Zamu taimaka muku wajen magance matsalar tsaro: Kasar Zambia ga Najeriya
- Kasar Zambia ta bayyana niyyar taimakawa Najeriya wajen magance matsalar tsaro
- Jakadan Kasar ya bayyana cewa Zambia na da ilimi wajen kawar da matsalar tsaro
- Najeriya na fama da matsalar tsaro da ta addabi sassa daga Kudu zuwa Arewa
Abuja - Gwamnatin kasar Zambia a ranar Talata ta bayyana damuwarta kan matsalar tsaron da ta addabi Najeriya kuma ta yi alkawarin cewa zata taimakawa Najeriya wajen maganceta.
Kasar Zambia ta ce zata taimakawa Najeriya ne saboda ita ma ta taka rawar gani wajen samun yancin kasashen kudancin nahiyar Afrika daga turawan mulkin mallaka.
Jakadan Zambia dake Najeriya, Solomon Samuel Jere, ya bayyana hakan yayin sanar da taron zaman lafiyan da Cocin Seventh Day Adventist suka shirya yi ranar Asabar mai zuwa, rahoton Punch.
Yace Zambia shirya take da ta taya Najeriya da labaran leken asiri wanda zasu taimaka wajen samar da tsaro.
Yace:
"Zambia ba zata zuba ido 'yan uwanta dake Najeriya su cigaba da fama da ta'addanci ba. Ku san yanzu Zambia tayi sabon Shugaba wanda ya samar da sabbin hanyoyi."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Yanzu haka, akwai kasashe da dama irinsu India da wasu kasashen Afrika dake Zambia muna horar da jami'ansu wajen yaki da ta'addanci da yan bindiga."
"Saboda haka, Zambia zata taimakawa Najeriya wajen yaki da yan ta'adda."
Femi Adesina: FG na samun cigaba a fannin yakar rashin tsaro, jama'a ne ba su gani
Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya ce gwamnatin tarayya ta na cigaba da samun nasarori kan yaki da rashin tsaro a kasar nan.
Har a yanzu, ana cigaba da samun matsalolin garkuwa da mutane, 'yan fashin daji da kuma harin da 'yan bindiga ke kaiwa a fadin kasar nan.
A yayin jawabi a ranar Litinin yayin tattaunawa da gidan Talabijin na Channels, Adesina ya ce duk wanda ke duba kokarin gwamnatin nan ba zai hada shi da na gwamnatin da ta shude ba.
Asali: Legit.ng