Najeriya na Fuskantar Matsin Lamba daga Ƙetare, Ana So Natasha Ta Koma Majalisa

Najeriya na Fuskantar Matsin Lamba daga Ƙetare, Ana So Natasha Ta Koma Majalisa

  • Majalisa dattawan Najeriya ta fara samun matsin lamba daga kasashen ketare kan mayar da Natasha Akpoti-Uduaghan bakin aiki
  • Fatoumatta Njai, 'yar majalisar Gambiya ta rubuta wa Sanata Godswill Akpabio waisika, tana neman a dawo da Natasha majalisa
  • Njai, ta ankarar da majalisar Najeriya take dokar da take yi na hana 'yar majalisar komawa aiki bayan karewar wa'adin dakatarwarta

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja – Fatoumatta Njai, shugabar kwamitin walwalar yara da mata a majalisar dokokin Gambiya, ta yi magana kan rikicin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.

Ta bukaci majalisar dattawan Najeriya ta dawo da Sanata Natasha, mai wakiltar Kogi ta Tsakiya bakin aiki, bayan karewar wa'adin dakatarwar watanni shida.

An bukaci majalisar dattawan Najeriya ta mayar da Sanata Natasha bakin aiki bayan karewar wa'adin dakatarwarta.
Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan tana jawabi a wani taro da aka shirya a Abuja. Hoto: Natasha H Akpoti
Source: Facebook

An hana Natasha komawa majalisar dattawa

Akpoti-Uduaghan ta rubuta wasika ga sakataren majalisar tarayya a ranar 28 ga Agusta, 2025, inda ta sanar da shi niyyarta na dawowa bakin aiki, kamar yadda The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Sabon tarihi: An bayyana yadda Kwastam ke tattarawa gwamnati N20bn a kowace rana

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lauyanta, Victor Giwa, ya ce sanatar za ta koma tare da takwarorinta a ranar 23 ga Satumba, yana mai cewa:

“Komai ya kammala na komawarta aiki, tana shirin dawowa daga London domin ci gaba da wakiltar al'ummarta a majalisar. Wa’adin dakatarwar watanni shida ya kare."

Sai dai a ranar Talata, majalisar tarayya ta hana ta shiga harkokin majalisa, tana mai cewa har yanzu batun dakatarwar na gaban kotun daukaka kara.

Mun ruwaito cewa, majalisar ta ce dakatarwar da aka yi mata tun a ranar 6 ga Maris, 2025, za ta ci gaba da aiki har sai kotu ta yanke hukunci.

An bukaci a mayar da Natasha bakin aiki

A wasikar da ta rubuta ranar 9 ga Satumba, 2025, zuwa ga shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, Njai ta bayyana dakatarwar a matsayin abin da ya wuce gona da iri da kuma sabawa kundin tsarin mulki.

“Yau Natasha Akpoti-Uduaghan ce aka dakatar, gobe kuma wata ko wani dan majalisar ne za a dakatar. Ina ganin bayan cikar watanni shida na dakatarwar da aka yi ba bisa doka ba, to lokacin mayar da ita bakin aiki ya yi."

Kara karanta wannan

Najeriya ta yi gargadi bayan luguden wutan Isra'ila a Qatar da jiragen yaki

Ta yi nuni da hukuncin da Mai shari’a Binta Nyako ta yanke a ranar 4 ga Yuli, 2025, cewa dakatar da ɗan majalisa sama da watanni shida ya wuce gona da iri.

'Yar majalisar ta Gambiya ta zargi majalisar dattawan Najeriya da kin bin hukuncin kotu bayan hana Akpoti-Uduaghan dawowa a ranar 22 ga Yuli.

'Yar majalisar Gambiya, Fatoumatta Njai ta nemi majalisar NAjeriya ta mayar da Sanata Natasha bakin aiki.
'Yar majalisar Gambiya, Fatoumatta Njai, tana jawabi a zauren majalisa. Hoto: @ProfMgbeke
Source: Twitter

"Majalisar Najeriya ta saba doka" - Njai

Wasikar 'yar majalisar ta ce:

“Majalisar dattawa ta ƙara tsawaita wa'adin dakatarwar da aka yi ba bisa ka'ida ba, matakin da ya saba wa dokar mulkin dimokuradiyya."

Ta ce Sanata Akpoti-Uduaghan ta na wakiltar mutanenta, kuma tana wakiltar mata da matasa masu kishin gaskiya da adalci.

“A matsayinta na kasa mafi girma a cikin ECOWAS, ya zama wajibi Najeriya ta zama abin koyi a tsakanin kawayenta."

- Fatoumatta Njai.

An hana Sanata Natasha shiga majalisa

A wani labarin, mun ruwaito cewa, sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta fusata bayan da jami'an tsaro suka hana ta komawa bakin aiki a majalisar dattawa.

Ta nuna takaicinta kan yadda aka hana ta komawa kujerarta duk da cewa ta sanar da majalisar ranar da za ta dawo bakin aiki.

Kara karanta wannan

Da gaske an kwace sarautar da Sarki ya ba Shugaba Tinubu a Arewa? Gaskiya ta fito

Sanata Natasha, mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, ta yi zargin cewa majalisar ta koma wurin karya doka ƙarƙashin jagorancin Godswill Akpabio.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com