Donald Trump Ya Tona Asirin Amurka kan Harin da Isra'ila Ta kai Iran

Donald Trump Ya Tona Asirin Amurka kan Harin da Isra'ila Ta kai Iran

  • Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa shi ne ya jagoranci harin da Isra’ila ta kai kan Iran a ranar 13, Yuni, 2025
  • A baya gwamnatin Amurka ta ce Isra’ila ta kai harin ne ba tare da hadin gwiwar Amurka ba, amma Trump ya musanta hakan
  • Harin ya yi sanadiyyar mutuwar manyan hafsoshin soja, masana nukiliya da fararen hula da dama a tsakanin kasashen biyu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Amurka – Shugaban Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa shi ne ya jagoranci harin farko da Isra’ila ta kai Iran a ranar 13, Yuni, 2025.

Bayanin Trump ya saba da bayanan farko na gwamnatin Amurka da ta ce Isra’ila ta dauki matakin ne ita kadai.

Netanyahu, Trump, Ali Khamenei
Jagororin kasashen Isra'ila, Amurka da Iran. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Al-Jazeera ta ce Trump ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da manema labarai a ranar Alhamis, inda ya ce harin Isra’ila mai karfi ne sosai kuma shi ne ya jagorance shi kai tsaye.

Kara karanta wannan

Isra'ila ta yi kira ga 'yan Najeriya yayin da ake fargabar barazanar Trump

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Trump ya ce ya san da harin Iran

A cewar Trump, ranar da Isra’ila ta kai harin ta kasance rana mai muhimmanci ga Isra’ila, saboda hari daya ya yi barna sosai.

Ya ce:

“Isra’ila ce ta fara kai hari, harin kuwa ya yi matukar tasiri. Ni ne nake da cikakken iko a lokacin.”

Rahoton Yahoo ya ce ya yi furucin ne a yayin da yake kira ga ‘yan jam’iyyarsa ta Republican su soke wata doka domin saukaka amincewa da dokoki a majalisar dattijai.

Trump ya ce ya kamata jam’iyyarsa ta dauki wannan mataki irin yadda Isra’ila ta fara yakin da Iran ba tare da bata lokaci ba.

Yadda Isra’ila ta kai hari da martanin Iran

A ranar 13, Yunin 2025, Isra’ila ta kaddamar da hari kan Iran ba tare da wani gargadi ba, inda ta kashe manyan hafsoshin soja, masana kimiyyar nukiliya da fararen hula da dama.

Biyo bayan haka, Iran ta mayar da martani ta hanyar harba daruruwan makamai masu linzami kan Isra’ila.

Kara karanta wannan

'Da gaske ne ana kisan kiyashi a Najeriya,' Jigon APC ya goyi bayan Donald Trump

Ali Khamenei
Jagoran Iran, Ali Khamenei da tawagarsa. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Bayan haka, Amurka ta shiga yakin kai tsaye tare da Isra’ila, ta hanyar kai hare-hare kan manyan cibiyoyin nukiliya uku na Iran.

Maganar da Amurka ta yi a karon farko

A farkon yakin, Ministan harkokin wajen Amurka, Marco Rubio ya bayyana cewa Isra’ila ta dauki matakin ne da kanta, kuma Amurka ba ta da hannu cikin hare-haren.

Ya kara da cewa:

“Babban abin da muke so shi ne kare sojojin Amurka da muradunmu a yankin.”

Sai dai bayan Iran ta mayar da martani da kai hari kan sansanin sojojin Amurka da ke Qatar, an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin kasashen biyu.

Iran ta kafawa Amurka sharadin sulhu

A wani labarin, mun kawo muku cewa shugaban Amurka, Donald Trump ya ce yana son samun yarjejeniya da Iran.

A martanin da Iran ta yi a farkon makon nan, ta ce ba za ta amince da zama da Amurka ba har sai kasar ta cika wasu sharuda.

Kara karanta wannan

Janye biza: Wole Soyinka ya dura kan Trump, ya kira shi mai mulkin kama karya

Daga cikin sharudan da Iran ta gindaya akwai bukatar Amurka ta yanke alaka da Isra'ila tare da janye sansanonin soja a Gabas ta Tsakiya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng