"Wa Ya Kashe Man Inji?": An Gano abin da Ya Jawo Jirgin Air India Ya Yi Hatsari
- Masu bincike da suka tattara bayanan jirgin saman Air India da ya yi hatsari sun bayyana sakamakon binciken su na farko
- Ofishin Binciken Hatsarin Jiragen Sama na Indiya (AAIB) ya fitar, an gano cewa an katse man fetur da ke zuwa injinan jirgin
- An kuma gano cewa matuƙan jirgin biyu, Kyaftin Sumeet Sabharwal da Clive Kunder, sun yi magana da jun kafin hatsarin jirgin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
India - Wani rahoton farko da hukumar binciken hadurran jiragen sama ta Indiya (AAIB) ta fitar, ya bayyana abin da ya faru ta amfani da sautin da aka samu daga cikin matukan jirgin Air India da ya yi hatsari.
Rahoton ya bayyana abin da ake zaton ya faru kafin hatsarin da ya auku a ranar 12 ga Yuni, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 241 da ke cikin jirgin Boeing 787.

Source: Twitter
AAIB ta bayyana cewa daya daga cikin injinan jirgin ya daina samun karfi bayan da maɓallan sarrafa man jirgin suka koma matsayin CUT OFF jim kaɗan bayan tashi, inji rahoton Reuters.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Idan maɓallan man jirgi suna a matsayin CUT OFF, injinan jirgin ba za su kara samun mai ba.
Wannan maɓalli yana da nau’i biyu: CUT OFF da RUN. Idan yana kan RUN, yana nufin an bude hanyoyin shigar mai zuwa injin.
Abin da matukan jirgin Air India suka ce juna
Rahoton ya ce akwai 'yar gajeriyar tattaunawa da ta gudana tsakanin matukan jirgin Air India su biyu, jirgin da ke kan hanyarsa ta zuwa London.
Daya daga cikin matukan ya tambayi dayan cewa, "Me ya sa ka kashe?" Sai dayan ya amsa da cewa, "Ba ni ne na kashe ba."
A nan, “kashe” na nufin maɓallin CUT OFF na mai wanda AAIB ta ce shi ne ya hana injinan samun mai.

Kara karanta wannan
'A shirye na taho daman': Ɗan Bello ya faɗi abin da ya faru bayan cafke shi a Kano
Hukumar AAIB ta ce:
“Injin N1 da N2 sun fara rage karfi daga lokacin da suka tashi yayin da aka dakatar da shigar man fetur zuwa injinan.
"A cikin sautin da aka samu daga dakin direbobin, an ji daya daga cikin matukan yana tambayar dayan dalilin kashe maɓallan, sannan dayan ya ce ba shi ne ya yi hakan ba.”
Zantukan da suka faru a cikin dakin direbobi
An samo wannan zance ne daga cikin sautin da aka nada a cikin rumbun gudanarwar jirgin, wanda ke adana duk abin da ke faruwa a cikin dakin direbobin.
Hukumar AAIB ba ta bayyana wane matuki ne ya ce wane zance ba, tsakanin Captain Sumeet Sabharwal da First Officer Clive Kunder.
Sai dai rahoton ya ce maɓallan CUT OFF da RUN dukkansu sun kasance a matsayin da ya dace a wurin da hatsarin ya faru.
Rahoton ya ce:
“Lokacin da aka motsa maɓallan sarrafa man fetur daga CUT OFF zuwa RUN yayin da jirgi yana cikin iska, kowanne injin zai yi amfani da tsarin fasaha domin sake kunna kansa da dawo da karfin tashi.”

Source: Twitter
Illar kashe maɓallin man jirgi
Masana sun bayyana cewa da wuya a samu matuki da zai kashe maɓallin mai yayin da jirgi ke cikin iska ba tare da wata matsala ba, saboda sakamakon hakan injin zai daina aiki gaba ɗaya.
Rahoton AAIB bai dora laifi kai tsaye kan matukan jirgin ba.
Wani masani kan tsaron jiragen sama daga Amurka, John Nance, ya shaida wa CBS cewa babu wani matuki mai hankali da zai kashe maɓallan man fetur lokacin jirgi yana tafiya.
Ya ce:
“Babu wani matuki mai hankali da zai kashe waɗannan maɓallan yayin da jirgi ke cikin tashi.”
Kuskuren matukan jirgin Air India
Tun da fari, mun ruwaito cewa, ana zargin wani kuskure mai muni da ya faru yayin tashin jirgin Air India ne ya haddasa mummunan hadarin da ya yi ajalin mutum 241.
Wani masanin sufurin jiragen sama, Captain Steve, ya yi imani da cewa kuskuren matuki na kin dage tayoyin saukar jirgin ne ya jawo hadarin.
Sai dai, wannan ra'ayi ne na Captain Steve kawai, domin har yanzu hukumomi na ci gaba da gudanar da bincike don gano dalilin hadarin.
Asali: Legit.ng

