Jirgin Sojin Sama Ya Rufto kan Makaranta ana cikin Karatu, Mutane da Dama Sun Mutu
- Jirgin sojojin saman Bangladesh ya rikito kan makaranta yayin da ɗalibai ke tsakiyar karatu a Arewacin babban birnin kasar, Dhaka
- Rahotanni sun nuna cewa mutum 19 sun mutu, wasu sama da 160 sun samu raunuka sakamakon hatsarin na yau Litinin
- Gwamnatin ƙasar Bangladesh ta sha alwashin gudanar da bincike mai zurfi tare da tallafawa duka waɗanda lamarin ya shafa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Bangaladesh - Wani jirgin ɗaukar horo na rundunar sojin saman Bangladesh ya yi mummunan hatsari a babban birnin ƙasar watau Dhaka.
Rahotanni sun nuna cewa akalla mutane 19 aka tabbatar da sun mutu yayin da wasu sama da 160 suka samu raunuka sakamakon hatsarin jirgin sojojin da yau Litinin.

Source: Getty Images
Jaridar Sky News ta ruwaito cewa jirgin ya rikito ƙasa ne a harabar makarantar Milestone School and College da ke unguwar Uttara a Arewacin Dhaka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jirgin sojoji ya faɗa kan kwaleji a Dhaka
Rahoton ya nuna cewa ɗalibai na tsaka da rubuta jarabawar gwaji, wasu kuma na cikin azuzuwa ana darasi, ba zato jirgin ya faɗa kan makarantarsu.
Hatsarin jirgin, nau'in F-7 BGI mai aikin horo, ya haddasa gobara mai ƙarfi tare da tashin hayaƙi, wanda ya turnuƙe sararin sama.
Sojojin Bangladesh sun tabbatar da hatsarin cikin wata sanarwa, inda suka ce:
“Jirgin ɗaukar horo na rundunar sojin saman Bangladesh F-7 BGI ya faɗi a Uttara. Jirgin ya tashi da misalin ƙarfe 1:06 na rana agogon GMT.”
Jami'an agaji sun kai ɗauki makarantar
Jami’an agajin gaggawa sun garzaya wurin da lamarin ya faru, inda hayaniya ta tashi yayin da ɗalibai, malamai, da mazauna unguwar ke tserewa domin tsira da rayukansu.
Ma’aikatan ceto sun yi ƙoƙarin kai agaji ga waɗanda suka samu rauni da kuma kashe gobarar, kamar yadda BBC News ta kawo.
Wani likita daga Cibiyar Kula da Ƙuna da Likitancin Fata ta ƙasa ya bayyana cewa sama da mutum 50 ciki har da yara na kwance ana kula da raunukan ƙonewar da suka samu a hatsarin.

Source: Twitter
Wane matakin Gwamnatin Bangladesh ta ɗauka?
Da yake mayar da martani game da hatsarin, shugaban gwamnatin rikon ƙwarya ta ƙasar, Muhammad Yunus, ya tabbatar wa da al’umma cewa za a gudanar da bincike mai zurfi tare da tallafa wa waɗanda abin ya shafa.
“Za a ɗauki duk matakan da suka dace domin gano musabbabin hatsarin da kuma samar da duk wani taimako ga waɗanda lamarin ya shafa,” in ji Yunus.
Hukumomi sun rufe yankin gaba ɗaya, kuma ana sa ran masu binciken soji za su fara bincike kai tsaye.
Wannan na daga cikin mafi munin hatsarin jiragen soji da ya faru a lokacin zaman lafiya a tarihin ƙasar Bangladesh a ’yan shekarun nan.
An gano dalilin hatsarin jirgin Air India
A wani rahoton, kun ji cewa hukumomin Indiya sun fitar da rahoton binciken farko kan hatsarin jirgin Air India da ya faru a watan Yunin da ya gabata.

Kara karanta wannan
"An karya doka," Abin da Atiku ya yi ana jimamin rasuwar Buhari ya harzuƙa Ministan Tinubu
An gano cewa danna madannin katse tafiyar mai zuwa injunan jirgin ne ya haddasa haɗarin jirgin saman, wanɗa ya halaka sama da mutum 250.
Masu bincike sun sami damar ciro bayanai daga akwatunan rikodin na jirgin, wanda ya ƙunshi bayanai da sautunan murya.
Asali: Legit.ng

