Burkina Faso Ta Tsaurara Doka, Gwamnatin Soja Ta Dauki Mataki a kan Auren Jinsi
- Majalisar rikon ƙwarya ta Burkina Faso ta amince da dokar da ta haramta luwadi da auren jinsi tare da sanya hukuncin ga duk wanda ya karya ta
- Matakin da majalisar ta dauka ya warware matsayar kasar a baya, inda ta shiga jerin wasu kasashen Afrika da suka ba masu wannan akida mafaka
- Yayin da dokar ta gargadi baki a kasar Afrikar, yanzu ana jiran Shugaban Soji da ke mulki, Kyaftin Ibrahim Traoré ya sanya wa dokar hannu
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Kasar Burkina Faso – Majalisar rikon ƙwarya ta Burkina Faso ta zartar da wata sabuwar doka da ta haramta dangantakar soyayya a tsakanin jinsi iri ɗaya.
Matakin na zuwa ne shekara ɗaya bayan gwamnatin kasar ta gabatar da kudirin da ya ƙunshi haramcin a cikin sabon tsarin dokar iyali.

Kara karanta wannan
Tinubu ya amsa kira kan kirkirar 'yan sandan jihohi, ya gano sirrin magance ta'addanci

Source: Getty Images
BBC ta ruwaito cewa wannan matakin da aka kada kuri’a a kai ranar Litinin, zai iya kai mutum ɗaurin shekaru biyu zuwa biyar a gidan yari da kuma biyan tara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kasar Burkina Faso ta haramta auren jinsi
Aljazeera ta wallafa cewa, Ministan Shari’a, Edasso Rodrigue Bayala, ya bayyana cewa duk wadanda ba ‘yan ƙasa ba da aka kama da wannan laifi, za a maida su kasarsu.
Yanzu mataki na gaba shi ne shugaban mulkin soja na kasar, Kyaftin Ibrahim Traoré, ya sanya hannu kan wannan doka.
Traoré ya karɓi mulki a shekarar 2022 bayan hambarar da tsohon shugaban sojan rikon ƙwarya, Lt Col Paul-Henri Damiba.

Source: Twitter
Burkina Faso, ƙasar da ke yankin Sahel, na daga cikin ƙasashen Afrika 22 kacal daga cikin 54 da suka amince da dangantakar jinsi iri ɗaya a baya.
A wasu ƙasashen nahiyar, wannan laifi na iya kaiwa hukuncin kisa ko ɗaurin na lokaci mai tsawo a gidan yari.

Kara karanta wannan
Likitoci sun shata wa gwamnatin Tinubu layi, za su dauki mataki a cikin kwanaki 10
Makwabtan Burkina Faso a kan auren jinsi
A bara, Mali – wanda ke kusa da Burkina Faso kuma ƙarƙashin mulkin sojoji – ta amince da dokar da ta haramta luwadi da auren jinsi.
Wannan doka ta Burkina Faso na zuwa a lokacin da wasu ƙasashen Afrika suka tsaurara dokokinsu kan LGBT, abin da ya jawo suka suka daga ƙasashen waje.
Bankin Duniya, misali, ya dakatar da bayar da rance ga Uganda saboda dokokinta masu tsanani kan LGBT.
Najeriya ma tana daga cikin ƙasashen da suka kafa dokar hana luwadi, kuma Ghana ta amince da doka makamanciyar wannan a bara, amma Shugaban Kasar bai sa hannu ba.
Daga cikin waɗannan ƙasashen, Uganda ce ta fi tsauri, inda ta kafa hukuncin kisa tare da ɗaurin rai-da-rai ga wanda aka kama da dangantaka tsakanin jinsi iri ɗaya.
Tinubu ya kawo doka kan masu auren jinsi
A baya, mun wallafa cewa Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya sanya hannu kan wani muhimmin gyara ga dokar sojojin kasar nan.
Dokar ta haramta auren jinsi, aikata luwadi da madigo, da kuma zane-zane (tattoo), shaye-shaye, da sauran abubuwan da za su kawo kunya a bainar jama’a.
Sashi na 26 na sabuwar dokar sojoji ya tabbatar da cewa sojoji ba za su iya yin auren jinsi ba, ciki har da yan luwadi ko madigo matuƙar suna aikin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
