Tashin Farashin Mai a Duniya Ya Shafi Najeriya bayan Harin Isra'ila a Qatar
- Farashin danyen mai na Bonny da Najeriya ke hakowa ya tashi zuwa $67 a kasuwar duniya bayan Isra’ila ta kai hari Qatar
- Danyen mai na Brent ma ya tashi zuwa $66.58 amma har yanzu farashin bai kai $75 da Najeriya ke fata ba a kasafin 2025
- A jiya ne kasar Isra'ila ta kai hari Qatar a yayin da ake magana kan sulhu da kungiyar Hamas domin kawo karshen yaki a Gaza
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Farashin danyen mai samfurin Bonny na Najeriya ya karu da $2, inda ya tashi daga $65 zuwa $67 a kasuwar duniya.
Rahotanni sun nuna cewa farashin ya karu ne sakamakon harin da Isra’ila ta kai Qatar, ƙasa mai arzikin mai da gas.

Source: Getty Images
Reuters ta ce harin ya jawo tashin hankali a kasuwannin duniya, inda ‘yan kasuwa suka fara saye da sayarwa cikin hanzari saboda tsoron karuwar rashin tabbas a Gabas ta Tsakiya.
Sai dai duk da wannan karin, farashin bai kai $75 ba, wanda shi ne farashin da aka yi hasashe wajen tsara kasafin kuɗin Najeriya na shekarar 2025.
Farashin danyen man Najeriya ya tashi
Farashin gangar mai samfurin Brent da ake amfani da shi wajen kwatanta sauran nau’in man fetur, ya tashi zuwa $66.58, wanda ya karu da $1 kafin harin Isra’ila.
Rahoton Vanguard ya bayyana cewa hakan ya nuna yadda harin ya tada hankalin kasuwannin duniya a fannin danyen mai.
Masana sun bayyana cewa irin hare-haren kan kawo gagarumin sauyi a kasuwar man duniya, musamman idan ƙasar da abin ya shafa na daga cikin manyan masu samar da mai ko gas.
Tasirin kasashen OPEC kan farashin mai
A daidai lokacin da ake fargabar karin farashi, kungiyar OPEC+ ta sanar da sassauta takunkumin da ta sanya a kan samar da mai.
Wasu rahotanni sun bayyana cewa kungiyar ta ce za ta ƙara ganga 137,000 a kowace rana daga watan Oktoban 2025.
Wannan ya sa wasu masana suka yi hasashen cewa karin samar da mai na iya haifar da faduwar farashi zuwa kasa da $60 a kowace ganga.

Source: UGC
Shugaban kungiyar OGSPAN a Najeriya, Mazi Colman Obasi, ya ce:
“Sassauta takunkumin samar da mai a wannan lokaci na nufin karin fitar da shi zuwa kasuwa, wanda hakan zai iya janyo raguwar farashi zuwa kasa da $60 a kowace ganga.”
Illolin matakin ga kasafin Najeriya
Wani masani ya bayyana cewa wannan yanayi na iya kawo cikas ga aiwatar da kasafin kudin Najeriya na 2025, wanda aka gina bisa tsammanin farashin gangar mai a kan $75.
Ya ce, idan farashin ya ragu zuwa kasa da $60, akwai yiwuwar kudin shiga na kasa su ragu, lamarin da zai kara dagula matsalolin bashi da rashin kudin gudanar da manyan ayyuka.

Kara karanta wannan
Fetur: Yadda harajin Tinubu zai shafi ma'aikata, masu sana'a, 'yan kasuwa da sauransu
Za a kawo harajin mai a Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Najeriya ta yi karin haske kan harajin mai na 5% da ake shirin kawowa.
Shugaban kwamitin shugaban kasa kan harkokin haraji ya bayyana cewa ba a farkon shekarar 2026 za a fara karbar harajin ba.
Ya kuma tabbatar da cewa ba shugaba Bola Ahmed Tinubu ba ne ya kawo harajin domin yana kunshe a dokokin Najeriya tun a baya.
Asali: Legit.ng

