An Kama 'Dan Najeriya da Ya Damfari Dubunnan Mata da Sunan Soyayya a Argentina

An Kama 'Dan Najeriya da Ya Damfari Dubunnan Mata da Sunan Soyayya a Argentina

  • Wani 'dan Najeriya Ikechukwu N. ya shiga hannu a Argentina bisa zargin damfara ta yanar gizo da ya shafi dubunnan mata da aka kwace kadarorinsu
  • An cafke shi ne karkashin aikin hadin gwiwa da aka lakaba suna "Operation Jackal", wanda INTERPOL ke jagoranta domin dakile damfara
  • Wannan shi ne karo na farko da kasar Argentina ta kama wanda aka sanya a cikin jerin wadanda ake nema ruwa a jallo a duniya baki daya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Argentina –Hukumomin kasar Argentina sun kama wani ɗan Najeriya mai suna Ikechukwu N., wanda hukumar INTERPOL ta ke nema ruwa a jallo.

Ana neman Ikechukwu kan zargin jagorantar wata babbar ƙungiyar masu aikata laifuffukan yanar gizo da kuma shirya damfara ta soyayya da ta yaudari dubunnan mata a duniya.

Kara karanta wannan

Kano: 'Dan jarida ya debo ruwan dafa kansa, ICPC ta kama shi kan zambar N14m

INTERPOL ta kama dan Najeriya
Hotunan jami'an INTERPOL da 'dan Najeriya da su ka kama a Argentina Hoto:@INTERPOL_HQ
Source: Twitter

INTERPOL ta sanar da wannan kame ne a shafinta na X a ranar Talata, inda ta ce an kama Ikechukwu a karkashin wani gagarumin shiri da aka lakaba wa suna Operation Jackal.

Hukumar ta bayyana cewa a karkashin wannnan shiri, an dauko aikin dakile ayyukan ƙungiyoyin masu laifuka daga yammacin Afrika.

Yadda aka kama 'dan Najeriya a Argentina

A cewar INTERPOL, wannan shi ne karo na farko da kasar Argentina ta kama wanda aka sanya a cikin mutanen da ake nema ruwa a jallo saboda girman laifuffukansu.

An bayyana Ikechukwu a matsayin wanda ya kafa kuma ke jagorantar ƙungiyar masu laifi na duniya, wadanda ke amfani da yanar gizo wajen yaudarar mata.

Ana yaudararsu da kalaman soyayya har su fada tarko a karbi makudan kudi daga hannunsu, a wani salo na damfarar matan da ke bukatar su ji shaukin soyayya.

Kamun nasa ya samu ne da haɗin guiwar ’yan sandan tarayya na Argentina (PFA), da Jami’an tsaron filin jirgi, da kuma taimako daga INTERPOL Brazil, IFCACC da FIS.

Kara karanta wannan

Kano ta dauki sabon kambu, ta zama ta 2 a tara kudin shiga a jihohin Najeriya

Yadda INTERPOL ke aikinta a duniya

INTERPOL ta bayyana cewa wannan shiri, wanda aka fara a watan Janairu na 2025, yana taimakawa kasashe wajen gano da dawo da kadarorin da ke da nasaba da laifuffuka.

Ana zargin ɗan Najeriya da damfara mata da dama a duniya
Hoton wasu daga cikin jami'an INTERPOL Hoto: @INTERPOL_HQ
Source: Twitter

Hukumar ta bayyana wannan kamun a matsayin wata babbar nasara da alama ce ta yadda haɗin guiwar ƙasashe ke kawo ci gaba a yaki da laifuffukan yanar gizo.

Ta kuma bayyana takaici a kan yadda ake samun karuwar aikata irin wadannan laifuffuka da ke da alaka da intanet a sassa daban-daban na duniya.

'Dan Nijar na yaudarar matan Najeriya

A baya, mun wallafa cewa matashi mai suna Yusuf Sidi, ɗan asalin Nijar, ya zama barazana ga mata da dama, yana amfani da soyayya da ƙarya wajen samun hotunan tsiraicin mata.

Rahotanni sun tabbatar da cewa wasu mata a Kano sun fada tarkon Yusuf, wanda babu kunya ya ce zai saki hotuna da bidiyon tsiraicinsu, ko kuma su fanshi kayansu a kudi masu nauyi.

Kara karanta wannan

Mai Wushirya: Bayan tsawon lokaci yana bidiyon fitsara da wadarsa, kotu ta dauki mataki

Ko da aka tuntubi Yusuf Sidi, ya ce shi 'dan kasuwa ne, kuma ba zai goge hotuna da bidiyon matan da ke hannunsa ba, har sai ta ba shi kudi ko a baza a intanet.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng