Rufa Rufa Ta Ƙare: An Gano Mummunan Halin da Iran Ta Jefa Isra'ila a Kwanaki 12
- Rahotanni sun nuna cewa tattalin arzikin Isra'ila ya fuskanci koma baya da ba a taɓa gani ba sakamakon musayar wuta da Iran
- Wani masani, Naser Abdelkarim ya ce Iran ta yi wa Isra'ila mummunar illa kuma ba a ɓangaren tsaro kaɗai ba
- Ya ce hatta darajar kuɗin kasar ya faɗi baya ga maƙudan kuɗin da sojoji suka laƙume, sannan akwai batun biyan ƴan ƙasa diyya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Israel - Tattalin arzikin Isra’ila ya shiga halin tsaka mai wuya bayan yakin kwanaki 12 da kasar ta yi da jamhuriyar musulunci ta Iran.
Rahotanni daga masana da kafafen yaɗa labarai sun nuna cewa biliyoyin Daloli ne suka salwanta sakamakon wannan rikici da ya shafe kwanaki 12.

Source: Getty Images
Jaridar TRT Hausa ta ƙasar Turkiyya ta rahoto cewa Isra’ila ta kashe kusan Dala biliyan 5 a makon farko na musayar wutar tsakaninta da Iran.

Kara karanta wannan
Wace ƙasa ta yi nasara tsakanin Iran da Isra'ila? Netanyahu ya yi jawabi bayan tsagaita wuta
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar rahoton, ƙasar ta kashe Dala miliyan 725 kullum a kan yaƙin, daga ciki Dala miliyan 593 na tafiya ne wajen kai hare-hare yayin da Dala miliyan 132 ake warewa don kariya da haɗa sojoji.
Halin da Iran ta jefa tattalin arzikin Isra'ila
A nata bangaren, Jaridar The WSJ ta ce tsarin kariyar makamai masu linzami na Isra’ila ya ci gaba da laƙume kuɗi, ta kai ana kashe tsakanin Dala miliyan 10 zuwa 200 a kowace rana.
Cibiyar Aaron Institute for Economic Policy da ke Isra’ila ta yi hasashen cewa idan harin ya ci gaba na wata ɗaya, kuɗin da za a kashe gaba ɗaya na iya haura Dala biliyan 12.
Wani masani kuma wanda ke dab da zama Farfesa a Jami’ar Amurka ta Falasɗinu, Naser Abdelkarim, ya ce tasirin wannan rikici ya wuce ɓangaren tsaro kadai.
Isra'ila na iya asarar Dala biliyan 20
Masanin ya bayyana cewa Isra’ila na iya rasa kimanin Dala biliyan 20 idan aka haɗa asarar da ta yi kai tsaye da wacce ba ta kai tsaye ba a waɗannan kwanaki 12.

Kara karanta wannan
Shugaban Amurka ya tsallake rijiya da baya a Majalisa bayan harin da ya kai ƙasar Iran
Har wa yau, Abdelkarim ya ce ana sa ran giɓin kasafin kuɗin Isra’ila zai ƙaru zuwa kashi 6%, kuma biyan diyya ga ‘yan ƙasa zai jefa ƙasar cikin matsin tattalin arziki.
Rahoton hukumar harajin Isra’ila ya ce fiye da mutum 10,000 sun bar gidajensu a makon farko na rikicin, kuma mutum 36,465 sun nemi a biya su diyya.

Source: Getty Images
Mafitar da ta rage wa Isra'ila bayan yaƙi da Iran
Domin cike giɓin kuɗi da ke ƙaruwa, Abdelkarim ya ce gwamnatin Isra’ila na nazarin ɗaukar ɗaya daga cikin matakai uku, Rage kashe kuɗi a fannin kiwon lafiya da ilimi, Kara haraji, ko aɗo kudi.
Ma’aikatar kuɗi ta Isra’ila ta tabbatar da cewa asusun ƙasar na ƙara yin ƙasa, inda ta nemi a tura Dala miliyan 857 zuwa ma’aikatar tsaro, tare da rage Dala miliyan 200 daga kasafin kuɗin lafiya, ilimi da wasu ayyukan jin ƙai.
A ƙarshe, Abdelkarim ya bayyana cewa darajar kuɗin Isra’ila, shekel, ta faɗi zuwa 3.7 kan kowace Dala 1, amma daga baya ta farfaɗo zuwa 3.5.
Adadin mutanen da aka kashe a Iran
A wani rahoton, kun ji cewa Iran ta sana da cewa an kashe mutane 610, wasu fiye da 4,700 kuma sun jikkata a kwanaki 12 da ƙasar ta yi yaƙi da Isra'ila.
Ma'aikatar lafiya ta kasar Iran ta ce mafi yawan mamatan fararen hula ne, ciki har da yara 13 da likitoci biyar da ma’aikatan agaji.
Ta ƙara da cewa an lalata asibitoci guda bakwai da motoci na gaggawa tara sakamakon harin da Isra’ila ke kaiwa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
