Rasha Ta Kai Sabon Hari Gabashin Turai, Ta Harba Makamai Masu Linzami a Ukraine
- Ukraine ta tabbatar da mutuwar mutane uku da raunata wasu 10 a harin makamai masu linzami da Rasha ta kai birnin Kyiv
- An ce yara uku sun jikkata a yankin Zaporizhzhia yayin luguden bam na daruruwan makaman Rasha ya ci gaba da sauka
- Poland ta rufe wani sashi na sararin samaniyarta tare da tura jiragen yaki saboda ba kasar kariya daga hare-haren Rasha
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Ukraine - Birnin Kyiv da kewaye sun fuskanci luguden bam mai tsanani daga jiragen yaki marasa matuka da makamai masu linzami na Rasha a daren Lahadi.
Hukumomin gwamnati sun tabbatar da cewa akalla mutane uku sun mutu yayin da wasu kusan 10 suka jikkata a wannan mummunan hari.

Source: Getty Images
Rasha ta kai mummunan hari Ukraine
Kafar labaran Reuters ta rahoto cewa daya daga cikin waɗanda suka mutu yarinya ce mai shekara 12, duk da cewa ba a tabbatar da wannan ba har yanzu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ministan harkokin wajen Ukraine, Andrii Sybiha, ya bayyana cewa harin na Rasha ya kasance “babban luguden bam” na daruruwan makamai.
Ya jaddada bukatar ƙasashen duniya su saka karin takunkumi kan Moscow domin tilasta wa shugaba Vladimir Putin ya daina wannan yaƙin.
A shafinsa na X, Sybiha ya wallafa cewa:
“Ya zama wajibi Putin ya ji radadin ci gaba da wannan yaƙin – a jikinsa, a aljihunsa, a tattalin arzikin ƙasarsa, da kuma mulkinsa. Wannan shi ne kawai zai iya sa shi ya dakatar da wannan yaƙin marar ma’ana."
Asibitoci da gidaje sun shiga halin ha’ula’i
A Zaporizhzhia da ke kudancin Ukraine, rahotanni sun tabbatar da cewa harin ya raunata akalla mutane 16 ciki har da yara uku.
Wani bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta ya nuna gine-gine da dama na ƙonewa bayan luguden wutar, inji rahoton TVC News.
A Kyiv, magajin gari Vitali Klitschko ya ce asibitin zuciya na gwamnati ya kama da wuta sakamakon harin.

Kara karanta wannan
An shiga jimami bayan ramin hakar ma'adanai ya rufta da sama da mutane 100 a Zamfara
Shaidu sun ce jiragen yaki marasa matuka ne suka kai hari cikin birnin da tsakar dare, inda aka rika jiyo karar harbin manyan bindigogi da fashewar bam.
Da dama daga cikin mazauna garin sun tsere zuwa tashoshin jirgin ƙasa na karkashin ƙasa domin neman mafaka, inda suka kwana a kan gadaje na wucin gadi.

Source: Facebook
Kasashen makwabtan Ukraine sun dauki mataki
Harin ya sa ƙasar Poland ta rufe sararin samaniyarta a yankunan kudu maso gabas, inda ta kuma tura jiragen yaki a matsayin kariya.
Wannan mataki ya nuna irin barazanar da yaƙin Ukraine ke haifarwa ga ƙasashen makwabta, inji rahoton ABC News.
Hukumomin Ukraine sun ce harin ya ci gaba har zuwa safiyar Lahadi, inda suke kokarin fatattakar jerin jirage marasa matuka da ake turawa daga Rasha.
Rasha ta kashe mutane 15 a Ukraine
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Rasha ta kai mummunan hari da makamai masu linzami kan Kyiv, inda ta kashe mutane 15 tare da raunata 156.
Shugaban kasa Volodymyr Zelenskyy ya ce harin ya ruguje wani gini mai hawa tara, wani tsohon gini na zamanin da a yammacin birnin Kyiv.
Yayin da ake fargabar adadin waɗanda suka mutu zai ƙaru, Zelenskyy ya buƙaci kasashen duniya da su tsoma baki a lamarin.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

