasar suka tashi da azumi

Yayin da Najeriya da sauran kasashen duniya ke yini kafin su sha ruwa, wasu kasashen Turai rana bata faduwa sai ta kai kusan sa’oi 23 a sama. A kasashen da ke yankin Arctic rana ba ta faduwa har na tsawon sa’oi 24, watau kwana da yin ke nan.

A Finland wacce ta ke yankin Scandinavian, ana yiwa kasar kirari ne da ‘kasar da rana ke fitowa da tsakar dare’. Domin dare minti 55 ne kacal. Wani dan asalin Bangladesh mai suna Mohammed mazaunin Finland shi da matarsa ya ce suna yin sahur da misalign karfe 1:00 na dare, su kuma yi buda baki da misalin karfe 12:48 na washegari.

‘Yan uwansa a gida na mamakin yadda suke azumi a irin wannan matsanancin yanayi, na azumin sama da sa’oi 20 a kullum har na tsawon wata guda. Wadannan wurare a Turai, sun sha ban-ban da juna. Wani lokaci akan soma azumi da misalin 3:00 na dare, a kuma yi buda baki da misalin 9:00 na washe gari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng