Biafra: An Daure Shugaban 'Yan a Ware da Ya Fara Hargitsa Najeriya a Kasar Finland
- Kotu a ƙasar Finland ta yanke wa ɗan Najeriya mai rajin Biyafara, Simon Ekpa, hukuncin ɗaurin shekara shida a gidan yari
- An same shi da laifin ƙoƙarin tayar da zaune tsaye da kuma tallafawa ƙungiyoyin da ake kira ga ta’addanci a yankunan Najeriya
- Rahotanni sun nuna cewa kotun ta ce hukuncin ba na ƙarshe ba ne, inda ake sa ran zai ɗaukaka ƙara zuwa kotu ta gaba
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Finland – Wata kotu a ƙasar Finland ta yanke wa ɗan Najeriya mai rajin kafa ƙasar Biyafara, Simon Ekpa, hukuncin ɗaurin shekara shida a gidan yari.
Kotun ta bayyana cewa Ekpa, wanda ya kasance mazaunin garin Lahti a Finland ya yi amfani da kafafen sada zumunta wajen haifar da rikice-rikice da tayar da hankali a Najeriya.

Source: Twitter
Jaridar YLE da ke kasar Finland ta wallafa cewa hukuncin da aka yanke masa ya biyo bayan shari’ar da ta ɗauki lokaci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An tuhume shi ne da laifuffuka masu girma da suka haɗa da shiga cikin ƙungiyar ta’addanci, zamba, da kuma yin amfani da hanyoyin karya doka wajen cimma manufofinsa.
Ekpa: Abubuwan da kotu ta tabbatar
Kotun ta ce an tabbatar da cewa tsakanin watan Agusta 2021 zuwa Nuwamba 2024, Simon Ekpa ya yi ƙoƙarin ƙarfafa rajin ɓallewar yankin Biyafara ta haramtacciyar hanya.
Ta ce ya yi amfani da tasirin mabiyansa a shafukan sada zumunta wajen tayar da hankalin jama’a da kuma karfafa masu ɗaukar makami a yankin.
Bisa hujjojin da aka gabatar, kotun ta gano cewa ƙungiyoyin da ya ingiza sun yi amfani da makamai, abubuwa masu fashewa da harsasai a Najeriya.
Biafra: Karin laifuffukan Simon Ekpa
Baya ga batun ta’addanci, kotun ta ce an kuma same shi da laifin zamba ta haraji da karya doka a ƙasar Finland.
Wannan ya ƙara sanya kotun yin nazari a kansa, wanda ya sa ta ga dacewar yanke masa hukuncin ɗaurin shekara shida a gidan yari.
Kotun ta bayyana cewa aikinsa yana da haɗari ga zaman lafiya a Najeriya da Finland, kasancewar yana amfani da matsayinsa a ƙasashen biyu wajen aiwatar da shirye-shiryensa.

Source: UGC
Ekpa zai iya ɗaukaka ƙara a Finland
Sai dai duk da wannan hukunci, BBC Hausa ta rahoto cewa Simon Ekpa zai iya daukaka kara idan bai gamsu da hukuncin da aka masa ba.
An gano haka ne saboda hukuncin da aka yanke masa ba shi ba ne na ƙarshe, wanda hakan ke nufin shari’ar na iya ci gaba da ɗaukar lokaci kafin ta kai ƙarshe.
Al’amuran da suka shafi Simon Ekpa sun daɗe suna jawo ce-ce-ku-ce a Najeriya, musamman a Kudancin ƙasar inda rajin kafa ƙasar Biyafara ya taɓa yin ƙarfi.
An daure Sarkin Najeriya a Amurka
A wani rahoton, kun ji cewa wata kotun Amurka ta daure wani Sarkin Najeriya daga jihar Osun saboda kama shi da laifi.
Rahotanni sun nuna cewa an fara magana kan wanda zai maye gurbinsa kasancewar wasu 'yan fadar sun ce ya bata musu suna.
Wasu daga cikin 'yan masarautar da Sarkin ke mulka sun yi kira ga gwamnatin jihar Osun da ta gaggauta tsige shi da nada magajinsa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


