Bayan Barazanar Isra'ila, Saudi Ta Kulla Yarjejeniyar Tsaro da Pakistan Mai Nukiliya

Bayan Barazanar Isra'ila, Saudi Ta Kulla Yarjejeniyar Tsaro da Pakistan Mai Nukiliya

  • Saudiyya da Pakistan sun amince da yarjejeniyar tsaron juna domin ƙarfafa haɗin gwiwa a fannin tsaro
  • Yarjejeniyar na zuwa a lokacin da kasashen Gabas ta Tsakiya ke nuna damuwa kan dogaro da Amurka kan tsaro
  • A cewar Saudiyya, duk wani hari da aka kai ga ɗaya daga cikin ƙasashen biyu, za a ɗauke shi tamkar hari ga juna

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Saudi Arabia – Kasar Saudiyya da Pakistan da ke da makaman nukiliya, sun sanya hannu kan wata sabuwar yarjejeniyar tsaron juna.

Rahotanni sun nuna cewa na yi yarjejeniyar ne a ranar Laraba, kuma tana nuna alamar ƙarfafa dangantakar tsaro da suka gada tsawon shekaru da dama.

Shugabannin Saudiyya da Pakistan yayin kulla yarjejeniyar tsaro.
Shugabannin Saudiyya da Pakistan yayin kulla yarjejeniyar tsaro. Hoto: @PakPMO
Source: Twitter

Gwamnatin Pakistan ta wallafa a X cewa duk kasar da aka kai wa hari a cikinsu, dukkansu za su dauki abin kamar su aka taba.

Kara karanta wannan

Atiku ya yi nazari, ya gano abin da yake tunanin ya hana kawar da 'yan bindiga a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An sanar da cewa yarjejeniyar za ta ƙara tabbatar da haɗin gwiwa a fannin tsaro, musamman bayan hare-haren da aka kai wa ƙasar Qatar daga Iran da Isra’ila a cikin shekara guda.

Dalilin yarjejeniyar Saudi da Pakistan

Rahoton Reuters ya nuna cewa wani babban jami’in Saudiyya ya bayyana cewa ba saboda wata bukatar gaggawa aka yi yarjejeniya ba.

Jami'in Saudiyyan ya ce hakan wani mataki ne na dindindin domin ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro da ta daɗe tana gudana tsakanin ƙasashen biyu.

Ya ce matakin wata hanya ce ta tabbatar da tsaro a yankin da ke cike da rikici, musamman bayan hare haren Isra’ila kan shugabannin Hamas a Doha, lamarin da ya fusata ƙasash Larabawa.

Tasirin Gaza da rikicin yankin

Yarjejeniyar na zuwa ne a daidai lokacin da Isra'ila ke ci gaba da kai hari Gaza, wanda ya jawo mummunar damuwa a ƙasashen Gabas ta Tsakiya.

A shekarar 2025 da muke ciki, an kai hari kai tsaye ga Qatar sau biyu, daga Iran da kuma daga Isra’ila, lamarin da ya ƙara dagula al’amura.

Kara karanta wannan

Ana maganar sulhu, 'yan bindiga sun farmaki motar jami'an tsaron NSCDC

Haka kuma, wannan yarjejeniya ta Saudiyya da Pakistan na iya shafar lissafin dabarun tsaro a yankin.

Saudi na kara kulla alaka da Indiya

Bayan sanar da yarjejeniyar, ma’aikatar harkokin wajen Indiya ta bayyana cewa ta san da lamarin kuma za ta yi nazari kan tasirinsa ga tsaron ta da kuma zaman lafiyar yankin.

Jami’in Saudiyya ya jaddada cewa duk da dangantakar tsaro da Pakistan, ƙasarsa na ƙara bunƙasa hulɗa da Indiya, wacce ita ma ƙasa ce mai makaman nukiliya.

Abin da yarjejeniyar ta ƙunsa

A cewar bayanin da ofishin Firaministan Pakistan ya fitar, yarjejeniyar ta ƙunshi tsaro ta kowane mataki na soja.

Ya kara tabbatar da cewa duk wani hari da aka kai ga ɗaya daga cikin ƙasashen, za a ɗauke shi a matsayin hari ne kan duka biyun.

An nuna a talabijin na ƙasar Pakistan yadda Firaminista Shehbaz Sharif da Yarima mai jiran gado na Saudiyya, Mohammed bin Salman, suka sanya hannu tare da rungumar juna.

Shugabanni da ministocin Saudiyya da Pakistan bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar tsaro. Hoto: @GovtofPakistan
Shugabanni da ministocin Saudiyya da Pakistan bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar tsaro. Hoto: @GovtofPakistan
Source: Twitter

Shugaban sojojin Pakistan, Asim Munir, wanda ake ɗauka a matsayin mutum mafi ƙarfi a ƙasar, ya halarci bikin rattaba hannun.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe Sarkin da suka yi garkuwa da shi, sun jefar da gawarsa a daji

Isra'ila ta yi kisan kare dangi a Gaza

A wani rahoton, kun ji cewa binciken majalisar dinkin duniya ya nuna cewa Isra'ila ta yi kisan kare dangi a zirin Gaza.

Rahoton ya zo ne bayan bincike ya nuna cewa Isra'ila ta aikata laifuffuka har guda hudu da suke a matsayin kisan kare dangi.

Majalisar dinkin duniya ta bukaci dukkan kasashe da su tashi tsaye wajen ganin sun hana Isra'ila cigaba da kai hari kan Falasdinawa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng