UN: Ƴar Najeriya Ta Yi Zarra, Ta Zama Ƴar Kwamitin Nukiliya na Duniya
- Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres, ya zabi Farfesa Rabia Sa’id daga Jami’ar Bayero Kano a cikin kwamitin masana
- Sabon kwamitin da ya kunshi kwararru akalla 21 za su binciki illolin yaki da makaman nukiliya ga lafiyar duniya ta fuskoki daban-daban
- Ana kallon nadin Farfesa Rabi'a a matsayin wata babbar nasara ga Najeriya, musamman wajen wakilcin mata a fannin kimiyya
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Kasar US – Majalisar Dinkin Duniya ta nada Farfesa Rabia Sa’id a matsayin daya daga cikin 'yan sabon kwamitin kimiyya mai zaman kansa kan illolin yaki da makaman nukiliya a duniya.
Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres ne ya bayyana nada Farfesa Rabia Sa’id, fitacciyar masaniyar kimiyyar lissafi daga Najeriya, a cikin sabon kwamitin.

Source: Facebook
Voice of Nigeria ta wallafa cewa wannan nadin ya sanya Najeriya a sahun gaba cikin wata muhimmiyar manufa ta duniya da ke da nasaba da zaman lafiya, lafiyar jama'a da tsaron duniya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
UN ta sanya ‘yar Najeriya a kwamitinta
Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa an kafa kwamitin mai zaman kansa, wanda ya kunshi masana 21 da suka shahara bayan amincewar kudurin Majalisar Dinkin Duniya.
Kwamitin zai gudanar da bincike na musamman domin kimanta illoli a jiki da zamantakewa da yaki da makaman nukiliya zai iya haddasawa a doron kasa.
Aikin kwamitin zai gudana a matakai daban-daban — na cikin gida, na ƙasa da ƙasa, da kuma na duniya, yana mai duba sauye-sauyen yanayi, gurbatar muhalli da tasirinsa a kan tattalin arziki.

Source: Facebook
Kwamitin zai gabatar da cikakken rahoton bincikensa ga Zaman Majalisar Dinkin Duniya na 82 a shekarar 2027, sakamakon zai taimaka wa ƙasashen duniya wajen fahimtar hatsarin da ke tattare da amfani da nukiliya.
Najeriya ta ƙara samun daraja a idon duniya
Daya daga cikin 'yan kwamitin ita ce Farfesa Rabia Sa’id, ƙwararriyar masaniya a fannin kimiyyar yanayi da sararin samaniya daga Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK).
Farfesa Rabia, wacce da ita aka kafa kungiyar Association of Women Physicists of Nigeria, za ta kara fito da Afrika da Najeriya a cikin wannan muhimmin bincike da za a gudanar.
An bayyana cewa ƙwarewarta a fannin kimiyyar yanayi zai taka rawa mai matuƙar muhimmanci wajen nazarin canje-canjen da za su biyo bayan yaki da makaman nukiliya, musamman ga yanayi da muhalli.
Farfesa Rabia Sa’id na cikin manyan masana daga ƙasashe 21, da suka haɗa da waɗanda suka kware a fannoni kamar kimiyyar nukiliya, lafiyar jama’a, ilimin muhalli, noma da tattalin arziki.
An gano kasashe masu makamin nukiliya
A wani labarin, mun wallafa cewa rahotanni sun bayyana cewa cewa Amurka da Rasha na da kimanin 87% na dukkannin makaman nukiliya da ake da su a duniya.
Har ila yau, ƙasashen biyu ne ke da 83% na makaman yaki da aka ajiye a cikin rundunonin sojojinsu, waɗanda ke a shirye don amfani idan bukatar hakan ta taso.
An kiyasta akwai makaman nukiliya 12,241 a duniya, daga cikin wannan adadi, makamai 9,614 na cikin ma'ajiyar rundunonin sojoji, kuma suna iya harba su nan take.
Asali: Legit.ng


