Cin Amana: Magidanci Ya Kama Matarsa Tsirara da Wani Namiji a Gado, Ya Ɗauki Mataki

Cin Amana: Magidanci Ya Kama Matarsa Tsirara da Wani Namiji a Gado, Ya Ɗauki Mataki

  • Wani magidanci ɗan shekara 38 a duniya ya ga abin mamakin da bai taɓa tsammani ba lokacin da ya dawo gida ba tare da sanar da matarsa ba
  • Mutumin mai suna, Mpanga ya bayyana yadda ya samu matarsa da wani mutumi tsirara a gadon aurensu
  • Kotu ta ci tarar kwarton da aka kama maƙudan kuɗi sannan ta yi wa matar nasiha kan ta gujewa cin amana da neman maza

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Zambia - Dubun wata matar aure da ke zaune a unguwar Chipata a Lusaka, kasar Zambia, mai suna Prisca Zulu, mai shekaru 30, ta cika, an kama ta da wani namiji tsirara a dakin aurenta.

Mijinta, Mpanga, wanda ke aiki a matsayin ma'aikacin kamfanin sarrafa ƙarfe ya shafe makonni shida a garin Chongwe kafin ya dawo gida don ganin iyalinsa.

Kara karanta wannan

Musulmi sun fusata da dodanni suka farmaki limamin Musulunci, an roki gwamna

Aure ya samu matsala.
Miji ya kama matarsa da wani kwance tsirara a ɗakin aurensu Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Zambian Observer ta rahoto cewa magidancin ya yanke shawarar ba matarsa mamaki ta hanyar dawowa gida ba tare da sanar da ita ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Magidanci ya kama matarsa taɓa cin amana

Sai dai magidanci ɗan shekara 38 ya riski abin baƙin ciki da takaicin da bai taɓa taammani ba a lokacin da ya isa gida.

Mpanga ya bayyana cewa matarsa ta nuna halin rashin gaskiya da mamaki bayan ya ce da ita, “Masoyiya, na dawo gida.” Sai ta leƙo taga kawai ta rufe labule.

Mpanga ya ce ya shiga gidan ta ƙofar ɗakin girki, inda ya lura cewa matarsa na tafiya cikin damuwa da ruɗani.

Saboda yadda lamarin ya ba shi mamaki, ya nufi ɗakin kwana, inda ya iske ƙaramin wando na maza a kan gado da wasu kayan namiji warwatse a ƙasa.

Yadda Mpanga ya kama mutum tsirara

Ya ce da ya ɗauki wandon dubawa, sai matarsa ta yi ƙoƙarin kwace masa, suka fara kokawa, daga nan ne ya faɗa kan wasu tulin kaya a tsakiyar ɗaki.

Kara karanta wannan

Damfara: Rundunar ƴan sanda ta kama matashi da ke kwaikwayon muryar gwamnoni

A cewarsa magidancin, a cikin kayan ya ga wani mutumi tsirara ya ɓuya, daga nan ya gane dalilin da ya sa matarsa take masa noƙe-noke kwanan nan.

Tare da taimakon maƙwabta, aka kama kwarton mai suna, David Mbere zuwa ofishin 'yan sanda na Kabanana, kamar yadda Tribune ta ruwaito.

Me ya faru da ma'auratan da suka je kotu?

Bayan haka, Mpanga ya shigar da ƙara a kotun Mstero, yana neman diyya na K30,000 daga David saboda lalata da matarsa.

A gaban kotu, David ya amsa cewa sau biyu ne kawai ya kwana da Prisca, yayin da ita ma matar ta amince da laifinta, tare roƙon afuwa daga mijinta.

Alkalin kotun, Harriet Mulenga, ta yanke hukunci cewa David zai biya Mpanga K35,000 a matsayin diyya, sannan ta yi wa Prisca nasiha kan illar cin amana da lalata a cikin aure.

Matar aure ta yanke al'aurar mijinta

A wani labarin, kun ji cewa wata mata ta yanke al'aurar mijinta yana tsaka barci, ta dafa ta bayan ta kashe shi a ƙasar Brazil.

Matar wadda ba a bayyana sunanta ba ta yi kisan ne domin huce haushi bayan ta kama mijin nata yana kallon finafinan batsa a gidansu.

Binciken ‘yan sanda ya nuna cewa matar ta hallaka mijinta, sannan ta yanke gabansa da kuma wasu sassa na jikinsa, tuni aka kama ta domin gurfanar da ita a kotu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262