Jagororin Adawa Sun Dura a kan Trump, An Gargade Shi kan Shiga Shari'ar Netanyahu

Jagororin Adawa Sun Dura a kan Trump, An Gargade Shi kan Shiga Shari'ar Netanyahu

  • Shugabannin adawa da na gwamnati a Isra’ila sun fara musayar yawu a kan kalaman Shugaban Amurka, Donald Trump
  • A wani sako Da ya fitar a baya-bayan nan, Shugaba Trump ya nema wa Benjamin Netanyahu afuwa a Isra'ila
  • Ya ce bai dace a ce ana shari'a da Firayim Ministan na, saboda haka ya ke ganin a yafe duk zargin da ake masa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Kasar Israel – Shugaban adawa na Isra’ila, Yair Lapid, ya caccaki tsohon shugaban Amurka, Donald Trump kan shiga harkokin kasarsa mai cin gashin kanta.

Trump ya jawo wa kansa martanin ne bayan ya nemi a yafe shari'a da ake yi da Firayim Ministan kasar, Benjamin Netanyahu bisa tuhume-tuhume da dama.

Kara karanta wannan

An taso Firaministan Isra'ila a gaba bayan gama yaƙi da Iran, ya fara roƙon arziƙi

Firayim Minista, Benjamin Netanyahu da Shugaban Amurka, Donald Trump
Shugabannin adawa a Isra'ila sun soki Trump Hoto: Getty
Source: UGC

BBC ta wallafa cewa Trump ya ce kamata ya yi a soke shari'ar Netanyahu a cikin gaggawa, wannan a yafe wa 'wannan 'gwarzon.'

Yan adawa a Isra'ila sun hayayyakowa Trump

Al Arabiyya News ta ruwaito cewa Yair Lapid ya bayyana a wata hira da gidan yanar gizo na Ynet, inda ya soki kalaman Trump bisa kalamansa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

“Muna godiya da goyon bayan shugaban Trump, amma... shugaban kasa bai kamata ya tsoma baki a shari’a da ke gudana a kasa mai ‘yancin kanta ba.”

Lapid wanda ke jagorantar jam’iyyar adawa ta Yesh Atid, ya goyi bayan matsayar wani jagora a kasar, Simcha Rothman daga jam’iyyar Religious Zionism.

Rothman wanda shi ne shugaban kwamitin shari’a na majalisar dokokin Isra’ila. ya ce:

“Ba aikin shugaban kasar Amurka ba ne ya tsoma baki a harkar shari’a ta cikin kasar Isra’ila."

Ana son Netanyahu ya fuskanci shari'a

Rothman wanda ya jima yana sukar abin da ya kira karfi da iko da kotuna ke nunawa, ya ce yadda ake tafiyar da shari’ar Netanyahu yana kassara kasarsu.

Kara karanta wannan

Sabuwar matsala: Isra'ila za ta gurfanar da Netanyahu, Trump ya nemi afuwa

A bangarensa, Ministan tsaro na cikin gida, Itamar Ben Gvir, wanda ke jagorantar wata jam’iyya mai ra’ayin rikau a kawancen Netanyahu, na da mabambancin ra'ayi.

Firayim Minista Benjamin Netanyahu
Ana tuhumar Benjamin Netanyahu da cin hanci Hoto: Benjamin Netanyahu
Source: Facebook

Shi ma Ministan harkokin wajen kasar, Gideon Saar, ya ce ci gaba da shari’ar Netanyahu a lokacin da ake cikin yaki, “ba daidai ba ne kuma rashin adalci ne.

Yana goyon bayan kiran Shugaban Amurka, Donald Trump da a soke tuhume-tuhumen da ake masa baki daya.

Laifuffukan da ake zargin Netanyahu da aikatawa

Shari’ar da aka sha dagewa tun fara ta a watan Mayu 2020, tana ci gaba yayin da Netanyahu ke musanta aikata wani laifi.

A cikin shari’ar farko, an zargi Netanyahu da matarsa Sara da karbar kyaututtuka masu tsada da darajarsu ta kai $260,000 daga wasu attajirai don su samu tagomashi a harkokin gwamnati.

A wasu shari’o’in biyu daban kuma, an zarge shi da kokarin cimma yarjejeniya da wasu kafafen watsa labarai na Isra’ila domin su rika buga masa rahotanni masu kyau.

Netanyahu ya sha neman dage zaman shari’ar da dama, inda a baya-bayan nan ya nemi hakan bisa dalilin yakin da ake yi a Gaza tun watan Afrilu 2023, sai Lebanon da Iran a watan Yuni.

Kara karanta wannan

Bayan yaƙi da Isra'ila, Shugaba Trump ya faɗi abin da Amurka za ta tunkari Iran da shi

Isra'ila ta yi asara a yaki da kasar Iran

A baya, kun ji hukumomin Isra’ila sun bayyana cewa hare-haren da Iran ta kai kan ƙasarsu cikin kwanaki 12 sun yi sanadin mutuwar mutane 28 da jikkata 3,000.

Bayanai sun tabbatar da cewa wannan hari ya kasance mafi muni da aka taba kaiwa ƙasar Isra’ila daga wata ƙasa, duk da yadda ya ke Kai hari makwabtanta.

Dakarun sojin Isra’ila (IDF) sun bayyana cewa Iran ta harba kusan makamai masu linzami 550 da kuma jiragen yaki marasa matuka har 1,000 a cikin makonni biyu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng