Shugaban Amurka Ya Gana da Firaministan Isra'ila, An Ji Abin da Suka Tattauna kan Iran

Shugaban Amurka Ya Gana da Firaministan Isra'ila, An Ji Abin da Suka Tattauna kan Iran

  • Firaministan Isra'ila ya kai ziyara ƙasar Amurka a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa domin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza
  • Benjamin Netanyahu ya gana da Shugaba Donald Trump a fadar White House, kuma sun tattauna kan batatutuwa da dama ciki har da yakin Iran
  • Netanyahu ya jaddada cewa Isra'ila na nan a kan bakarta na shafe ƙungiyar Hamas mai mulki a Gaza

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Amurka - Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya gana da Shugaba Donald Trump yayin da ya kai ziyara fadar White House a ƙasar Amurka.

Netanyahu ya bayyana cewa yayin wannan ganawa, sun fi mayar da hankali ne kan yadda za a ’yantar da ƴan Isra'ila da ƙungiyar Hamas ke rike da su a Gaza.

Shugaban Amurka ya gana da Netanyahu.
Firaministan Isra'ila.ya kai ziyarsa ƙasar Amurka Hoto: @Netanyahu
Source: Twitter

A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X ranar Laraba, Netanyahu ya jaddada cewa yana da ƙudurin rushe karfin soja da na siyasa na Hamas gaba ɗaya.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya mika wa 'yan adawa bukatar takara bayan samun sarauta a Pantami

Abin da Trump da Netanyahu suka tattauna

Firaministan ya ce shi da Shugaba Trump sun tattaunawa kan tasirin nasarar da suka samu kan Iran, bayan yakin da ya gudana tsakanin Isra'ila da Iran na tsawon kwanaki 12.

Amurka ta tallafawa Isra'ila a yakin, inda ta kai hare-hare kan manyn cibiyoyin shirin nukiliyar Iran guda uku.

"Har yanzu ba mu kammala aikin mu a Gaza ba. Dole ne mu ‘yantar da duk fursunonin mu, mu lalata da kawar da karfin soja da mulkin Hamas gaba ɗaya,” in ji Netanyahu.

Wannan shi ne ziyararsa ta uku zuwa Amurka tun bayan da Trump ya hau mulki karo na biyu a ranar 20 ga Janairu.

Netanyahu ya tabbatar da shirin tsagaita wuta

A baya ya shaida wa manema labarai cewa, ko da yake yakin da Isra’ila ke yi a zirin Gaza bai kammala ba, akwai tattaunawar tsagaita wuta da ke gudana.

Kara karanta wannan

Me ya yi zafi?: Trump na barazanar korar attajirin duniya Elon Musk daga Amurka

Trump ya gana da Netanyahu a ranar Talata karo na biyu cikin kwana biyu, inda suka tattauna halin da ake ciki a Gaza.

Jakadan Trump na musamman a Gabas ta Tsakiya ya nuna cewa Isra’ila da Hamas na dab da cimma yarjejeniyar tsagaita wuta bayan kusan shekaru biyu ana yaki.

Netanyahu ya tabbatar da cewa ana kokarin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas.

Rahoto ya nuna cewa tawaga daga Qatar, wanda ke matsayin mai shiga tsakani a tattaunawa tsakanin Isra’ila da Hamas, ta gana da manyan jami’an Amurka kafin isowar Netanyahu a ranar Talata.

Netanyahu ya gana da shugaban Amurka.
Firaministan Isra'ila ya tabbatar da shirin tsagaita wuta a Gaza Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Netanyahu ya gana da manyan jami'an Amurka

Netanyahu ya gana da Mataimakin Shugaban Amurka JD Vance sannan ya kai ziyara majalisar dokokin Amurka a ranar Talata, inda ake sa ran zai sake komawa a ranar Laraba don ganawa da shugabannin Majalisar Dattawa.

Bayan ganawa da Kakakin Majalisar Wakilai ta Republican, Mike Johnson, Netanyahu ya sake nanata cewa yakin Isra’ila a Gaza ba a kammala ba, amma masu sasanci na aiki tukuru domin cimma tsagaita wuta.

Kara karanta wannan

Kotu ta yi hukunci kan bukatar Firaministan Isra'ila bayan kammala yaƙi da ƙasar Iran

A farkon ganawar, shugabannin biyu sun nuna cewa akwai cigaba a yunkurin da ake yi na kwashe wasu daga cikin Falasdinawa daga Gaza, wani lamari da ya jawo cece-kuce a duniya.

An fara shirin tsagaita wuta a Gaza

A baya kun ji cewa Isra’ila ta amince da sharuɗɗan da aka shimfida domin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta na tsawon kwanaki 60 a Gaza.

Shugaban Amurka, Donald Trump ne ya bayyana hakan, yana mai cewa Hamas za ta amince da waɗannan sharuɗɗa domin kawo ƙarshen yaƙin.

Sai dai Trump bai fayyace cikakkun sharuɗɗan da aka amince da su ba, amma ya yaba da rawar da Qatar da Masar suka taka a matsayinsu na masu shiga tsakani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262