Matasa Sun Banka wa Majalisa Wuta, An Tilastawa Firayim Minista Yin Murabus a Nepal
- Dubunnan matasa da suke yin zanga-zangar yaki da rashawa sun tilasta wa Firayim Minista K.P. Sharma Oli yin murabus
- Rikici ya tsananta a Nepal bayan kashe masu zanga zanga 19 da jikkata sama da 100 sakamakon harbe-harben ‘yan sanda
- Hotuna da bidiyo da aka gani sun nuna yadda aka cinna wa majalisar dokokin kasar wuta, sannan aka farmaki gidajen ministoci
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Nepal - Firayim Ministan kasar Nepal, K.P. Sharma Oli, ya yi murabus daga mukaminsa a yau Talata, 9 ga watan Satumba, 2027.
Shugaban ya ajiye aikinsa ne bayan dubunnan matasa masu zanga-zangar yaki da rashawa sun mamaye tituna kasar tare da gwabzawa da 'yan sanda.

Source: Getty Images
Murabus din K.P Sharma ta zo ne kwana guda bayan 'yan sanda sun kashe mutane 19 tare da jikkata sama da 100, kamar yadda Aljazeera ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An cinnawa majalisar Nepal wuta
Zanga-zangar matasan ta samo asali ne daga haramcin amfani da kafafen sada zumunta da gwamnatin Oli ta sanya, lamarin da ya fusata jama’a.
An ce matakin ‘yan sanda na yin amfani da barkonon tsohuwa da harsasai na roba kan masu zanga zangar ne ya rura rikici a kasar, wanda ya sa gwamnati ta soke haramcin.
Duk da murabus din Firayin Ministan, an ce matasan ba su hakura ba, suka mamaye majalisar dokokin Nepal da ke Kathmandu, tare da cinna mata wuta.
Wasu daga cikin matasan da suka shiga majalisar sun yi ta murna suna daga hannu sama tare da rera wakokin nasara, inda daya daga cikinsu ya rubuta a bango da manyan baki, “MUN YI NASARA.”
An farmaki gidajen Firayim Minista da ministoci
Sai dai duk da kone-kone da lalata dukiyoyin da ake yi a birnin Kathmandu, ba a sake samun karuwar kisan mutane ba, domin jami’an tsaro sun ja da baya.
Rahoton BBC ya nuna cewa masu zanga-zanga sun banka wuta a cikin gidajen wasu ministocin kasar, yayin da aka rika kwashe ministocin a jiragen sama don tsira da rayukansu.
Hakazalika, an rahoto cewa an kona wasu sassa na gidan Firayim Minista Oli da wuraren gwamnati da ke Singha Durbar, ciki har da ofishin Firayim Minista da majalisar tarayyar.

Source: Getty Images
Firayim Ministan Nepal ya rubuta wasiƙar murabus
A cikin wasiƙar murabus da ya aika wa shugaban kasa Ramchandra Paudel, Firayim Minista Oli ya ce:
“Ganin irin mawuyacin halin da kasa ta shiga, na ga dacewar in yi murabus daga yau don a samu mafita ta fuskar siyasa da kundin tsarin mulki.”
Shugaba Oli, mai shekara 73, shi ne firayim minista na 14 a kasar tun bayan da aka soke tsarin sarauta a 2008. An rantsar da shi karo na hudu a watan Yulin bara.
Sai dai, ba a taba jin ya tanka kan zarge-zargen rashawar da ta sa ake zanga-zangar ba, ko a taron jam’iyyun siyasa da ya kira a safiyar Talata kafin ya yi murabus.
Jirgi ya yi hadari da mutane 72 a Nepal

Kara karanta wannan
Lamari ya kazanta: Masu zanga zanga sun kona matar tsohon Firayim minista a Nepal
A wani labarin, mun ruwaito cewa, fasinjoji sama da 10 sun rasa rayukansu bayan jirgin saman da suke ciki ya gamu da hatsari a kasar Nepal.
Hukumomin kasar sun bayyana cewa jami'an agajin gaggawa sun riga sun killace wurin da jirgin ya fada, a kokarin kashe wuta da ceto mutanen ciki.
Firayim Minista, K.P. Sharma Oli ya kira taron mukarraban gwamnatinsa kan wannan mummunan lamari da ya faru da jirgin saman.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

