Birtaniya Ta Juya Wa Tinubu Baya, Ta Ki Amincewa da Bukatarsa kan Sanata Ekweremadu

Birtaniya Ta Juya Wa Tinubu Baya, Ta Ki Amincewa da Bukatarsa kan Sanata Ekweremadu

  • Gwamnatin Birtaniya ta ki amincewa da bukatar Najeriya ta mika Sanata Ike Ekweremadu ya karisa hukuncinsa a gida
  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tura tawaga ta musamman domin a sasanta ta yadda Ekweremadu zai koma gidan yarin Najeriya
  • Sai dai wata majiya ta ce gwamnatin Birtaniya ta nuna damuwa kan yiwuwar Najeriya ta bar tsohon sanatan ya karasa hukuncinsa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

UK - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya gamu da tangarda a kokarinsa na dawo da tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu gidan yarin Najeriya.

Hakan dai ya biyo bayan matakin da Gwamnatin Birtaniya ta dauka kan bukatar gwamnatin Tinubu na bai wa Najeriya Sanata Ekweremadu domin ya karasa hukuncinsa a gida.

Sanata Ekweremadu
Hoton tsohon mataimakin shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ike Ekweremadu Hoto: Ike Ekweremadu
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa Birtaniya ta ki amincewa da gwamnatin Najeriya, ta ce a bar tsohon sanatan ya gama hukuncin da aka yanke masa a Landan.

Kara karanta wannan

Alkawarin da Amurka ta yi wa Najeriya kan matsalar rashin tsaro

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukuncin da aka yanke wa Ekweremadu

Idan ba ku manta ba, Sanata Ekweremadu na zaman ɗaurin shekaru sama da tara da aka yanke masa a Birtaniya kan laifin safarar sassan jiki.

An gurfanar da shi a watan Maris 2023, inda kotu ta yanke masa hukuncin shekaru tara da watanni takwas saboda hada-hada da shirya amfani da kodar wani matashi ba bisa ka’ida ba.

Tinubu ya tura tawaga Birtaniya

A farkon watan Nuwamba, Shugaba Bola Tinubu ya aika da tawaga ta musamman zuwa Landan domin tattauna batun Ekweremadu da yiwuwar a mika shi Najeriya ya ƙarasa hukuncinsa.

Tawagar ta haɗa da Yusuf Tuggar, Ministan Harkokin Waje, da Lateef Fagbemi, Antoni Janar (AGF) kuma Ministan Shari’a.

Sai dai jaridar UK Guardian, ta ruwaito cewa wani jami’i daga Ma’aikatar Shari’a ta Birtaniya (MoJ), ya tabbatar mata da cewa an yi watsi da bukatar Najeriya.

Birtaniya ta ki yarda da bukatar

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi ya fadi matsalar da ake fuskanta wajen kawar da rashin tsaro

Jaridar ta ce:

“Wata majiya daga MoJ ta tabbatar da cewa an ƙi amincewa da bukatar gwamnatin Najeriya.
"Gwamnatin Burtaniya na ganin cewa Najeriya ba za ta iya bada tabbacin Ekweremadu zai ci gaba da zaman gidan yarinsa bayan an mika shi ba.”
Shugaban kasa, Bola Tinubu.
Hoton shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a Aso Rock Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

A cewar wani jami’in ma'aikatar shari'a:

“Duk wata bukatar caza wa fursunoni wurin zama yana karkashin ikonmu ne, dole sai mun tantance ko hakan zai dace da adalci.”
“Birtaniya ba za ta lamunci bautarwa ta zamani ba, kuma duk mai aikata irin wadannan laifuka zai fuskanci hukunci daidai da abin da ya aikata.”

Me ya hana Shugaba Tinubu zuwa Amurka?

A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta yi karin haske kan shirin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu na kai ziyara Amurka domin gana wa da Shugaba Donald Trump.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya idan da ya ce da yiwuwar Tinubu ya tafi Amurka kan zargin yi wa kiristoci kisan kare dangi.

Kara karanta wannan

Matakai 5 da Bola Tinubu ya dauka bayan sace dalibai a Kebbi da Neja

Sai dai ya kafa sharadin cewa Tinubu zai nemi zaka da Trump ne kawai a lokacin da ya dace, inda ya uaddada cewa Najeriya na bakin kokarinta wajen dawo da zaman lafiya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262