Mexico: Rigima Ta Barke a Majalisar Dattawa, Sanata Ya Naushi Shugaba a Wuya
- Rigima ta kaure tsakanin sanatoci a Majalisar Dattawan Mexico yayin da aka zargi yan jam'iyyun adawa da cin amanar kasa
- Rahoto ya nuna cewa rikicin ya kai ga doke-doke tsakanin sanatocin jam'iyyun adawa da mai mulki
- Shugaban Majalisar Dattawan Mexico ya yi barazanar kai kara kotu kan dukan da sanatan jam'iyyar adawa ya yi masa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Mexico - Dambarwa ta barke a majalisar dattawan Mexico a zaman ranar Laraba yayin wata muhawara kan batun yaki da masu safarar miyagun kwayoyi.
Rikicin ya fara ne lokacin da aka zargi sanatocin tsagin adawa da neman a shigo da dakarun Amurka, su taimaka wajen yaki da kungiyoyin miyagun kwayoyi a Mexico.

Source: Getty Images
Shugaban jam'iyyar adawa ta PRI, Alejandro Moreno, ya nuna bacin ransa lokacin da zaman ya kusa ƙarewa, kamar yadda Reuters ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda rigima ta kaure a Majalisar Mexico
Sanata Moreno ya gaza hakuri, ya tashi ya nufi mimbarin majalisar ya yi wa shugaban majalisar dattawa, Gerardo Fernández Noroña na jam’iyya mai mulki korafin an ƙi ba shi damar magana.
A wani bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta, an ga Moreno yana ingiza Noroña, ya naushe shi a wuya sannan ya ture wani mutum ƙasa lokacin da ya shiga tsakani.
Matsalar ta taso ne bayan zargin da aka yi wa jam’iyyun adawa PRI da PAN cewa sun nemi a kira dakarun Amurka su shigo Mexico domin yaƙi da miyagu, zargin da jam’iyyun suka karyata.
Me ya jawo doke-doke a Majalisar Dattawan?
Bayan rikicin, shugaban Majalisar Dattawa ya ce zai kai ƙarar shugaban marasa rinjaye, Moreno bisa laifin raunata shi tare da neman a cire masa kariyar majalisa.
"Muhawara na iya zama mai tsauri, mai zafi, amma yau da aka fallasa ‘yan adawa a matsayin masu cin amanar ƙasa, sun ɓata rai saboda gaskiya ta bayyana.”
Sai dai Moreno ya mayar da martani, inda ya zargi Noroña da fara rikicin. Ya ce: “Shi ne ya fara kai mani hari; ya yi hakan ne saboda ya gaza toshe mana baki da hujjoji.”
Duka ‘yan majalisar biyu na fuskantar wasu matsaloli daban-daban. Moreno na iya fuskantar tsigewa daga mukami bisa zargin cin hanci lokacin da yake gwamnan jihar Campeche daga 2015 zuwa 2019.
Shi kuwa Noroña, an gano yana da gida mai tsada, a daidai lokacin da Shugabar Mexico, Claudia Sheinbaum ke kokarin ganin an yi rayuwa mai sauki, lamarin da ya sa ake sukarsa.

Source: Getty Images
Mexico ba ta neman taimakon Amurka
A gefe guda, Shugaban Amurka, Donald Trump ya umarci a yi amfani da dakarun soji wajen yaƙi da kungiyoyin miyagun ƙwayoyi na Latin Amurka da aka ayyana a matsayin kungiyoyin ta’addanci.
Sai dai gwamnatin Mexico ta jaddada cewa “ba za ta yarda da shigar dakarun Amurka cikin ƙasarta ba.”
Trump ya kori shugaban hukumar DIA a Amurka
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban Amurka ta sallami babban hafsan soja, Laftanar Janar Jeffrey Kruse, wanda ya jagoranci hukumar leken asirin tsaro ta ƙasa (DIA).
An ruwaito cewa babban sojan ya rasa aikinsa ne bayan rahoton da ya fitar kan harin da Amurka ta kai wa Iran ta saba da ikirarin Donald Trump.
Rahoton DIA ya nuna cewa hare-haren Amurka kan wuraren nukiliyar Iran a watan Yuni bai yi gagarumin barna ba, abin da ya saba da ikirarin shugaban kasa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


