Yana Shirin Kai Hari Najeriya, Trump Ya ba da Umarni a Yi Gwajin Makaman Nukiliya
- Shugaba Donald Trump ya ba da umarnin a fara gwajin makaman nukiliya don daidaita da kasashen Rasha da China
- Ya ce Amurka za ta fara gwaje-gwaje kamar sauran ƙasashe saboda wasu na ci gaba da gwajin makaman nukiliya a bayyane
- Masu suka sun ce matakin Trump na iya tayar da sabon rikicin nukiliya, yayin da Rasha ta ce za ta dauki mataki a kai
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Amurka — Shugaba Donald Trump ya umarci ma’aikatar tsaro ta ƙasa da ta fara gwajin makaman nukiliya nan da nan, domin “daidaita karfin Amurka” da kasashen Rasha da China.
Trump ya bayyana hakan ne a shafinsa na sada zumunta jim kaɗan kafin ganawarsa da shugaban kasar China, Xi Jinping, a Koriya ta Kudu.

Source: Getty Images
Kafar watsa labaran NBC News ta ruwaito shugaban Amurka yana cewa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Saboda shirye-shiryen gwaje-gwajen wasu ƙasashe, na umurci ma’aikatar yaƙi ta fara gwajin makaman nukiliya akan tsarin da ya dace. Aikin zai fara nan da nan.”
Dalilin Trump na dawo da gwajin nukiliya
Lokacin ƙarshe da Amurka ta yi gwajin makamin nukiliya shi ne a 1992 lokacin mulkin tsohon Shugaba George H.W. Bush, wanda daga baya ya sanya doka kan irin wannan gwaji.
Trump ya ce bai yanke wannan shawara don ta zama barazana ga kowa ba, sai dai don tabbatar da cewa Amurka ba ta da nakasu a fagen karfin matakan tsaro, inji rahoton CNN.
“Amurka tana da makaman nukiliya fiye da kowace ƙasa. Rasha tana biye, China kuma tana da 'yar tazara, amma za ta iya kai karfi nan da shekaru biyar,” in ji Trump.
Ya kara da cewa:
“Muna ganin wasu ƙasashe suna ci gaba da gwaje-gwaje, mu kuma mun tsaya shekaru da dama ba gwaji. Lokaci ya yi da mu ma za mu fara yi.”
Gwajin Nukiliya: Rasha ta gargadi Amurka
Mai magana da yawun fadar Kremlin, Dmitry Peskov, ya ce Rasha ba ta da masaniyar wani gwaji daga kowace ƙasa, amma ya tunatar da cewa:
"Idan wani ya soke yarjejeniyar hana gwaje-gwaje, Rasha za ta dauki mataki a kan hakan.”
Peskov ya kara da cewa, gwajin makaman Rasha kwanan nan ba na nukiliya ba ne, yana mai cewa gwajin fasahar makamai masu nisan zango ne kawai, in ji rahoton Yahoo.

Source: Getty Images
Barazanar sabon rikicin nukiliya
Kungiyar ICAN ta bayyana cewa Rasha ce ke da mafi yawan makaman nukiliya — 5,449, yayin da Amurka ke da 5,277, watau 90% na makaman nukiliya na duniya duka suna hannunsu.
Trump dai ya fuskanci suka daga ‘yan jam’iyyar Democrat, musamman wakilai daga jihar Nevada, inda nan ne yake da tsohon wurin gwaji na nukiliya.
Masu sharhi sun ce wannan matakin na Trump na iya tayar da sabuwar gasar gwaje- gwaje da ma mallakar makaman nukiliya, wanda zai jefa duniya cikin sabon tashin hankali.
Trump na barazanar kai hari Najeriya
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Shugaba Donald Trump ya ce zai iya turo sojoji Najeriya ko jiragen yaki domin kai hari kan masu kashe Kiristoci.
Trump ya bayyana hakan ne a lokacin da manema labarai suka yi masa tambaya kan yanayin da yake tunanin zai kai hari Najeriya kamar yadda ya yi barazana.
Shugaban Amurka dai ya ce zai kai hari Najeriya ne bayan zargin cewa ana yi wa Kiristoci kisan kare dangi a kasar, abin da ya ce ba zai zuba ido yana kallo ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


