Shugaban Kasar Amurka, Donald Trump Ya Mutu? An Ji Gaskiyar Halin da Yake Ciki

Shugaban Kasar Amurka, Donald Trump Ya Mutu? An Ji Gaskiyar Halin da Yake Ciki

  • A yayin bikin ranar 'yan kwadago, kafafen sada zumunta suka cika da labarin cewa shugaban Amurka, Donald Trump ya mutu
  • Jita-jitar a soshiyal midiya, ta nuna cewa ko dai Donald Trump ya mutu, ko kuma yana fama da rashin lafiya mai tsanani
  • Amma abin mamaki, sai aka ga shugaban Amurkan tsaye kyam a gaban mutane, inda ya bayyana gaskiyar halin da yake ciki

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Amurka - Shugaban Amurka, Donald Trump ya karyata jita-jitar da ta bazu a shafukan sada zumunta cewa ya mutu ko kuma yana fama da rashin lafiya mai tsanani.

Trump ya yi wannan furuci ne a taron manema labarai a ranar Talata, 2 ga Satumba, 2025, inda ya ce bai taba jin wannan jita-jitar kai tsaye ba.

Donald Trump ya warware rudanin da aka samu game da jita-jitar ya mutu
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump a wajen taron yakin neman zabensa. Hoto: @realDonaldTrump
Source: Twitter

Donald Trump ya yi tsokaci kan labarin mutuwarsa

Kara karanta wannan

Magana ta kare: Nyesom Wike ya bayyana matsayarsa kan karawa da Tinubu a 2027

Mujjallar Forbes, ta rahoto cewa, lokacin da wani dan jarida ya tambaye shi ko ya san cewa mutane da dama a shafukan sada zumunta sun ce ya mutu, sai ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“A’a ban gani ba? Wai da gaske ne? Ban gani ba ko kadan.”

Ya ce ya taba ganin rahotanni daban daban da ke nuna alamar tambaya kan lafiyarsa, amma bai taba cin karo da wannan rahoto na cewa ya mutu ba.

Trump ya kara da cewa:

“Wannan magana ce mai tsanani… Na san suna yawan tambayar, ‘Shin lafiyarsa kalau kuwa? Me ke damunsa?’ Amma ban taba jin ana cewa na mutu ba.”

Labaran karya ake yadawa kan mutuwar Trump

Trump ya dora alhakin jita-jitar a kan kafafen yada labarai, yana mai cewa “labaran karya” ne ake yadawa.

Sai dai bincike ya nuna cewa jita-jitar ta fito ne daga masu amfani da shafukan sada zumunta, ba daga manyan kafafen labarai ba, inji rahoton E News.

Hasashen ya karu ne bayan Trump ya yi 'yan kwanaki ba tare da ya bayyana a bainar jama’a ba, sannan an ga hotunan rauni a hannunsa.

Kara karanta wannan

2027: Wike ya kyale Jonathan, ya fadi mutum 1 da zai rusa PDP idan ya samu takara

Donald Trump ya ce ana yawan tambaya game da lafiyarsa, amma bai taba ji ana jita-jita kan mutuwarsa sai yanzu.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump a cikin dakin taro a Washington, D.C. Hoto: @realDonaldTrump/X
Source: Getty Images

Abin da ya faru a shafukan sada zumunta

A ranar Juma’a, 29 ga Agusta, kalmomin “Trump ya mutu” da “Ina Trump yake?” suka fara yaduwa a dandalin sada zumunta na X.

Hakan ya faru ne yayin da aka lura da tsaikon jadawalin shugaban kasa, lamarin da ya kara watsa wa jita-jitar fetur, ta ci gaba da ci kamar wutar daji.

Sai dai daga baya, Trump ya bayyana a bainar jama’a a ranar Asabar lokacin da ya ziyarci filin wasan golf dinsa da ke a Sterling, Virginia.

Mataimakin shugaban kasa JD Vance ya ce yana da cikakken tabbacin cewa Trump yana lafiya kuma zai kammala wa’adinsa ba tare da wata tangarda ba.

Trump zai fitar da Falasdinawa daga Gaza

A wani labarin, mun ruwaito cewa, a wani yunkuri na sake fasalin Gaza, shugaban Amurka, Donald Trump ya shirya fitar da Falasdinawa daga zirin.

Kara karanta wannan

An gudu ba a tsira ba': Sarki ya faɗi yadda mutane 13 suka mutu a kogi a tsarewa yan bindiga

Ana tunanin cewa Trump zai ba Falasdinawa kudi domin su bar yankin zirin Gaza, sannan a kafa sababbin garuruwa da cibiyoyin kasuwanci a yankin.

Sai dai akwai yiyuwar shirin ya gamu da suka daga kasashen makwabta na Larabawa, wadanda ke ganin bai dace a tilasta wa al’ummar Gaza barin gidajensu ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com