Sabon Tarihi: Dubban 'Yan Auren Jinsi Sun Gudanar da Ziyarar Bauta a Vatican a Karon Farko
- An samu sauye-sauye da dama a bana game da maniyyata aikin ibada daga addinin Kirista a fadar Vatican a Rome
- An tabbatar da cewa an samu mabiya addinin Katolika 'yan auren jinsi 1,400 daga ƙasashe 20 sun gudanar da taron ziyara a Vatican
- Masu ziyara sun shiga cikin shirye-shiryen coci, inda suka yi addu’o’i, tattaki da kuma shiga ƙofa babban cocin Saint Peter’s
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Rome, Italy - A karon farko a tarihin Vatican, an samu sauyi kan masu halartar aikin hajji da aka saba gudanarwa.
An ce sama da yan Katolika masu goyon bayan auren jinsi 1,000 tare da abokansu suka gudanar da ziyara ta musamman a makon jiya.

Source: Getty Images
Yan auren jinsi sun gudanar da ziyara a Vatican
Fox News ta ce taron ya tara mutane 1,400 daga ƙasashe 20, wanda ya zama wani ɓangare na shekara tsarkakakkiya a wurinsu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majiyoyi sun tabbatar da cewa Kungiyar La Tenda di Gionata ta shirya hakan domin neman ba su dama kamar sauran yan Adam.
Duk da cewa an taba zuwa Vatican a baya, wannan shi ne karo na farko aka saka irin wannan ziyara a cikin shirin a hukumance.
Yveline Behets, mace mai shekaru 68 daga Brussels, ta yi tafiyar kilomita 130 tare da wasu masu ra'ayin auren jinsi don isa Roma ta hanyar tsohuwar hanyar Francigena.
Ta ce:
“Ina so ka da a rinka amfani da kalmar ‘maraba’ ba daidai ba. Mu ba baki ba ne kawai, mu iyali daya ne."

Source: Getty Images
Yan luwadi sun yi murna da ba su dama
Kamar yadda miliyoyin masu ziyara suka saba, waɗannan masu tattaki suma sun nufi cocin Saint Peter’s Basilica don shiga ta tsarkakakkiyar ƙofar a cikin Vatican.
Da safe, daruruwa sun halarci taron addu’a a cocin Gesu a tsakiyar Roma, sannan da dare suka gudanar da taron addu’a ta musamman, cewar rahoton CNN.

Kara karanta wannan
An kama wasu daga cikin ƴan bindigan da suka kashe Kiristoci a Kwara? Gaskiya ta fito
Hugo, dan shekara 35 daga Canada, ya ce wannan ziyara ta musamman “alamar suna da muhimmanci ne domin su ji an ƙara ɗaukar su a ciki.”
Sai dai ya bayyana cewa hanyar samun cikakkiyar karɓuwa akwai tsawo, domin coci har yanzu tana ganin auren jinsi ba daidai ba.
Abin da Fafaroma ya ce kan 'yan auren jinsi
Fafaroma Francis, wanda ya rasu a watan Afrilun 2025, ya yi ƙoƙarin buɗe coci ga kowa, duk da cewa bai canza koyarwa ba.
Shekarar 2023 ya amince limamai su rika sanya wa masu auren jinsi albarka, wanda ya jawo suka daga masu adawa musamman a nahiyar Afirka.
Magajinsa, Fafaroma Leo XIV, ya tabbatar da cewa aure tsakanin namiji da mace ne, amma ya ce ba zai rushe matakin Francis ba.
An hana Peter Obi shiga fadar Vatican
Kun ji cewa an hana Peter Obi shiga fadar Vatican, inda aka rantsar da sabon Fafaroma Leo XIV, bayan mutuwar Francis.
An ce jami’an tsaro sun dakatar da Obi a kofar fadar duk da roƙon Rabaran Francis Arinze, har sai da Bola Tinubu ya sa baki aka bar shi.
Tsohon minista, Femi Fani-Kayode ya ce ba a bar Obi ya gana da Fafaroma ba, sai dai ya gaishe da Shugaban kasa Bola Tinubu da ke wurin.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

