Rashawa: Amurka za Ta Rika Daukar Mataki Mai Tsauri kan Manyan Najeriya
- Amurka ta ce ba za ta lamunci cin hanci da rashawa ba, kuma za ta hana masu hannu a laifin samun bizar shiga kasar ta
- Rahotanni sun nuna cewa gargadin ya shafi manyan mutane ko shugabanni da ake zargi da almundahana a Najeriya
- Wannan sanarwa ta zo ne yayin da gwamnatin shugaba Bola Tinubu ke ikirarin ƙara ƙaimi wajen yaƙi da cin hanci da rashawa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya sake jaddada matsayarsa na tsaurara mataki kan duk wani ɗan Najeriya da ke da alaka da rashawa.
Wannan batu ya zo ne a daidai lokacin da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke cewa tana ƙara ƙaimi wajen yaƙi da rashawa da cin hanci a ƙasar.

Source: Facebook
Sanarwar ta fito ne daga shafin X na ofishin jakadancin Amurka a ranar Litinin, inda aka bayyana cewa yaƙi da rashawa ba shi da iyaka kuma babu wanda zai kubuta daga hukunci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gargadin Amurka ga manyan Najeriya
Ofishin jakadancin ya bayyana a fili cewa ba zai lamunci barin mutane marasa nagarta suna shiga kasarsa ba.
Ya ce:
“Yaƙi da rashawa ba shi da iyaka. Ko manyan mutane ne suka shiga ciki, za a iya hana su samun biza.”
Maganar Amurka kan magudin zabe
Punch ta wallafa cewa tun a watan Mayun 2023, Amurka ta sanar da ɗaukar matakan hana wasu mutane da suka lalata tsarin zaɓe a Najeriya samun biza.
Ministan Amurka ya ce ƙasarsa ta jajirce wajen kare dimokuraɗiyya a Najeriya da duniya baki ɗaya.
Amurka ta ce matakin da aka ɗauka kan masu tada zaune tsaye a zaɓen 2023 ya yi daidai da ƙudirinsu na kare dimokuraɗiyya.
A cewar shi waɗanda suka kawo tasgaro wajen gudanar da zaɓen Najeriya ba za su kubuta daga hukunci ba, ciki har da hana su shiga Amurka.
Matsayar gwamnatin Tinubu kan rashawa
A gefe guda, Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ya ce gwamnatin Tinubu ta ƙuduri aniyar magance rashawa ta hanyar ƙarfafa tsare-tsaren hukumomi.
Ya bayyana hakan a Abuja yayin wani taro na tattaunawa kan tsarin yaƙi da rashawa da kuma haɗa kai da kwamishinonin yaɗa labarai na jihohi.

Source: Twitter
Rahoton VON ya nuna cewa Mohammed Idris ya ce gaskiya da riƙon amana su ne ginshiƙan dimokuraɗiyya, kuma gwamnati za ta ci gaba da aikin ta a kan wannan turba.
Ministan ya ƙara da cewa Shugaba Tinubu yana ɗaukar matakai na yin garambawul a fannin shari’a domin kawo ƙarshen jinkiri a gurfanar da masu aikata rashawa.
Amurka ta cafke dan Najeriya kan sata
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Amurka ta sanar da kama wani dan Najeriya da ake zargi da satar makudan kudi.
Amurka ta bayyana cewa an kama matashin ne bayan ya yi kutse a wata jami'a ya wawure kudi masu tarin yawa.
Bayanai da hukumomin shari'a na kasar suka fitar sun nuna cewa ba a samu kudin a hannunsa ba, kuma hakan zai kara girmama lamarin.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


