Sheikh Saleh: An Zabi Sabon Babban Mai Fatawa kuma Shugaban Malaman Saudiyya

Sheikh Saleh: An Zabi Sabon Babban Mai Fatawa kuma Shugaban Malaman Saudiyya

  • Sheikh Saleh bin Humaid ya zama sabon babban mai ba da fatawa na Saudiyya kuma zai jagoranci majalisar manyan malamai
  • Nadin Sheikh Humaid ya zo ne bayan rasuwar Sheikh Abdulaziz al-Sheikh, wanda ya rike mukamin daga 1999 zuwa rasuwarsa a 2025
  • An ce Sabon babban mai ba da fatawar, Sheikh Humaid ya taba zama limamin masallacin Harami da shugaban majalisar Shura

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Riyadh – Rahotannin da muka samu na nuni da cewa Sheikh Dr Saleh bin Humaid ya zama sabon babban mai ba da fatawa na Saudiyya.

Mai kula da masallatan nan biyu, watau Sarki Salman bin Abdulaziz ne ya nada shi tare da bashi mukamin shugaban majalisar malaman kasar.

An samu rahoto cewa Saudiyya ta nada sabon babban mai fatawa bayan mutuwar Al-Sheikh.
Hoton Sheikh Dr Saleh bin Humaid, wanda aka ce Saudiyya ta nada sabon babban mai fatawa. Hoto: @insharifain
Source: Twitter

Sabon nadin Mufti bayan mutuwar Al-Sheikh

Sakon da kafar labaran Inside the Haramain ta fitar a safiyar Laraba, ya nuna cewa fadar sarkin Saudiyya za ta sanar da nadin a hukumance nan ba da jimawa ba.

Kara karanta wannan

Al Sheikh: Limamin Arafa kuma shugaban malaman Saudiyya ya rasu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nadin sabon babban mai ba da fatawa ya biyo bayan rasuwar mai rike da mukamin, Sheikh Abdulaziz bin Abdullah al-Sheikh, a ranar Talata yana da shekaru 80.

Al-Sheikh ne ya rike wannan babban matsayi na jagoran addini mafi girma a Saudiyya tun daga 1999 har zuwa rasuwarsa a 2025.

Rasuwarsa ta kawo karshen wani babi na tarihi a fagen jagorancin malamai a Saudiyya, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.

Shugabanni daga kasashe daban-daban sun aiko da sakonnin ta’aziyya, ciki har da Sarki Salman da Yarima Mohammed bin Salman.

Wanene Sheikh Humaid, sabon shugaban malamai?

Sheikh Dr Saleh bin Humaid, ya kasance malami da ake matukar girmamawa a Saudiyya da kasashen waje, kamar yadda aka wallafa a shafin WikiPedia.

Ya taba zama daya daga cikin manyan limamai tara na Masallacin Harami a Makka, inda yake jagorantar sallar tarawihi da Juma’a.

Haka kuma, ya taba zama shugaban majalisar Shura ta Saudiyya, abin da ya kara masa kima a fannin siyasa da shugabanci.

Kara karanta wannan

Zaman sulhu: Sheikh Gumi ya gargadi jami'an tsaro kan 'yan ta'adda

Sabon mukaminsa na babban mai ba da fatawa ya tabbatar da matsayin sa a matsayin jagora ga al’ummar Musulmi.

Muhimmancin mukamin babban Mai ba fatawa

Mukamin babban mai ba da fatawa shi ne matsayin jagoran addini mafi girma a Saudiyya, kuma yana da tasiri a fagen shari’a da zamantakewa.

Hakan ya hada da bayar da fatawowi kan manyan batutuwa da suka shafi rayuwar Musulmi da tsarin kotunan kasar.

An samar da wannan mukami a shekarar 1953 lokacin da Sarki Abdul Aziz ya nada Muhammad ibn Ibrahim Al ash-Sheikh a matsayin babban mai ba da fatawa na farko.

Sheikh bin Humaid yanzu zai ci gaba da rike wannan tarihi tare da fuskantar manyan kalubale na zamani.

Jerin wadanda suka rike mukamin

  • Muhammad ibn Ibrahim Al ash-Sheikh (1953–1969)
  • Mukamin ya tsaya daga 1969–1993
  • Abdul Aziz bin Abdullah bin Baz (1993–1999)
  • Abdul-Aziz ibn Abdullah Al ash-Sheikh (1999–2025)
  • Saleh bin Humaid (2025–yanzu)

Saudiyya: 'Dan sarki ya rasu baya dogon suma

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Yarima Al-Waleed bin Khaled ya rasu bayan shekaru 20 cikin dogon suma da ya faru bayan hatsarin mota a London.

Kara karanta wannan

Abba Gida-Gida zai rage bashin Ganduje, za a biya karin N5bn ga 'yan fansho a Kano

Mahaifinsa, Prince Khaled bin Talal bin Abdulaziz Al Saud, ya tabbatar da labarin rasuwar cikin alhini da yarda da ƙaddarar Allah.

Rahoto ya nuna cewa Yarima Al-Waleed bin Khaled bin Talal yana cikin dangin sarakunan Saudiyya, amma ba ɗa ko ɗan'uwan Sarki Salman ba ne kai tsaye.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com