Yanzu-Yanzu: Shugaban Zambia na farko Kenneth Kaunda ya mutu

Yanzu-Yanzu: Shugaban Zambia na farko Kenneth Kaunda ya mutu

  • Shugaban kasar Zambia na farko, Kenneth David Kaunda ya rasu a ranar Alhamis 17 ga watan Yuni, a Lusaka, babban birnin jihar
  • Tsohon shugaban kasar ya rasu ne bayan an kwantar da shi a asibitin sojoji a ranar Litinin
  • Dansa Kambarange Kaunda ya tabbatar da rasuwar mahaifinsa yana mai cewa ya shaki numfashinsa na karshe a ranar Alhamis

Shugaban kasar Zambia na farko, Kenneth Kaunda, ya rasu yana da shekaru 97 a duniya a cewar kafafen watsa labarai na kasar Zambia, Mwebantu ta ruwaito.

Shugaban na farko ya mulki kasar tsawon shekaru 27 tun daga shekarar 1964 a lokacin da kasar ta samu yancin kai daga kasar Burtaniya kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Shugaban Zambia na farko Kenneth Kaunda
Shugaban Zambia na farko Kenneth Kaunda. Hoto: Rolls Press/Popperfoto
Asali: Getty Images

Dan tsohon shugaban kasar, Kambarange Kaunda ya tabbatar da rasuwar mahaifinsa yana mai cewa ya shaki numfashinsa na karshe a ranar Alhamis 17 ga watan Yunin 2021.

Shugaban Zambia Edgar Lungu ya bukaci al'ummar kasar su masa addu'a.

DUBA WANNAN: An kama matar da ta damfari ɗan siyasa N2.6m da sunan za a yi amfani da 'iskokai' a taimaka masa ya ci zaɓe

Kenneth ya rasu ne kwanaki kadan bayan rahotannin cewa an kwantar da shi a asibitin sojoji da ke babban birnin jihar ta Lusaka inda ake masa maganin cutar Pnuemonia.

A matsayinsa na shugaba na farko kuma cikin wadanda suka yi gwagwarmayar samun yancin kasar, Kenneth Kaunda ya jagoranci kasarsa a lokacin da kasar ke cikin mawuyancin hali.

KU KARANTA: Dakatar da Twitter ya hana wa gwamnonin PDP kafar yaɗa labaran ƙarya, Fadar Shugaban ƙasa

Marigayi Kaunda ya sauka daga mulki ne bayan ya sha kaye hannun Frederick Chiluba, shugaban Movement for Multiparty Democracy.

A shekarar 2000, ya yi murabus a matsayin shugaban jamiyyarsa ta United National Independence Party (UNIP).

Kaunda ya rasu ne a lokacin da annobar korona ke yaduwa a kasar da ke kudancin Afirka.

Ma'aikatar lafia na Zambia ta ce gadaje sun cika dari bisa dari a asibitocin kasar saboda masu fama da cutar ta korona.

A wani labarin, kun ji cewa an kashe wani jami'in dan sanda sannan an sace wasu yan kasar China su hudu da ke aiki a layin dogo na Legas zuwa Ibadan kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Wakilin majiyar Legit.ng ya ruwaito cewa yan bindigan sun labe ne a kan iyakar Adeaga/Alaagba wani gari da ke kan iyakar jihohin Oyo da Ogun a ranar Laraba.

Mazauna wasu unguwanni a Zaria sunyi Sallar Al-Ƙunuti kan 'yan bindiga Yan bindigan sanye da bakaken kaftani sun kutsa wurin da ake aikin layin dogon a kauyen Adeaga/Alaagba da ke karamar hukumar Odeda a jihar Ogun.

Asali: Legit.ng

Online view pixel