Donald Trump Ya Tafi Asibiti Duba Lafiyarsa, Amurkawa na Jefa Tambayoyi

Donald Trump Ya Tafi Asibiti Duba Lafiyarsa, Amurkawa na Jefa Tambayoyi

  • Shugaba Donald Trump zai sake yin gwajin lafiya karo na biyu a cikin shekara guda, abin da ya jawo tambayoyi daga jama’a
  • Rahotanni sun bayyana cewa Donald Trump, mai shekara 79, zai yi gwajin ne a asibitin sojoji na Walter Reed da ke kasar Amurka
  • Fadar White House ba ta bayyana dalilin sake gwajin lafiyar ba, duk da cewa an riga an duba shi da farko a watan Afrilun 2025

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Amurka – Shugaban Amurka, Donald Trump, zai sake yin gwajin lafiya a karon biyu a cikin shekara guda.

Lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce game da lafiyarsa da kuma gaskiyar bayanan da Fadar White House ke fitarwa.

Donald Trump na Amurka
Shugaban Amurka, Donald Trump yana wani jawabi. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rahoton Yahoo News ya nuna cewa a ranar Jumma’a, Trump zai je asibitin sojoji na Walter Reed da ke Maryland, inda zai fara magana da dakarun soji kafin a yi masa gwajin.

Kara karanta wannan

Ana batun zargin kisan Kiristoci, yan bindiga sun yi ta'asa a masallacin Katsina

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masu lura da lamura sun fara tambaya me yasa ake kiran wannan gwajin “na shekara-shekara” alhali an riga an yi makamancin sa a Afrilun 2025.

Fadar White House ta ki bada bayanai

Gidajen jaridu kamar CNN da NBC News sun nemi karin haske daga White House kan dalilin sake gwajin, amma babu martani kai tsaye.

Trump, wanda shi ne shugaban Amurka mafi tsufa da aka taba zaba, ya ce yana cikin koshin lafiya kuma babu abin da ke damunsa.

A cikin wata tattaunawa, USA Today ta rahoto Trump ya ce:

“Zan yi gwajin lafiya na rabin shekara ne. Ina cikin koshin lafiya sosai, ban da wata matsala ta jiki ko kwakwalwa.”

Zargin da ake yi kan lafiyar Trump

Zuwa asibitin da ya yi ya biyo bayan rahotannin da suka bayyana cewa Trump yana da matsalar jijiyoyi bayan an lura da kumburin kafafunsa da raunuka a hannunsa a kwanakin baya.

Kara karanta wannan

Kano: 'Dan jarida ya debo ruwan dafa kansa, ICPC ta kama shi kan zambar N14m

Fadar White House ta bayyana cewa raunukan suna da alaƙa da maganin da yake sha don kula da lafiyar zuciya.

Shugaban Amurka, Donald Trump
Shugaba Trump na Amurka yana wani jawabi. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Sai dai wasu jama’a da kwararru na tambayar dalilin yin gwajin na biyu cikin wata shida, suna zargin cewa akwai wani abin da ake ɓoye wa jama’a.

Donald Trump ya kare zancen lafiyarsa

Tun a baya da aka masa tambayoyi, Trump ya kare kansa yana mai cewa lafiyarsa tafi ta tsofaffin shugabanni kamar Joe Biden da Barack Obama.

Kalaman nasa sun jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta, inda wasu ke ganin yana ƙoƙarin kau da kai daga tambayoyin da suka shafi lafiyarsa.

Trump ya rasa kambun zaman lafiya

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban Amurka, Donald Trump bai samu kambun zaman lafiya na duniya da ya so a ba shi a bana.

A 2025, an ba 'yar gwagwarmayar kare dimokuradiyya da yaki da mulkin danniya, Maria Corina Machado kambun.

Jami'an gwamnatin Trump, 'yan uwansa na jini da wasu kasashe sun nemi a ba shi kambun amma duk da haka bai samu ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng