Kotu Ta Garkame Mutum 2 kan Yunkurin Kashe Shugaban Kasa da Asiri a Zambia
- Kotu a Zambia ta daure mutum biyu na tsawon shekaru saboda yunkurin kashe Shugaba Hakainde Hichilema da sihiri
- An kama Leonard Phiri, dan kasar Zambia, da Jasten Mabulesse Candunde, dan kasar Mozambique a shekarar 2024
- Alkalin kotun, Fine Mayambu ya bayyana dalilan da ya sa kotu ta amince da tuhumar da ake masu, tare da kiransu makiya Zambia
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Kasar Zambia – Wata kotun Majistare da ke kasar Zambia ta kama wasu mutane biyu da laifin yunkurin kashe shugaban kasar Hakainde Hichilema
Kotun ta ce ta kama Leonard Phiri, dan kasar Zambia, da Jasten Mabulesse Candunde, dan kasar Mozambique, da yunkurin yi wa Hichilema sihiri.

Source: Facebook
BBC ta wallafa cewa a zaman kotun, an yanke masu hukuncin daurin shekara biyu a gidan yari bayan an tabbatar da cewa sun yi yunkurin kashe Shugaba Hichilema.
Zambia: An kama mutum 2 da sihiri
The Cable ta ruwaito cewa an kama mutanen ne a watan Disamba 2024 tare da kayan tsafi, ciki har da hawainiya mai rai da sauran kayan tsumbu.
Kotu ta same su da laifi bisa dokar hana sihiri da aka kafa tun zamanin mulkin mallaka a shekarar 1914, kuma da wannan aka dogara wajen yanke masu hukunci.
A yayin da ake yanke hukuncin, Alkalin kotun, Fine Mayambu, ya bayyana cewa:
"Wadanda aka yanke wa hukunci ba abokan gaba ne kawai ga shugaban kasa ba, amma abokan gaba ne ga daukacin ‘yan Zambia.”

Source: Facebook
Rahotanni sun ce wadanda aka kama da laifin sun yi ikirarin cewa su malamai ne na gargajiya ba masu sihiri ba.
Amma kotu ta ce an tabbatar sun gabatar da kansu a matsayin masu sihiri. Alkalin ya ce Phiri ya nuna yadda gaban kambu da aka huda zai iya haddasa mutuwa cikin kwana biyar.
An roki kotun kasar Zambia afuwa
Lauyan wadanda ake tuhuma, Agrippa Malando, ya roki kotu ta yi musu afuwa kasancewar ba su taba aikata laifi a baya ba.
Sannan ya kuma bukaci kotu ta ci su tara maimakon dauri, amma kotun ba ta amince da bukatarsa ta karshe ba kan wadanda ya wakilta.
Alkalin ya ce:
“Tambayar ba ita ce ko suna da sihiri ko a’a ba. Tambayar ita ce ko sun gabatar da kansu a matsayin masu sihiri, kuma shaidu sun tabbatar da hakan.”
Baya ga hukuncin daurin shekara biyu da aka yanke masu bisa ikirarin sihiri, an kuma yanke musu wata shida saboda mallakar kayan tsafi.
Sai dai kotu ta ce hukuncin zai gudana lokaci guda, wato zasu shafe shekara biyu kacal a gidan yari, daga ranar da aka kama su a watan Disamba 2024.
Shugaba Hichilema, wanda ya taba bayyana cewa bai yarda da sihiri ba, bai fitar da wata sanarwa a kan lamarin ba.
Tsohon Shugaban Zambia ya mutu
A baya, mun wallafa cewa tsohon shugaban ƙasar Zambia, Edgar Chagwa Lungu, ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru 68 bayan fama rashin lafiya na tsawon lokaci.
Jam’iyyarsa ta PF ce ta tabbatar da rasuwar tsohon Shugaban Kasar a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis, 5 ga Yuni, 2025, tare da addu'ar ya samu rahama.
Marigayi Lungu ya rasu ne a wani asibiti da ke Pretoria, ƙasar Afirka ta Kudu, inda yake samun kulawa ta musamman kafin ajalinsa ya yi halinsa, kamar yadda 'yarsa, Tasila Lungu-Mwansa, ta tabbatar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


