An Rasa Makomar Tsagaita Wutar Iran Ganin Ayatollah Khamenei Ya Yi Gum
- Kasar Iran da Isra’ila sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta, domin kawo karshen rigimar da ake yi tsakanin kasashen biyu
- Sai dai jagoran addini a kasar, Ayatullah Ali Khamenei bai fitar da wata sanarwa ba kan lamarin zuwa yanzu da yaki ya lafa
- Khamenei ne ke da ikon yanke shawara kan manyan lamura, hakan ya sa mutane da dama ke jiran jin matsayinsa game da tsagaita wutar
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tehran, Iran - A jiya Talata 24 ga watan Yunin 2025 aka sanar da tsagaita wuta tsakanin kasashen Isra'ila da Iran.
Shugabannin Iran da wasu manyan jami’ai sun tabbatar da an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakaninsu da Isra’ila a hukumance.

Source: Getty Images
Rahoton BBC Hausa ya ce Shugaba Donald Trump ne ya tura bukatar haka domin dakile cigaba da zubar da jini.
Iran/Isra'ila: Ƙoƙarin Trump domin tsagaita wuta
Shugaban Amurka, Donald Trump shi ya fara maganar neman sulhu domin tsagaita wuta tsakanin kasashen guda biyu.
Trump ya ce sun yi yarjejeniya kan kowace kasa za ta bar kai hare-hare kan yar uwarta na wani lokaci.
Sai dai daga bisani, Trump ya nuna damuwa kan yadda kasashen Iran da Isra'ila suka ki bin ƙa'ida inda suka kai hari kan junansu.
Hakan ya biyo bayan shafe fiye da kwana 10 ana kai munanan hare-hare tsakanin Iran da kuma Isra'ila.
Meye Ali Khamenei ya ce kan tsagaita wuta?
Duk da haka, babban limamin Iran, Ayatollah Ali Khamenei, bai ce uffan ba kan wannan sabon mataki na tsagaita wuta da aka cimma.
Kamar yadda aka sani, Khamenei ne ke da ikon yanke hukunci na ƙarshe kan muhimman al’amuran ƙasa kuma mutane da dama na jiran matsayarsa.
Rahotanni sun ce Ayatullah Ali Khamenei ya bar gidansa da ke tsakiyar birnin Tehran.

Kara karanta wannan
Wace ƙasa ta yi nasara tsakanin Iran da Isra'ila? Netanyahu ya yi jawabi bayan tsagaita wuta
Amma wasu majiyoyi sun ce yanzu haka yana zaune a wani wajen daban da tsaro ya karade shi.

Source: UGC
Ana hasashen Khamenei ya sauya matsuguni
Sai dai, gwamnatin Iran ba ta tabbatar da wannan sauyin matsuguni da Khamenei ya yi ba, ko dalilinsa na barin wancan wuri.
Tun bayan harin da Isra’ila ta kai Iran ranar 13 ga Yuni, ba a sake ganin Khamenei a bainar jama’a ba.
Wasu bayanan sirri sun nuna cewa harin da Amurka ta kai bai tarwatsa muhimman cibiyoyin nukiliyar Iran gaba ɗaya ba.
Bincike ya kuma nuna cewa Iran na samun taimako daga China wajen kaucewa takunkuman da Amurka ta kakaba mata.
Isra'ila ta zargi Iran da ɗaukar nauyin ta'addanci
Mun ba ku labarin cewa Isra'ila ta zargi Iran da ɗaukar nauyin ƙungiyoyin ta'addanci ana tsaka da shirin tsagaita wuta.
Isra'ila ta ayyana babban bankin Iran a matsayin ƙungiyar ta'addanci don hana kudi zuwa kungiyoyin da Iran ke tallafawa a Gabas ta Tsakiya.
Ministan tsaro a kasar ya ce wannan hakan na daga cikin yunkurin hana Iran hada-hadar kuɗi da ke taimaka wa ayyukan ta'addanci da rikice-rikice a yankin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng