Wani bala'i da ya taso a kasar Amurka, da har yanzu an kasa shawo kanshi
Wani sabon bala'i da ya barke a jihar California ta kasa Amurka ya sanya mutane cikin tashin hankali da dimuwa, inda yayi sanadiyyar raba mutane masu dinbin yawa da muhallin su ba tare da sun so hakan ba
Wani sabon bala'i da ya barke a jihar California ta kasa Amurka ya sanya mutane cikin tashin hankali da dimuwa, inda yayi sanadiyyar raba mutane masu dinbin yawa da muhallin su ba tare da sun so hakan ba. Bala'in in dai ba komai bane illa gobarar daji da ta kama a wani daji dake jihar ta California makwanni da yawa da suka gabata.
Wutar tana cigaba da karuwa inda har ya zuwa yanzu an kasa shawo kanta. Hakan ya samo asali ne sakamakon zafi da kuma kadawar iska mai karfi da ake yi a yankin da abin ya shafa shine ya sanya wutar cigaba da ruruwa tana kara yaduwa a yankin.
Iska mai karfi da ke kadawa a yankin tana kawo babbar koma baya a aikin kashe wutar da ake yi. Hayakin wutar a halin yanzu har ya kai ga kasar Canada da birnin New York.
DUBA WANNAN: Likitoci zasu tafi yajin aiki a Abuja
Ma'aikata na cigaba da aikin kashe wutar ta bangarori guda 20 na yankin jihar ta California. Kimanin 'yan kwana - kwana dari shida ne ke kokarin ganin sun kawo karshen yaduwar wutar.
Ma'aikatan kwana - kwanan sun samu taimako daga wurin wasu fursunoni dake zaune a gidan yari, wadanda suka fito da karfin su wurin kashe wutar.
Ma'aikatan kwana - kwana daga kasar Switzerland da kuma kasar Australia sun je kasar ta Amurka domin taimakawa wurin kashe wutar.
Rahotanni sun bayyana cewar wutar ta raba mutane sama da dubu 21 daga gidajen su, bayan haka kuma gobarar tayi sanadiyyar kone wasu dubunnan kadada na gonaki a yankin da abin ya shafa.
A wani bangaren kuma wani mutumi dan kimanin shekara 51 ya shiga hannun hukumar tsaron kasar ta Amurka, inda aka gurfanar dashi a gaban kuliya, a bisa tuhumar sa da ake yi da kunno wuta a dajin Clevaland.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng